*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
*{Page 43....44}*
Mommy na t'saye dai tana sababi Samir na lure irin kallon da Khamis ke mishi sarai kuma yasan ma'anar wannan shegen kallon nashi na tsokana da shegen surutun shi wanda magana ke taf ar ciki bai ko kula shi ba.
"Toh Mommy mu zamu tafi" fad'ar Khamis
"Malan nace maka nagama neh bace min ni dagani"
"Wai Samir miye kake min haka neh tun yaushe na fad'a maka na kirata kan kuna tahowa ko su kake raina ya b'aci neh?
"Allah baki hakuri Mommy yanzu zamu tafi" kwasar wayoyin shi yayi tare da saura agogon shi har suka fito sai ga Siyama etama ta fito.
"Laa Yaya ena zakaje kayi kyau sosai kaman ba kai ba"
"Unguwa zamuje Siyama"
"Yaya kayi kyau sosai"
"Thanks lil" ya fad'a tare da fita waje.
"Toh Siyama ayi mana addu'a Allah yasa Auntyn ki ta karbi yayanki" cikin rashin fahimtan maganan take kallon shi.
"Yaya ena zakuje?
"Wurin Auntyn ki da kike magana kullum wama kike kiran ta Salma koh"
"Laa Yaya shine bazaka fad'a min muje tare ba"
"Kar ki damu Siyaman Samir next time dake za'aje"
"Tohm shikenan Allah ya bada sa'a bye bye" Mommy ma da addu'a dacewa ya fita haka Khamis ya rik'a tsokanan Samir k'arshe dai haka ya shiga kunshe dariyan ba tare da fad'in komai na ganin Samir ya cika kaman zae fashe tare da kama hanyan gidan su Salma suna tafiya neh tamkar wasu baki Samir yaqi ba Khamis daman yin wani surutu sam shi bai so haka ba,banda mahaifiyar shi che ta sa shi wlhy da bazai je ba dan Mommy ta wuce duk tunanin kowa da zata fad'a mishi abin yaqi yi ar dai dai k'ofar gate d'in gidan Alhaji Jibril suka t'saya mai gadi ya bud'e wayan Samir d'in neh ta shiga kara ganin Faruk neh yasa shi dauka.
"Man yanzu kai tunda ka koma ka cigaba da halin naka neh koh ba gaisuwa ba komai naji shirun yayi yawa har sako na turama ar WhatsApp amma baka duba ba" cikin fitar da numfashi mai zafi Samir ya mishi magana.
"Sorry Faruk jiyan neh bana jin dadi so yanzu haka ma ka ganni munada wani uzuri neh gamo hanya"
"Hanya kuma ena zakaje?
"Mommy che ta aikemu"
"Mommy che ta aike ku ko dai kuka aika kanku"
"Uhm kaji bana son surutu nikam ga Khamis nan ma"
"Oh ok bashi toh daman tun dazu nake kiran shi wayan bata shiga" Khamis koh kaman jira yakeyi ya kyalkyale da wata muguwan dariya shima Faruk dariyan sae ya bashi dariya.
"Ya ake ciki neh ena ta kiran ka wayan taqi shiga"
"May n network neh gani da mutumin zamuje hira" cike da mamaki Faruk ya tambaya
"Hira kuma Samir din neh zai je hira wurin wa?
"Oh toh gani nan dai nima dan jagora neh bansan ya ake ciki ba tafiya kawai muke"
"Amma nayi mamaki Khamis ya samu wacce yake neman neh?
"Ena fa Mommy neh ta tada mishi hankali tare da mishi mata wai dai ar taimaka mai saboda ya zama tuzuru" jin abinda sukeyi yasa shi karb'e wayan ya kashe tare da t'saki.