Part 14

6 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 27....28}*

Washe gari Samir neh zaune da Siyama akan dinning su biyu ba tare da kowa ba shigowa Mommy tayi tare da zama kusada Siyama tana facing d'in shi zuba mishi ido tayi ganin duk ya rame yayi wani iri alamun abin na tab'a zuciyan shi kenan har lokacin kiran sunan shi tayi wanda yasa shi d'agowa yana ansata.

"Na'am mommy"

"Daman magana zan maka kan Fadila ta kirani tana bukatan kudi ar tura mata duk abinda Allah ya hore koh" kallon mommy yayi yana magana.

"Mommy gaskiya yarinyar nan tana da kashe kudi kuma kike goya mata baya bamu san mai takeyi da kudi haka ba edan muka duba ba kusan ta so bamu da tabbacin mai takeyi da kudi haka ta amma tana waje ba'a sati bata kira tayi complain din kudi ba ki bari zan kirata da kaina zamuyi magana"

"Toh naji kafin nan ka tura mata duk da baka san miye uzurin ta ba edan har ka tura mata nida kaina zan kirata nayi mata warning kan karb'an kudi ko ta kuma kira bazan mata magana ba"

"Shikenan ni bari naje d'akin Mom d'inku ta dan k'wana da zazzabi jiya"

"Subhanallahi Mommy ai koh ban sani ba"

"Eh dake dai jiya neh kawai ni na tafi" mik'ewa tayi tare da wucewa shi kuma ya zuba ma Siyama idanu tana cin abincin ta hankali k'wance babu wata damuwa tattare da eta bata san komai na rayuwa ba bata san ya duniya take ciki ba babu abinda ta sani sai farin ciki wanda shima haka yake ar baya bai san wata damuwa ba sai da Daddyn shi ya bar duniya tun bayan rasuwan neh duk da yasa dangana amma wani abu sai ar hankali toh tun bayan wannan lokacin bai sake sanin wata damuwa ba sai 'yan kwanakin nan da wannan abin ya faru Allah ya kawo sauki ar duk wani lamari nashi abinda yake fama kenan.

"Babyn Yaya" ya ansata ar hankali.

"Na'am Yaya"

"Ar ena kika samu wannan cake d'in da kika bani jiya kinga jiya shi naci da tea kuma ya min d'adi edan zamu fita shopping sai mu biya mu siya koh" cike da farin ciki da murna ta bashi ansa.

"Laa Yaya Aunty Salma neh fa tayi da kanta dana tashi dawowa shine ta bani"

"Ok amma meyasa ranar dana zo daukan ki baki bani ba"

"Yaya na manta neh amma yanzu ai na baka dana ganshi ar cikin kayana saboda na manta tace zata bani kuma ka tafi shine yasa na ajiye maka" hakan nan kanwar tashi take burgeshi.

"Ya za'ayi na sake samu yanzu kuma?

"A'a Yaya ai kiran ta kawai zanyi ta min sai muje mu karb'a"

"A'a ki barshi ba sai kin kirata ba Siyama ki barshi kawai edan muka fita sai mu duba ko zamu eya samun shi" ba tare data amince bazata kira shi ba ta ansa shi da toh Yaya.

Bayan sun tashi yayi wurin small mom eta kuma tayi d'akin Mommy duba wayan Mommy takeyi anan taci karo da numbern Mamin Salma take ta kira ta kuwa bugu biyu Mamin Salma ta dauka.

"Mami" jin muryan Siyama yasata murmushi.

"A'a Siyama kece?

"Eh Mami ena k'wana?

"Lafiya lau ya Mommyn ki?

"Tana lafiya Mami ena Aunty Salma"

"Tana d'aki ar bata neh?

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now