Part 25

7 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 49....50}*

Umma na zaune da Amina yayin da take jin bayanin Amina tsakanin Samir da Simrah har ta kai k'arshe.

"Umma dan Allah kiyi hakuri kima Simrah afuwa wannan abun ya faru bada san ranta ba Umma kiyi la'akari da kaddaran mutum an riga an rubuta haka dole sai ya faru da eta dan Allah kiyi hakuri wannan dalilin neh yasa ta ar cikin wannan halin badan kin riskemu lokacin da muke maganan ba Umma da bazamu taba fad'a miki wannan abun ba dan munsan dole ranki zae bac'i, Umma ki hakuri wallahi tayi neh bada son ranta ba" numfasawa Umma tayi tana kallon Simrah dake share hawayen ta.

"Bakomai Amina na fahimce ki sannan etama na fahimce ta sai dai banji dad'in boye min da kukayi ba yanzu da ban taddaku kuna maganan ba bazaku fad'a min ba haka zakuyita boye abu ar rai yana damun ku,nasan halin Simrah yarinya che mai zurfin ciki daman banyi tunanin zata fad'a min ba amma Amina harda ke amma ba damuwa nasan yarinyata ke damun ku sannan wannan abin data sanya ar ranta babu yadda zai kaita sai dai na mata uzuri kuma ena mai rokon Allah ya bata lafiya ya kuma yaye mata abinda ke ranta ke kuma" tana duban Simrah

"Wannan abin daya sameki bazan che bai kamata 'ya mace ba sai dai na miki uzuri kuma ya zame miki izinah da kuma masu yin wannan abun domin ramin karya kurarre neh lokacin shi dole zai wuce da kin fad'a mishi gaskiya da haka bata faru ba don na tabbata enhar sonki yakeyi da gaske toh zai bukaci ganin hoton ki sannan ba zae bari ki zurfafa cikin son shi ba en har baya sonki dan na tabbata ar lokacin da zae bar ki ai ba bin shi zaki cigaba dayi ba amma boye mishi gaskiya da ki kayi shine ya jawo haka tunda ya tafi kinga ya kara neman ki? Girgiza kai tayi alaman a'a.

"Toh Simrah ena mai miki nasiha da kiyi kokari ki cire wannan yaron akan ki dan babu yadda son shi zae kai ki gashi kinga dai halin da kike ciki sannan ki dage da addu'a nima insha Allah zan cigaba da miki addu'a en son shi ba alkhairi bane Allah ya cire miki shi"

"Umma nagode da kwarin gwiwan da kika bani nagode Umma ma wanda ar baya na rasa shi sannan kiyi hakuri dalilin daya sa na boye miki nasan hankalin ki zae tashi shiyasa amma insha Allah bazan sake boye miki abu ar kaina ba kuma nasan nayi kuskure ena mai neman afuwa wurin ki da wurin ubangiji akan abinda nayi Allah ya yafe min kan karya da kuma yaudaran da nayi mishi kuma insha Allah edan Allah ya sake had'a mu zan neman yafiyan sa akan abinda nayi"

Murmushin karfin hali Umma tayi tana kallon ta.

"Haka nake son ji kuma Allah ya yafe mana gaba daya" Amin suka amsa cikin k'arfin hali etada Amina.

"Umma insha Allah akan wannan abin bazan sake zubar da hawayena ba  endai akan Samir neh daga yau zanyi kokarin mantawa dashi duk da yana da wuya amma bazai sake zuba ba" cikin jin dadi Umma take kallon ta.

"Ko kefa 'yar albarka" cikin jin dadi Amina ta rungume Simrah.

"Gaskiya Simrah naji yau kin burgeni insha Allah ubangiji zai miki zab'i mafi alkhairi" kai kawai ta girgiza ma Amina Umma ta kalla Amina.

" Amina had'a mata tea koh sae ta sha"

" Umma ena son nayi brush bana jin dad'in bakina"

"Kina  eya tashi ko Amina ta tayaki?

"Umma toh gaskiya bana jin dad'in jikina sosai sai an taimaka min"

"Toh Amina dafa mata sai na had'a tea din" tuni Amina ta taimakawa Simrah sukayi toilet yayinda Umma ta had'a mata tea tare da kabe mata wurin k'wanciyar nata saboda gadon ya turmushe sakamakon kukan da sukata Yi dan shi kanshi Faruk bai ji ba sai data shigo tukun ya fita shi kuma ya fita Umma taji dad'i sosai dan tasan ko ba  komai damuwan dake damun yarinyar nata zai ragu fitowa sukayi daga toilet tare da zama kan gadon Amina ta mik'a mata tea din.

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now