chapter 32

308 17 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*

🅿️-3️⃣2️⃣

____________________________________________________________________________________________Da fargaba hajara ta qarasa shiga falon dan ita fa yanzu har wani shakkun deeni takeji a yan kwanakin nan duk da wani lokacin abin yakanyi tasiri Amma fa in ta fannin fita ne to ba sauqi,

Ga mamakinta bata tarar da shi a falon ba, hakan yasa ta yi wucewarta dakinta,

Har bayan Isha baice da ita komai ba saima ganin da tayi ya fito da key a hannunshi da alama fita zaiyi,

Tasowa tayi ta qaraso gunshi tare da fadar" honey Ina zuwa da daren nan,

"Gidan umma! Daga haka yayi wucewarshi yabarta a Nan,

Ai dasqarewa tayi a gun a fili ta furta "na kashe maciji na manta ban sare Kan ba!

Wani irin baqin ciki ne ya taso mata har wani d'aci takeji a maqogoranta tanaji inama bata yiwa jidda wannan qazafin ba, dan dai yanzu gashi abin ya dawo mata dan batasan me suke ciki da jiddar ba amma tanada tabbacin inda jidda na gidan to duk tsiya bazabar deeni ya rabe taba, amma takeji yanzu fa??

Gabadaya  ranta ya cunkushe tama rasa kalar tunaninda zatayi, gashi zuciyar ta sai hasaso mata takeyi jidda nacan maqale da mijinta,

Dabas tayi a kujera tareda kifa kanta a hannun kujerar tanajin wani zafi a ranta.

Deeni kuwa bayan fitarshi Saida yatsaya yasiyi madara mai sanyi a hanya kasancewar anaso in mutum ya qone ya yawaita Shan madara sannan ya doshi hanyar gidan.

Daga umma har jidda ba wanda ya tarar A falon sai yaya sadiq shikadai yana cin abinci yana kallon ball,

Bayan sun gaisane yaya deeni ya tambayeshi umma fa?

Cewa Yaya sadiq yayi tana dakin Abba,

Daga haka ya zarce sama ya nufi dakin jidda dan yasan dai dole tana dakinta tunda bata falon,

Jidda kuwa tsaye take ta juya baya tana qoqarin gyara gadon ta dan tuni tayi shirin bacci,

Kallonta ya tsayayi tun daga sama har qasa kasancewar rigarda ke jikinta irin yar qaramar nan ce iya cinya, gashi daga samanta duk net ne, shagala yay yana kallonta saidai jin yafara jin sauyi ajikinshi yasa  yadanyi gyaran murya ya shiga dakin sosai a ranshi kuwa cewa yake qara inshiga kar incigaba da kallon ta azo ayi abin kunya.

Dagowa tayi da sauri dan bataji motsin tafiyar mutum ba,

Shigowa dakin yayi tare da rufe qofar sannan ya qaraso,

Wucewa tana dingirsa ta nufi gun da ta ajiye hijab din sallarta ta dauko ta saka sannan ta gaidashi,

"Lafiya, kawae yace mata yayi wa kanshi mazauni a gefen gadon tare da cewa "zo Inga qafar,

Matsowa tayi har zata zauna a side bed yace dawo nan, yafada tare da nuna mata gefen shi,

Dawowa tayi ta zauna, Yaya deeni yace" ki zauna sosae ki miqo qafar ingani,

Gyara zaman ta tayi tare da miqomai qafar saidai tana ganin alamar zai kai hannunshi a ciwon nata tayi saurin cafke hannun tana cewa" Yaya zafi!

Kallon hannunta data riqe nashi hannun yayi,

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now