chapter 34

407 15 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*

🅿️-3️⃣4️⃣

___________________Bude ƙofar dakin yaya deeni yayi tare da zuro kanshi ya ɗan leƙa waje duk da yana da tabbacin kowa na gidan ya kwanta, amma a cewar shi gara ya fara dubawa saboda tsaro ba dan tsoro ba😎, kallon ta yayi ganin tana ƙunshe dariya, dawowa daga baya yayi yace "Ni Ko? Ni kike wa dariya koh!?

Ganin yanda yayi maganar yana nuna kanshi lokaci guda dariyar da take ƙunshe wa ta fito, ai ko tashiga darawa, tsaye yayi kawai yana kallon ta dan shi baiga wani abin dariya da ya faru ba, ita kuwa ganin yanda yake leƙen waje da zura kai ne ya bata dariya, dan tasan umma yake leƙe yana tsoron ya sha faɗa, saidai abinda ya manta shine an rufe qofofin gidan ƙarshe dai dole sai yaje gurin umma, faɗan da yake gudu kuma sai yasha,

Katse ta yayi da cewar tashi ki rakani in fita ta baya saiki rufe ƙofar,

Dariya tasake yi tace keys din guda na hannun yaya Sadiq  sauran suna hannun Abba,

Komawa yayi cikin ɗakin yace "shike nan yau anan zan kwana💃🏻  ya faɗa tare da zama gefen gado.

Zaro ido waje tayi tare da cewa" zan karɓo maka a gun Abba mana,

Yace" to idan ya tambaye ki me zakiyi dasu fa kice mai me?
Cewa zan yi... Sai kuma ta ƙwalalo ido tare da rufe baki, murmushi yayi dan ya fahimci inda maganar ta taso dosa,

Janyota yayi yace "zaki bari in kwana anan ko? Kinga in umma ta ganni faɗa zata yimin kuma tsoro nakeji in ɗauki hanya ni kaɗai dare yayi... Ya faɗa cikin marairaita, kamar dai ƙaramin yaro, shiru tayi tana tunani kafin daga bisani ta samu mafita da sauri tace" yaya to me zai hana ka kira yaya sadiq yazo ya buɗe maka?

Sake marairai cewa yayi yace" to ai zai faɗawa umma ne,
Cewa tayi" a'a nasan bazai faɗa ba,
"Ni dai a'a saidai idan zakije ki amso min gurin Abba dan gara suji abakin ki ina nan da ace sadiq ne zai faɗa musu nasan faɗan sai yafi sauƙi,

Duk da yanda yasan zai shawo kan jidda dan taje karɓar key a dakin ƙi tayi, kuma badan bazai iya kiran sadiq bane a'a, yafi son taje da kanta wataƙil in suka ga haka sun bashi yar ƙanwarshi amma ta ƙi, kuma yasan itama faɗan take gudu, dole haka ya ɗaga waya ya kira yaya sadiq yace yazo ya buɗe mai ƙofar baya,

Miƙewa yayi yace "to muje ki rakani kar ummanki taji motsi ta fito ta ganni, dariya tayi tare da miƙewa ta dauki hijab ɗin ta tasaka, tare suka fito yana riƙe da hannun ta su ka nufi dogon koridon da zai sadasu da qofar,

Suna shiga wurin ya tsaida ta ganin har lokacin yaya Sadiq bai iso ba, sakin hannun ta mai tsananin taushi da sulɓi yayi tare da sa hannunsa  ya dafa bangon da ta jingina, ya matsa kusa da ita sosai har suna jiyo hucin junansu, ga ƙamshin su da ya haɗe wuri ɗaya ya samar da sassanyan ƙamshi mai daɗi da saka zuciyar masoya a shauƙi, ƙasa tayi da kanta ganin yanda yayi mata zobe gashi motsi kaɗan zatayi ta kai ga jikinshi,

Ɗago fuskarta yayi yace "to me ye Kuma na sunyar da kan, inace mun shirya yanzu koh?

Ɗaga kanta tayi alamar eh, amma duk da haka ta kasa sakewa, jin kamar motsin isowar yaya sadiq yasa ya juya gefen fuskar shi tare da turo mata kuncin shi wai tayi mai good night kiss, ƙoƙarin sunkuyar da kanta take yi da sauri ya ɗago kanta tare da kai mata kisa a forehead dinta yace sleep well lil sis! Sakinta yayi tare da cewa ki je, tsaye yayi har ta wuce duk da sadiq ya buɗe mai ƙofar amma saida ya jira ta wuce sannan ya fito yayi wa sadiq sai da safe ya wuce.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now