chapter 35

281 10 0
                                    

♠♣♠♣♠♣♠♣
     ♠♣♠♣♠♣
            ♠♣♠♣
                  ♠♣

*BAN TSANESHI BA*

♠♣♠♣♠♣♠♣
      ♣♠♣♠♣♠
            ♣♠♣♠
                 ♠♣

*story and written by*
*Asmau jafar*
  *(Ummu abdulhakim)*
             &
*zainab mukhtar*
        *(ummu maryam)*
*Aminan juna 👭🏻*

🅿️-3️⃣5️⃣

____________Da isar ta komai ba tace da suba ta nufi ƙaramar ƙofar fita suma basu ce da ita uffan ba sai dai tana Isa gun taja birki ganin ƙofar a rufe, kallon wulaqanci ta jefa wa kabiru driver da baba mai gadi tare da miƙa hannunta cike da isa alamar su bata keys din.

Shiru kabiru yayi kamar baiga abinda tayi ba sai baba maigadi ne yace "hajiya daman Alhaji ne.... Katseshi tayi da cewar ba shi na tambaye ka ba dattijo, mukulli kawae nace ka miƙomin, saidai bata kai ga ƙarasa zancen ta ba taji horn ɗin deeni a ƙofar gidan, da sauri ta juya batare da ta sake ce musu komai ba, ganin saurin bazaiyi mata ba yasa ta haɗa da gudu dan kar ya taddata a tsakar gidan, da gudunta ta buɗe ƙofar falon ta shiga, har zata wuce ɗakin ta ta tuna tasaka mai aikin ta  ta gyara mata dakin deeni ai nan take gaban ta ya faɗi da sauri tayi hanyar dakinshi a ranta tana cewa to wai me ma ya dawo dashi gida yanzu?ai dai na kusa maganin ka, tana kai tsakiyar falon shi kuma yana shigowa, ƙara ɗaga ƙafa tayi sai dai lokaci guda ta dasƙare a gun ganin mai aikin ta fito daga ɗakin ɗauke da tsintsinya da mopa,

Wata tsawa da deeni ya dakawa matashiyar mai aikin ba iya ita kaɗai ba har Hajara saida ta tsorata bale mai aikin, faɗan me ya shigar da ita dakinshi ya fara mata kafin daga bisani yace ta wuce ta bashi guri, kallon zaki gane kuranki yayiwa Hajara yayi hanyar dakinshi, har ya dauko takardun da yazo ɗauka zai fita kenan Hajara ta shigo dakin, har zata fara abin nan da hausawa ke cewa tabarmar kunya da hauka ake naɗe ta taga ya basar baice komai ba saima janyo ta da yayi suka fito ya rufe ƙofar ya zare duka keys din, har ya juya zai wuce taga ai inma ya fita a haka to yaci bulus, hakan yasa ta sha gaban shi ta fara faɗa wai yana son zubar mata da kima ya wulaƙantata a gun masu gadin gidan ta, duk cin mutuncin da yayi mata bai ishe shi ba saida yaje can yayi mata, inda take shiga ba nan take fita ba shi dai baima tsaya Jin surutan taba yayi tafiyar shi.

A skul kuwa lokacin da jidda ke bawa su baby labarin sun shirya da yaya deeni kamar su dake ta, musamman baby, dan wannan karon har hafsat saida ta shiga maganar wai ita banza ce, haka suka taso ta gaba suna masifa, ganin sun hayayyako mata ne itama ta fara faɗa wai ai basuji tace zata koma gidanshi ba bale su taso mata, kuma ma ai ba shi ke dukan ta ba da zasu ce mata banza😏

Baki buɗe suke kallon ta da mamaki ɗauke a fuskar su, baby tace" eyyyyeee lallae yarinyar nan wato ke mai miji koh? To ai inkinsan wata baki san wata ba, dan wlh kwanan nan zan dawo da ina cewa sai karshen wannan semester zan koma gidan umma tunda munkusa fara exams amma na fasa gobe goben nan zan dawo inshallah to Inga ta karyar shirin, sai kuyi a gaban umma, dan kinsan Allah? bazan  fita in bar daki ba sai dai ku zauna a falo can a gaban umma kuyi, yar rainin hankali kawai ƙyatt😏

Sharesu jidda tayi dan taga alamar bazasu fahimci inda ta sa gaba ba, dan tace sun shirya ai ba tana nufin zata koma gidanshi ba, amma tun da haka suke gani gara kawai ta barsu a hakan, dan tasan in shekara za'ayi bazasu fahimce ta ba.

Ganin ta sharesu ne yasa tasake cewa "kuma kina ji ana magana amma kin share mu,

Jidda tace" ki ji min matar nan, to me zan ce muku? Naga dai ba tambaya na kuka yi ba bale in baku amsa, ba kuma wani bayanin kuka nemi ji daga baki na ba bale inyi magana, faɗan ku ne kukeyi na banza to me zance muku? 

BAN TSANESHI BAWhere stories live. Discover now