Part 19

7 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 37....38}*

Salma che ta fito d'aga d'akin ta tana sanye da kayan bacci fuskan ta duk ya kumbura tasha kuka har ta gode Allah Mami na kallon ta bata che da eta komai ba gaishe da Mamin tayi ta k'arban ba tare data nuna wata kulawa cikin gaisuwan Salma ba kitchen ta shiga ta fito dauke da cup hannun ta dinning ta nufa ta zauna tayi shiru Mami ta duba bayan ta.

"Uhm yarinya kenan ai kadan ma kika gani dan baki san halin Daddyn ki bane" ta lura tun sanda Daddyn ta ya kirata ya mata magana akan auran Samir yasata kara sukurkucewa ta wani fita hayacinta shiyasa Mami ma ta fita sha'anin ta dan an nuna mata bata kai ba kasa shan ruwan tea din tayi wanda komai bata saka ba ta mik'e wurin Mamin ta tayi tana duban Mami.

"Mami dan Allah enche wani abu?

"Eh zaki eya cewa amma en kin tabbatar da maganan bata shafi abinda Daddyn ki ya fad'a miki bane"

"Mami akan ta neh dan Allah kisa baki Mami wallahi bana son wannan mutumin da Daddy yayi magana akan shi Allah akwai wanda nakeso Mami dan Allah" cike da takaici Mami ke kallon diyar tata.

"Toh ena shi wanda kike so d'in? Shiru tayi dan bata da abin cewa.

"Mami wallahi zan kawo muku shi kuyi hakuri ku kara min lokaci endai har lokacin da kuka daukan min yayi ban kawo shi ba na yadda Mami"  murmushin manya Mami tayi tana magana.

"Ai kin makaro Salma wallahi gwara ma ki cire wannan shashashan tunanin ar ranki anya ko kin sani enhar na saka baki cikin wannan maganan bake kadai ba hatta ni ran mu sai ya b'aci cikin gidan nan gwara ki saduda dan enhar kinga  wannan auran bai yiwu ba toh tabbas Allah neh yayi bashine mijin ki ba amma enhar mune iyayan ki toh Simrah bakida miji kamar Samir" fashewa tayi da kuka tare da mik'ewa tayi d'akin ta da gudu wanwar ta fad'a kan gadon ta tana surutai.

"Wallahi bana son shi zan eya mutuwa endai aka aura min shi nasan cewa iyayan Siyama neh kuma ena sonta sannan kuma yayan ta neh kuma ena son Mommy amma wallahi shi wannan bana san shi duk da ban tab'a ganin shi ba" hakan nan tayi ta surutai eta kadai tana kuka kamar wacce akayi ma mutuwa nikam dai wannan Salma akwai sakara😏.

   ******************************

Samir na zaune neh ar katafaren office d'in shi babu abinda kakeji sai kukan tsuntsaye da suke bayan window d'in dan mug ya kai bak'in shi wanda coffee neh cikin shi yake sha yana saukar da cup d'in yana kuma dannan system dake gaban shi Knocking d'in kofan akayi  izinin shigowa ya bada still hankalin shi na kan system d'in shi jin muryan masinjan shi yasa shi d'agowa sanar dashi yakeyi akan wani meeting da yake da shi PA dinshi ya sanar dashi cewa yazo baya nan amma ya bar mishi sakon ya fad'a mishi kuma k'arfe hudu neh meeting d'in kuma ya kira wayoyin sa ar kashe ba tare daya yi magana ba ya girgiza kai wanda hakan yasa masinjan gane cewa ya ansa maganan kenan dayayi wannan maganan da masinja yayi neh ya sanya shi tuna fa ya taho wayoyin sa ar kashe  kunna su yayi text message na PA dinshi ya shigo kan ayi mishi afuwa an mishi rasuwa kuma ya kira bai samu ba gashi za'a yi meeting k'arfe 4 koda ya gama karantawa bai reply nashi ba ya kira Mommy bugu biyu kuwa ta dauka.

"Mommy nayi mantuwa neh wlhy nake son fad'a miki"

"Mantuwan mey kuma Samir?

"Akwai wasu takkadu Mommy ar dakina masu mahimmancin kuma ya dace na fito dasu saboda akwai meeting da zamuyi dasu k'arfe 4 gashi na manta so shine nake son ar bama driver ya kawo min"

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now