*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
*Akwai wadanda suka biyo ni private jiya akan enhar Samir na son Simrah da gaske toh bai kamata ya guje ta ba kusan mutane biyar neh dan Allah tun farkon page 1 edan baku manta ba na sanar daku book d'in nan ya faru gaske sai dai abinda aka canza so ku cigaba da bin shi yadda yake beside ma waya che muku ya rabu da eta kenan oh dan Allah labarin nan ar tsare yake kawai dai ku cigaba dabi muna godiya*
*{Page 25....26}*
Daddyn Salma neh zaune ar parlon shi yayinda Mamin Salma ke zuba mishi abinci dan dawowan shi kenan d'aga Cairo wani business da suke running shida Samir kuma Alhamdulillah sun samu nasara Mami na mishi hira.
"Daddyn Salma gaskiya yanzu yakamata ache ka samu hutu kaga shekaru sun ja kaima ka samu ka huta kaima hakan nan"
"Uhm Mamin Salma yanzu ke ar tunanin ki sai na bar wannan tarin dukiyan da mahaifin Samir ya bar mishi duk dama yaron nada kokari, edan har na bar mishi banyi ma Alhaji adalci akan dukiyar shi ba tunda dai kinga su uku kadai Allah ya bashi kuma Samir kadai neh namiji sai Fadila neh fa sai kuma Siyama kinga kuma Fadila tana England bata dawo ba abubuwan zasu mishi yawa, zan cigaba da rik'e amanar su insha Allah har lokacin da karfina zae gaza"
"Shikenan tunda haka kace kuma kake so amma abinda yake daurin min kai shifa yaron nan Samir bai tab'a zuwa gidan nan wai da sunan gaisuwa ba ko wani abu"
"Banason ki damu da wannan nasan halin Samir ba irin wannan mutanan dake da kazarkazar bane duk da yaron nan na bani girma yana gani na tamkar mahaifin shi duk lokacin daya ga ya dace yazo da kanshi zai zo"
"Toh amma" shii ya kat'se mata maganar da zata sake dan baya son maganan ma k'wata k'wata"
"Ena Salma neh wai bangan ta ba?
"Tana d'akin ta" bai yi magana ba sai daya kai loman abinci.
"Ar gaskiya nagaji da ganin wannan yarinyar haka zaune karazub'e eta kadai che Allah ya bamu ena son sauke nauyina na mat'sayin mahaifinta ena son aurar da eta da kaina rayuwa da mutuwa duk da baka san waye gawar fari ba, na bata dama dayawa amma yarinyar nan taki sannan bana son na shiga hakkin ta kingane ai dan haka ki sanar da eta na bata nan da wata biyu ta fiddo wanda takeso edan ba haka ba duk wanda na yaba da tarbiyan shi zan aura mata shi"
"Daddyn Salma amma baka ganin wata biyu ya mata kadan anya Salma fa babu wanda take kulawa fa eta ma d'in shegen taurin kai amma zan mata magana"
"Yafi kam ki sanar da eta"
"Insha Allah" hirar su suka cigaba dayi mat'sayin mata da miji abinsu.
**************************
Samir na k'wance saman gado daka kanshi zaka san baya cikin walwala.
"Man k'arfe 4 jirgin ku zai tashi akwai abinda kake bukata neh? Bai bashi ansa ba sai girgiza mishi kai kawai dayayi cikin nazari shima Faruk yake kallon Samir d'in da tun sanda sukaje gidan su Simrah yanayin shi ya canza gaskiya yarinyar nan ba karamin cutar abokin shi tayi ba wallahi da zae ganta rashin mutunci zae buga mata Allah neh kadai ya sani kuma ko mai nene zai wuce cikin sauki insha Allah.
"Samir dan Allah dan annabi ena son ka cire wannan damuwan ar ranka yarinyar nan tunda ka gane dawa kake tare ka gane waye eta sai ka barta ga mata nan iri iri ar gari hadaddu ajinka nasan duk yadda kaje wurin mace bazata guje ka ba, kaga fa yanzu enhar ka koma gida Mommy zata san halin da kake ciki dan Allah ka daina damuwa edan kuma eta Simrah d'in kake so sai mu koma wurin ta" wannan maganan da Faruk yayi shine yasa shi jefa mishi wani wawan kallo dan tun dazu yaki d'agowa sai na ya koma wurin Simrah edan shi sun canza launi t'saban b'acin rai.