chapter 25

300 13 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmy Jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*

*_____________________________________________________________*

*~Dedicated to all members of ban tsaneshi ba group~*
*gasky muna godiya sosae da qaunar da kuka nunawa buk dinnan musamman*
*sis adama aliyu,*
*Sis nafisa alwasa,*
*Sis saratu abdlhi argungu,*
*Mmn antyma,*
*Sis halima yunus d duk sauran members Allah yabar qauna yabarmu cikin aminci luv you all sisters😍🥰❤️*
*wannan page din nakune kuyi yanda kukeso dashi*

*______________________________________________________________*

*Gaisuwarku dabance masoyan asali anty juwairiya barda,mom sa'aderht madoubee 🌹,zainab shantali (my  shant) Allah yabarmu tare ya qara danqon zumuncinmu luv you dubu dubu sisters😍🥰❤️💃🏻*

*_____________________________________________________________*

*🅿️-2️⃣5️⃣*

______________________har suka Isa hospital jidda na kuka hakan yasa zazzabin ya qara rufe ta da isar su aka kwantar da ita bayan sun gama duk wani Abu dazasuyi ne Sadiq yayi mishi sallama zai tafi har ya Kai qofa deeni yace"Please do not reveal this to anybody I will settle it down myself In Sha Allah,

"Gyada kanshi kawae yayi ya tafi,

Janyo kujerar roba dake dakin yayi ya zauna yayi Mata quri yana kallonta, azahirin gsky koshi baijin dadin abubuwan da ke faruwa amma Kuma ya rasa dalili sai dai ya daukar wa kanshi alqawarin inshaallah zaiyi wani abu akai zai Kuma hana hajara dukan jidda duk da har yanzu yanajin tsanar jidda a ranshi, amma ya qudurta zai yi wani abu akai,

Sai yanzu yake qarayin mamakin kansa da Kuma tunanin meyasa bai ta6a hanawa ba a duk lokacin da za'a daketa, sosai yayi zurfi a cikin tunanin shi har baisan lokaci ya tafi sosai ba sai da yaji ringing phone dinshi,

Hajara ce ke Kira, Yana dauka  tace "kana duba agogo kuwa? Qarfe 11 da kusan rabi fa, kana Ina ne?

"Hospital, Kawae yace mata,

"To waye ba laifiya dan nasan dai baka shiga dutyn dare ba har yanzu?

"Jidda,

"Ai take gaban ta ya Fadi Kar dai ta kashe Yar mutane, dan ta lura da lokacin da tabarta a yashe tana ta numfarfashi amma dayake qwararriyace gun duniyanci sai cewa tayi,

"To Kuma Dan jiddar ba lafiya shine akace ita kadai ke da haqqi akanka ko?

Sai da ya dauke wayar kunnenshi ya kalli screen din tsabar mamaki da yaji, Wai hajara ke wannan maganar sai yanzu yake tunanin lallae ko jidda nada haqqe akanshi Amma daidai da Rana daya bai ta6a sauke wa ba dan bai ta6a damuwa da ta ci ko ta Sha ba, tana da lafiya ko akasin hakan shiru yayi Yana istigfari a ranshi,

Jin yayi shiru yasa tayi tunanin Kila fa ta tafka kato6ara, sai kawae tayi abinnan da hausawa ke cewa tabarmar kunya da hauka ake nadeta, qarshe dai tsaki tayi ta takashe wayar,

Tun bayan da suka gama wayar deeni ya lula duniyar tunani yayi alqawarin gyara amma Kuma ta Ina zai fara?
Har gobe kallon qaramar qanwarshi yake yiwa jidda, bazai ta6a iya tafiyar da ita amatsayin matar auranshi ba,
Murmushin samun nasara yayi bayan yayi wani tunanin,

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now