chapter 19

232 13 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*

🅿️-1️⃣9️⃣

___________Girgiza kanshi yayi sannan yace"Babu matsala baba ai jidda qanwatace Allah yasa hakan shine mafi alkhaeri,

Inji cewar Yaya deeni, Dan dai da kunya ya dubi idon baba yace bayason yarshi, sannan dawane ido zai kalli iyayenta Mata dakuma amininsa Salim bacin ya qi Yar uwarshi,

"Amin Amin maisunan manya,

Abba yace " to mashaallah abin yazo da sauqi sosae fiye da tunaninmu Allah yyi mka albarka,
Sai batun auren dama wata3 muka yanke kafin lokacin ta gama makaranta yayi maka ko ko dai?

Nanma d'aga kanshi yayi alamar eh"

"To alhmdllh Allah yayi albarka sai kaje kafara shiri,

"Sallama yayi musu ya miqe jikinshi a matuqar sanyaye ko cikin gidan Bai je ba haka ya kama hanyar zuwa gidanshi,

Anan yabar su suna qara tattaunawa dan Abba yace shizaiyiwa 'yarshi magana inta amince shikenan, inkuma akasin hakane to ba Wanda zaiyimata dole, shiyasa ma ya hana baba yayi Mata mgna Dan baison ashiga haqqinta,

yayah deeni ne Akan hanyar zuwa gidanshi a hankali yakejan motar yama rasa tunaninda zaiyi shidai bazaice ga takamaiman abinda yakeji ba Amma dai yanada yaqinin bason auta yakeyi ba, so irinna auratayya sai dai na yanuwantaka, haka Kuma bayajin qiyayyarta irin sosai dinnan, Dan inbaya ganta ba ma mantawa yake da ita inya gantane yakejin tsanarta,

To Amma meyasa su Abba suka yanke wannan hukuncin alhalin dukansu sunsan burin jidda nason tayi karatu mai zurfi?
Mgnr gasky koshi yanason tayi karatu Dan tanada basira sosai shi baimasan ya akayi ba har auta tafara exam baije ya binciki karatunta ba,  ko tadage da karatun ko Kuma dai ta tsaya shirmene to amma.... Mtswww qaramin tsaki yaja batareda ya ida fadar abinda zai fada ba,

Har ya iso gidanshi Yana nazarin maganarda sukayi dasu Abba.

A hakimce ya tarar da gimbiyar Dan yau 'yan soyayyar ne suka motsa Yana shigowa falon da sauri ta miqe ta taryoshi hadata yayi da jikinshi yayi hugging dinta tare da bata light kiss a forehead dinta,

Kasancewar Yana jin yanayinshi ba Dadi yasanya ya wuce dakinshi direct Yana shiga Kuma Bai zarce ko inaba sai toilet, har yayi wankan ya gama Yana nazarin yanda zai gayawa gimbiyarshi wannan maganar,

Daga qarshe ma kawae ya yanke hukuncin bazai sanar da itaba sai lokacin da abin yazo sannan,

Dan yasanta Sarai intaji wannan maganar to ba shakka sai hankula sun tashi mussaman yanda take nuna qiyayyarta ga jidda a fili,

Ashe shiyasa tun farko  hajara batason auta Ashe akwae abinda take hangowa Wanda ni banta6a kawoshi arainaba sam,

Dafe kanshi yayi kafin yace" Sam su Abba basuyi tunani Akan wannan abinba to shi me ma zaice da jiddan ne?
Itama Kuma metasani na aure mtswww,

Daga haka ya darwaye jikinshi ya fito bandakin, aranar dai haka yakejinshi kamar Mara lafiya, da anty hajara tanemi sanin halinda yake ciki ma cemata yayi kanshi ke ciwo daga haka ya kwanta Akan gadon ya rufe idonshi, a zahiri zakayi tsammanin bacci yakeyi Amma kuma idonshi biyu yanata tunane tunane ne.

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now