chapter 51

692 34 20
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
♠♣♠♣♠♣
♠♣♠♣
♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
♣♠♣♠♣♠
♣♠♣♠
♠♣
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*Story*
*and*
*Written*
*By👇*

*Asmy Jafar*
*(Ummu Abdulhakim)*

&

*Zainab Mukhtar*
*(Ummu Maryam)*
*Aminan juna*👭🏻

*WATTPAD @Asmyjafar*

🅿️-5️⃣1️⃣

__________Jin tattausan tafin hannun shi a fuskar tane ya farkar da ita daga baccin gajiya da wahalar dukan da tasha, rungume hannun tayi a ƙirjin ta tare da matseshi sosai ba tare da tayi magana ba, shiru sukayi dukan su kafin daga bisani Deeni yace, "Sannu kinji Auta," gyaɗa kai kawai tayi
ɗakin ya sake daukar shiru na tsayin daƙiƙu.

A can police station kuwa su Abba sunje, duk wani statement da za'a cika anyi an turo kotu, zuwa gobe za suje can kotun suji hukuncin da alkali zai yi musu.

Iyayen Hajara kuwa basu san me ke faruwa ba a lokacin, sai da sukaga angama Cike-ciken takardu za'a tura su kotu sannan Hajara takira wayar Mommynta ta sanar da ita abinda ke faruwa amma ba gaskiyar abinda yafaru tafaɗa ba sai ma ƙazafin da tayiwa Deeni da Abba wai sun zo sun tarar ƴan makaranta na rigima sukayi fakin ashe da Jidda ne ake yin faɗan, shine Deeni na isowa yasa aka kamasu tare da jifan motar su.

Ran Momy ya ɓaci matuƙa, ta rasa me wannan ɗan iskan Deenin ke nufi da ƴar ta, wayar Daddy ta kira tare da shaida mai, ta ƙare maganar da cewar, " kuma dole ne a raba wannan ƙaddararren auren. Kashe wayar tayi bayan sun gama magana.

Deeni bai fito ɗakin Auta ba sai da aka kira sallar Azahar yayi alwala a ban ɗakin ta sannan ya fito zuwa masallaci.

Bayan sallar Isha'i duk suna zaune a falon Umma, Jidda na cin tuwo a kwano ɗaya itada Umma, yayin da Yaya Deeni ke kwance kan doguwar kujera yana danna waya, yaya Sadik kuwa sarkin tsokana yana kan ƙaramar kujerar dake fuskantar Deeni, sai cewa yayi, "Anty Jidda, ya kamata fa inje in kawo miki man zafi ki ɗan shafa saboda rage gajiya.... Bai gama faɗin abinda ke bakin shiba Yaya Deeni ya jefe shi da filon kujera tare da cewa, "Sadik ka kiyaye nifa, zan saɓa maka yanzun nan tunda kai ba abinda ka iya sai tsokana, ƙaton banza kawai.

Dariya yayi tare da kare jifar yana cewa, "Haba Bro daga taimako? Kuma da kake cewa ƙaton banza ka manta yanzu Yayata ce, dan haka ba zancen wani ƙaton banza ka barni inji ta bakin babbar Yaya idan tana da buƙata."

Haɗe fuska Jidda tayi tare da kallon Umma, wai koda Ummar za tayi magana amma sai taga Umma na murmushi, ai ko nan take tafara zumbura baki tana cewa, "Umma kina dai jin Yaya Sadik ko?"
Murmushi mai sauti Umma tayi a wannan karon tare da cewa, "eh! Na ji, ai taimaka miki zai yi ko kin rage gajiyar dukan da kika sha, tunda ke ga kinan kullum cikin sa karci, kina tsaye har a ɗauke ki a tura mota ayi miki dukan kawo wuƙa kina sake da baki, kuma wai mata ba ko maza ba saboda saunan ci, ai Sadik taimakon kine zaiyi.

"Yawwa Umma tah faɗa mata dai." Cewar Yaya Sadik yana dariyar tsokana.

Tuburewa Jidda tayi tare da fa ra bada labarin yanda abin ya kasance, tana cewa, "ita ba laifin ta bane tsorata tayi, kuma ai su biyu ne sun yi mata yawa," har da cewa, "ai idan suka sa ke Allah ramawa zanyi, dan wannan Zee ɗin marar auki ko Ni na fita ƙiba, ture ta zanyi in hau ruwan cikin ta in mata dukan tsiya,"

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now