*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
_Page 13&14_
Washe gari.
Da wuri Samir ya tashi yayi shirin office d'in shi sai dai kuma yana jiran kiran Simrah kamar yadda ta sabayi amma sai yaji shiru hakan neh yasa shi kiran ta bugu biyu kuwa ta dauka duk da daman ta gama aikin da zatayi.
"Assalam alaika baby"
"Wa'alaiki salam very own kin tashi lafiya?
"Ena kwana" tace dashi
"Lafiya kalau ya daren ki ya kuma Mamana?
"Mama tana lafiya kalau yasu Mommy?
"Alhamdulillah duk suna lafiya"
"Masha Allah yau ban kira ka enata aiki neh shiyasa am sorry"
"Kar ki damu princess dita yanzu zan tafi office amma kafin na tafi yau ena so naga kyakyawar fuskarki amma fa Video call zamuyi" wani irin mird'awa taji cikin ta yanayi sai ta basar dashi kaman bata ji ba sai da ya sake mata magana.
"Very own bakiji abinda na fad'a bane?
"Eh baby mai kace?
"Enaso naga fuskarki kafin na fita amma fa video call zamuyi kafin nazo naganki gaba da gaba"
"Wai baby nifa ban tab'a yin wannan video call d'in ba t'soron yin shi ma nakeji"
"Nima kinga ban tab'a yi ba amma yau akan ki zan fara"
"Oh toh shikenan baby kira ni toh"
"That's my girl" ya fad'a tare da kashe wayan b'angaranta kuwa yana kashewa ta kashe wayar dukkan ta Allah sarki yana ta zaman jiran ta yaji shiru k'arshe sai kiranta yayi yaji wayan ta ar kashe.
"Wai meyake faruwa neh da Simrah wannan abun tayi min dana tambayeta address d'in ta yanzu kuma ta sake kashe wayan oh may be Mama neh tayi kiran ta" shi kadan shi yayi ta magana kafin ya fice ar parlo ya tadda Mommy tasan yana azumin monday da friday shiyasa ma basuyi girki dashi ba.
"Mommy ena k'wana"
"Lafiya lau Samir an fito"
"Eh Mommy"
"Toh Allah ya bada sa'a koh ar kula da kai kuma tunda dai anki ayi aure har yanzu"
"Mommy zaki sha mamaki na ke kam na kusa hutawa da wannan gorin naki"
"Allah yasa daka bani mamakin gaske kenan"
"Ana tafe ni zan wuce kada na makara"Allah tsare tayi mishi kafin ya fita zuciyar shi na cike da tunanin abinda Simrah tayi mishi hakan nan ya daure ya kai kanshi office.
****************
Zaune suke Salma tana bama Aisha labarin da kuma company d'in shi wanda JJ ya samo mata sai dai banda gidan su sai da Aisha ta gama sauraranta sannan tayi magana.
"Toh Salma yanzu miye abinyi?
"Tashi zakiyi mu tafi company d'in nashi dan Allah dan na ganshi"
"Ni kuma sai nake ganin gaskiya Salma kar kiyi haka gwara ki rik'e kanki da abinda kikeji ar kanshi har Allah ya had'a ku"
"Tayaya zamu had'u Aisha muna gari d'aya amma had'uwan mu ya gagara"
"Kar ki damu insha Allah kun kusa had'uwa akwai wani friend d'in su Haidar ar kaduna yake so saura sati biyu auran shi amma anan zasuyi dinner dan nan amaryan zata zauna kinga mun samu hanyar da zaku had'u dashi kenan etace mafi sauki"