chapter 28

264 14 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*

*__________________________________________________________________*

*special thanks to;*
*sis adama aliyu, sis saratu argungu, sis nafisat alwasa, sis halima yunus, sis fiddausi(fidow) Allah yabar qauna sisters*

*________________________________________________________________*

*Jinjina ta ban girma gareku members na bantsaneshi ba👍👍👍  Allah yabar qauna a tsakaninmu fans muna muqo dubun gaisuwa gareku,*
*Mussaman masu comments🥴 iya wuya muna together inshallah*

*sis eeshart muna godiya da sharing🥰*

*__________________________________________________________________*

~*Dedicated to*~
*Big sis anty juwairiya barda,*
*Mom sa'aderht Abdullah madoubee 🌹*
*My qawalliya zainab shantali* *luv you so much Yan uwa🥰😘😍*

*_________________________________________________________________*

🅿️-2️⃣8️⃣

________________________________________________________Dafa kafadarshi yaji anyi daga bayanshi ko bai juyo ba yasan yaya Salim ne,

Ganin bai juyoba yasa yaya Salim yace" kazo mu koma ciki kasan ba cikakkiyar lafiya gareka ba,

A hankali ya waiwayo kallon yaya salim yayi da idonshi da sukayi jajir tsabar bacin rai gefe guda kuma ga fargabar irin hukuncin da umma zatayi mai,

Kama hanyar yayi batareda da yacewa yaya Salim komaiba, dan baijin zai iya magana a halin da yake ciki,

Koda suka Isa dakin hajara na waya saidai suna shiga ta yanke wayar tana tambayarshi me ake ciki ne?
Inasu jiddar ne ko har ta tafi?

Ba wanda ya tankata a cikinsu, kwanciya yaya deeni yayi tare da lumshe idonshi, shikadai yasan yanda yakeji a zuciyar shi har wani d'aci da maqaqi yake ji,

Ya dad'e a haka kuma ba bacci yakeyi ba yanaji hajara tana qananan surutanta amma bai tankata ba, har cewa tayi  ai kamata yayi ka godewa Allah dayasa kagani da idonka da wani ya fada maka da bazaka yadda ba, yanzu sai kasan matakin dauka Allah yasa ma bata manna maka wata cutar ba kar anjanyo min wahala ina zaman zamana,

Nasha fada maka maganganu akan yarinyar nan baka ta6a dauka ba ai yanzu da idonka ya gane maka magana ta qare, nifa tun shigowata na hange su a motarshi to nadan tsaya gaisawa ne shine fa ya rakota nan gurin daka gansu da alama sallama suke...... Enough!!! Ya fada da qarfi tare da dukan katifar,

Wayaya dauko ya Kira Dr jamil yace yazo yabashi sallama, ba yanda baiyi dashiba akan ya bari Koda zuwa gobene dan ba'ama gama saka mai ruwan da suka saura ba, Amma yace zaije gida ya qarasa jinyar,

Tattara kayan dake dakin hajara tayi shi kuma ya Kira Salim a waya, da misalin sha biyu sukabar hospital din, gidanshi ya kaishi tare da qara yimai addu'ar samun sauqi sannan ya juya dan baishiga gidan ba.

A bangaren su jidda kuwa har suka Isa gida tana kuka ba Wanda yace uffan acikinsu har suka shiga falon,

Zama jidda tayi kan  kujera sai  lokacin umma tayi magana tace "tashi kije ki kwanta ki huta kinji jidda,

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now