Part 6

6 0 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/FJR2jsNrkFxG6MDDtqmK7X

*Edan har kinsan bazaki eya comments ba toh kada ki shiga dan ko kin shiga zamu cire ki*

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

_Page 11&12_

Zaman sukayi kan bakin katifan Amina kamin Simrah ta deba ruwan da Aminan ta kawo mata dan tasha sai da taji wata nutsuwa tukun ta cire hijabin ta dan tana jin zafi.

"Simrah tabbas ba sai kin fad'a min ba ganin fuskar ki kadai yasa na gane chewa kina tattare da damuwa amma wani irin damuwa neh haka take damunki"

"Soyayya" Simrah ta fad'a tana kama hannun Amina k'warai Amina tayi mamakin jin furucin Simrah baki galala take kallon ta.

"Kina nufin kin fad'a cikin tarkon wani kenan kin t'sunduma cikin kogin son shi"

"Amina tabbas na t'sunduma cikin son Samir wanda kuma bansan ya zanyi ba"

"B'angane ba bai son kina son shi bane ko yaya? Amina ta tambayeta.

"Amina banida wata k'awar data wuce ki bani kuma da wacce zan eya zuwa na fad'a ma wannan maganar edan bake ba wacce ko Umma banjin zan sanar ma abinda yake faruwa, nasan ke k'awata kuma enada tabbacin bazaki tab'a fad'a ma wani wannan sirrin nawa ba shiyasa nazo wurin ki dan ki bani shawara"

"Simrah fito fili kimin dalla dalla yadda zan fahimta kinji"

"Shikenan amma kar ki min kallon wani abu daban da farko na dauka hotunan ta da nake sakawa ar Facebook dina ba komai bane sai gashi yana barazanar rabani da masoyin dana kamu da son shi"

"Ke nifa ban fahimta abinda kike nufi ba" Amina ta fad'a tana kallon Simrah.

"Amina akwai wata friend dina che ar Facebook sunan ta Salma ke kina ganin fa kinga kyau kudi da kuma hutu, tana yawan sakan pictures d'inta ar shafin ta na Facebook ni kuma nake saving d'in su nima na daura akan shafi na mutane dayawa suka min magana nayi banza dasu wanda nasan dalilin wannan hoton neh yasaka su suke min magana har ta kai da wasu ma zagina sukeyi da mai girman kai, ana haka wata rana wannan Samir d'in ya min magana...." Kaf labari Simrah ta sanar da Amina bata b'oye mata komai ba har ta kai k'arshen zancan tana sake riko hannun ta.

"Lallai Simrah bansan baki da wayau ba sai yau wannan wani irin gidadanci da rashin wayau, kar kiche min kina d'aga cikin irin matan da suke saka pictures d'in mutane ar profile d'inki haba Simrah yanzu kin cutar da kanki kuma kin cutar da wacce kike saka  pictures d'in nata"

"Amina b'angane na cuceta ba"

"Abu na farko ke kin cutar da kanki kinsan dalilin dayasa na fad'a miki haka?

"A'a Amina sai kin fad'a"

"Shin ar lokacin daya fara miki maganan baki tab'a tunanin zai che yana son ku had'u ba son aure na tsakani da Allah fa yake miki, shin baki tab'a tunanin halin da zaki shiga ba edan har ya gane gaskiya, shin baki tab'a tunanin zai eya  gudun ki ba edan har ya gano gaskiyar dawa yake tare kinga ai kin cuci kanki koh"

"Inalillahi wa'inna illaihir rajiun Amina bana fatan haka duk da ar yanzu nima wlhy nayi dana sanin abinda nayi wallahi nayi dana sanin sanya hoton daba nawa ba yanzu ya zanyi Amina amma eta mai yasa kika che na cuceta?

"Yauwa Simrah eta wacce kike daurawa akan profile d'in shin baki tunanin tanada aure, baki tab'a tunanin enhar tanada aure ba wasu suka kamu da sonta da ganin irin kyan da Allah yayi mata da kuma surarta har suka ji wani abu kanta shin baki tunanin irin zunubin da take dashi wurin ubangiji, haba Simrah da hankalin ki da kuma wayon ki mai ya kai ki da irin wannan abun dan Allah?

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now