chapter 30

326 24 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*


*Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhu yan uwa Kuma masoya muna masu baku haquri akan sauye sauyen da aka samu na canjin gida wanda munsan cewa Kuna sane da dalilin yin hakan, Amma inshallah yanzu komai yayi daidai dftr zaku bamu hadin Kai Dan gujewa faruwar abinda ya faru a baya, Allah yasa mu dace Amin, luv you all🥰❤️🥰*


🅿️-3️⃣0️⃣

____________________________________________________________________________________________A razane ta dago kanta dan ko a mafarki taji wannan qamshin turaren zata shaida ko waye, kaucewa tayi zata shige da sauri ya sha gabanta ya daure fuska sosai tamkar bai ta6a dariya ba yace,

"Daga Ina kike?

Cikin Sheshekar kukanta tace,

"Gidanmu,

"Da iznin wa Kika baro gidanki Kika dawo nan har Kika samu damur zuwa wani gun?

Shiru tayi tana cigaba da kuka,

A kausashe yace ba tambayarki nakeyi ba kinyi min shiru,

A shagwa6e tace "to ni banason gidanka ne tunda dukana akeyi,

Ya bude baki zaiyi magana kenan yaji muryar umma a bayansu tana cewa da iznina ta baro gidanka ko zaka maidata ne inji,

Kaucewa yayi ya bata hanya ta wuce abinta umma Kuma ta qarasa shigowa falon,

Gaisheta yayi a ladabce,
"Yawwa kawai tace ta samu wuri ta zauna,

Shima zaman yayi falon yayi tsit kamar ba wani mahaluqi mai motsi a ciki,

Sun dade ahaka kafin yaya deeni yace"

"Umma dan Allah kiyi haquri da duk abinda ya faru sharrin shaidan ne Kuma inshallah hakan bazata sake faruwa ba,

Katseshi tayi da cewar "sharrin shaidan ko dai sharrin shaidaniyar matarka? 

Ai kam hakan bazai sake faruwa ba kamar yanda kace dan ko jidda ko qofar gidanka bazata sake takawa  ba bale tayi rayuwa ciki har kuji dadin musguna mata kaida matarka,

Kai ko kunyar iyayen yarinyar nan bakaji?

Da wane ido zaka kalli mahaifanta,

Kuma Kai in akwae amana ko karen gidan Salim ai ka riqeshi da daraja bale qanwarshi jininshi, kaban mamaki deeni bakayi halin Mai sunanka ba sam,

To yanzu dai nace ai jiddar dai ta baro muku gidan ko???

sai kuyi yadda kuke so ai,
Kuma kaje ka kawo min takardar yar mutane kafin in maka ka kotu dan kasani toh, 

Cikeda da mamaki yake kallon umma wai ta makashi kotu,

Haquri ya qara bata ya miqe yabar gidan daman abinci yazo ci kuma baiga alamar za'a iya bashi Koda ruwa ne a gidanba,

Gidan Salim ya nufa daman yayi mai way gashi nan zuwa,

Cewa Yaya Salim yayi ya qarasa gidan kawae Shima yana hanya yakusa isowa.

Baifi minti 5 dayin parking ba sai ga yaya Salim ya iso,

Tare suka shiga gidan, Khalil nata wasanshi a falon, gaishesu anty ma'u tayi sannan ta miqe ta nufi ciki,

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now