Part 24

9 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 47....48}*

Yana zaune ar office yana duba wasu files yaji ana Knocking izinin bada shigowa yayi kafin ya zauna suna sake gaisawa kallon Faruk Khalil yayi sosai kafin ya mishi magana.

"Faruk ya na ganka haka lafiya? Cikin gajiya sosai daya ke jin jikin shi yayi ya bashi ansa.

"Khalil lafiya dai ba lafiya ba yama zance maka ko zan saka abin neh kanwata dai tunda bayan ni yanzu basuda kowa kusa take k'wance ar asibiti batada lafiya edan ka ganta karama amma wai ciwon zuciya"

"Subhanallahi ciwon zuciya kuma menene?

"Nima bansani ba" ya fad'a dai bai jin zae eya sanar  da Khalil dalilin Samir neh ta kamu da wannan ciwon.

"Oh ya Allah"

"Wallahi fa Khalil ka kirani kana son ganina shiyasa nazo sae na koma asibitin saboda na bar Umma eta kadai chan wurin ta ena son musu take away da abin bukata dan ban bar musu komai ba en maganan ba mai tsayi bane muyi dan samun time d'in komawa"

"Dama maganan ba wata mai t'sawo bane kan wacce nake son aura neh nake son muje anjima ka ganta kafin na kai ta gida"

"Wash Khalil kaga yanzu halin da ake ciki amma yanzu ba lokacin nan edan nace zan raka ka hira ba zae yiwu ba sai dai zuwa k'wana biyu haka sae muje"

"Shikenan Faruk ai kana tare da uzuri na maka amma ban eya jira zuwa k'wana biyu sai dai ko zuwa gobe haka"

"Ba damuwa Khalil bari naje" sallama sukayi ya fita kafin ya shiga kiran layin Umma wanda yasamu da k'yar sai data kusa yankewa sannan aka dauka jin ba Simrah bace yasa cikin girmamawa suka gaisa.

"Umma ena yini"

"Lagiya lau amma bangane wake magana ba"

"Uhm dama ni neh wanda nake zuwa wurin ta ena son zanyi magana da eta neh"

"Masha Allah sai dai yanzu bata kusa sai dai zuwa gobe haka sai ka kira"

"Daman ena son zuwa neh saboda tace zata min eso dan gaidaki" kallon Simrah dake k'wance tana bacci bata farka.

"Toh gaskiya dai muna asibiti neh yanzu haka" mik'ewa yayi kaman na gaban ta.

"Umma waye ba lafiya mey ke faruwa?

"Eh toh gaskiya dai Simrah che bata jin d'adi"

"Umma wani asibiti neh"

"Yana nan dai wai asibitin Dr Isma'il"

"Oh nasan asibitin abokina neh"

"Toh muna wannan asibitin edan ka tambaya Simrah Abubakar zasu kawo ka"

"Ba damuwa insha Allah zan shigo yanzu na"

"A'a ka dai bari zuwa gobe koh" girgiza kai yayi kaman yana gabanta.

"A'a Umma bazan eya jiran gobe ba gani nan zuwa"

"Toh Allah kawo ka lafiya" d'aga nan ta kashe wayan ya kwashi wayoyin sa duk tarun aiyukan dake gaban shi haka ya tsallake ya barsu yana fitowa sakatariyan shi ta mishi magana.

"Sir akwai bakin da zaku gana anjima"

"Ki basu hakuri enada uzuri mai muhimmanci yanzu bazan samu ganawa dasu ba dan bansan yaushe zan dawo ba sai dai zuwa gobe"

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now