Part 1

45 1 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Bismillahir Rahmanir Rahim, wannan labarin ya faru dagaske sai dai dan abinda aka rage da aka kara, bamu yadda wata wani wata ta canza mana shi ba*

_Page 1&2_

Wata matashiyar budurwa che k'wance akan sallaya bayan ta idar da sallahn magriba duk da ba wani ar haske ar d'akin haka tayi k'wanciyar ta sai hasken wayar ta dake rik'e da eta tana dannawa, duk erin yanda k'annenta ke wasa ar t'sakiyar gidan hakan bai sa taji sun dameta ba dan tayi nisa wurin danna wayarta.

   Matsowa nayi ar hankali dan ganin mai takeyi haka hankalinta gaba daya yayi kan wayar, wani shafi neh guda ar Facebook take dubawa duk da ba chatting takeyi da kowa ba ga tarin message na mutane amma sam hankalin ya ba wurin yake ba dan dama chatting d'in ba wani burgeta yakeyi ba shiyasa dayawan masu tura mata saqo sukaji shiru ba ansa zasuta zaginta da mai girman kai, dalilin kuwa dayasa suke fad'in haka saboda wani hadadden picture'n data daura akan profile picture wanda duk wanda yagani sai yaji ta burgeshi matuka saboda kyawun da Allah ya bata da kuma irin girman gida da tsaruwar shi wanda tayi photon ar cikin shi, wannan kadai ya esa ya tabbatar maka cewa eta babban yarinya che mai ji da kudi da kyau hadi da ilimin zamani, wanda ar zahirin gaskiya ba eta bace hasalima iyayanta talakawa neh, mahaifinta yayi shekaru biyu da rasuwa d'aga eta sai kannen ta biyu da mahaifiyar su wanda take sai da kayan sanyi, rayuwa sukeyi cikin rufin asiri da k'wanciyar hankali sun rik'e mutuncin su da kuma talaucin su.

  Simrah yarinya che mai hankali da nutsuwa gata da hakuri da juriya tana da iliminta dai dai gwargwadi dan ta kammala karatunta na secondary sai dai bata cigaba ba, fanni ilimin addini ma Allah ya bata sani sosai hakan yasa mahaifiyar ta ke matukar alfahari da eta.

  Ko kadan Simrah bata k'etare iyakar da Allah ya ajiye su sai dai akwai ta da rashin son magana ko kadan batada hayaniya wannan dalilin neh yasa mahaifiyar ta siya mata wayan zamani saboda kadaici da kuma yi mata talla akan sana'ar da takeyi dan akwai wata makociyar su tai mata bayani akan yanzu kasuwanci yana tafiya ta hanyar Social media wannan shine ma abinda ya kara mata k'arfin siyan wayar bayan alk'awarin da tasa tai mata akan ba kula qawayen banza da kuma samarin banza sosai wayan ta rage mata kadaici da kuma zaman kuramen da takeyi dan banajin Simrah nada wata k'awa da za'ache yau gata har suna ziyarar junan wanda ar yanzu tayi shiru tana duba tarin message d'in mutane wanda har ta gama bata ansa ko mutum daya tare da ajiye wayar jin an fara kiraye kirayen sallahn isha'i.

ABUJA.

Wani tamfetsetsen parlo neh duk wanda yasa kansa ciki komai ni'imar dake gidansu dole ya jinjinawa t'sayuwar wannan parlon sanyi da kanshi neh ke tashi ar cikin shi ga wani tangamemen TV dake manne ar bangon wani film neh ke haskawa ar tashar MBC 4 ta dayan gefen naji takun mutum ana saukowa d'aga stair case d'in ar hankali na maida kaina wurin dan ganin waye.

Wata babbar macece wacce Allah ya zubawa kyau da diri tare da t'santsar baiwa ta fanni daban daban take saukowa murmushi neh k'wance ar saman fuskarta tasha wani uban su lace mai daukar hankali kallo d'aya zaka mata zaka gano ruwan shuwa tattare da eta sai wani kamshi take zubawa kaman tayi barin turare ar jikin ta, d'aya d'aga cikin kujerun ta samu tare da zama, zaman ta kenan wata baby mai kyau chocolate color wacce bazata wuce shekaru 10 ba tasha doguwar riga ta shadda wacce ta kara fitowa da ainihin kywunta da kalarta.

  Cikin muryan ta mai sanyi take fad'in "Mommy kinga Yaya Samir yaqi bud'emin kofan d'akin shi nayita knocking yamin banza yaqi kulani" ta kai karshen maganan kaman zatayi kuka.

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now