End

14 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*END😔*

Ar washe garin ranar da misalin k'arfe 11 aka daura auran Amina da Faruk sosai mutane suka taro suka kuma shaida bikin duk wani abun daya dace ache anyi na hidiman babu wanda basuyi ba mutane dai sun taro fam gidan su Amina kai harma da gidan su Simrah dan an sauke wasu baqi ma achan Simrah kuwa sai tsokanan Amina etama takeyi tun bata biye mata har sanda suka fara halin nasu su Ramlat na musu iskanci hakan nan aka zauna zaman yini har 4 tayi daman Faruk yace da yamma za'a zo daukan ta sanda motoci suka zo kuwa Amina kuka takeyi eya kuka Mama da Umma nata mata nasiha hakan nan aka tafi da eta tanaji tana gani kaman yadda suka kai Simrah haka yanzu ma etace ar gefen ta tana lallamin ta su Khalil abokan ango su suka zauna musu dan abinda baza'a rasa ba ana zuwa tafiya kuwa ya tsunkuce amaryan shi sai gida dan yayi matukar missing dinta.

"Boo yanzu dan Allah mey zance dasu Umma en suka tambayeni fa?

"Mijin ki na bukatar ki shine ansan"

"Tayaya kake tunanin zan eya fad'a musu haka haba boo"

"Ni zan fad'a musu ai kar kiji komai edan Umma taji shiru tasan muna tare kuma ko ta kira ma ni zan dauka"

"Ai kuwa sae dai kai din ka dauka amma bani ba" suna wannan maganar suka karasa shigowa gidan suna shiga parlon ya jawota jikin ta wani nayen kiss ya shiga bata ta ko ena etama batayi kasa ar gwiwa ba ta bada kai da haddin kai kuma anan suka shiga nuna ma junan su yadda kowa yayi missing din dan uwan sa nima kuwa na basu wuri.

Salma duk wani abinda zatayi na gyara gida tayi shi hakan nan ta daure ta mishi girki cikin ta na wahalar da eta duk tayi wani iri kaman ba Salma ba amma gayen nan yana nan abinta damas da eta tana k'wance ney ar parlo kuma ar kasan tiles Samir ya shigo gidan ganin ta k'wance babu wani kayan arziki jikin ta kuma ar kasa ga yanayi na sanyi daya fara shigowa ga ACn dake aiki amma wai ar kasa take zaune yasa shi karasowa wurin da sauri yana dagata.

"Baby lafiya kike k'wance ar kasa tashi dan Allah"

"Honey sannu da zuwa"

"Sannu kema tashi" hannu ta mik'a mishi ya dagota ya zauna kan kujeran ta kwanta jikin shi.

"Meyasaki kwanciya ar kasa baki san ciwo zae eya kama ki ba kuma kinsan bake kadai bace"

"Hakan nan sanyin tiles din ya min dad'i shiyasa na k'wanta amma bazan sake ba insha Allah"

"Yauwa 'yar albarka tashi yanzu muje mu siyo abinda zamu ci"

"Na maka girki yana dinning"

"What banace kar kiyi ba ki huta"

"Honey toh ai naji sauki shiyasa nayi maka tashi muje kaci"

"Ke kinci ney?

"A'a oath kawai zan had'a"

"Toh kinsan ya za'ayi bari na had'a miki sai kisha nima naci nawa amma da kin daure kinci ko kadan ney"

"Nidai gaskiya bana so oath dina kawai nake so"

"Duk yadda kika che haka za'ayi" da kanshi ya had'a mata oath din sai daya tabbatar data koshi sannan shima yaci nashi taimaka mata yayi suka gyara wurin suna wannan yanayin Mommy ta kira shi akan tana son ganin shi kan maganan Fadeela da Khamis kwarai yasha mamaki mai sukayi haka sai data mishi bayani dalla dalla tukun ya gane kafin sukayi sallama yace mata zai zo gobe iyye ashe Khamis shiyasa baya tab'a zancan budurwa yasan yadda ajiyar sa take oh no wonder zae che shi mace bata gaban shi tashi na nan ar ajiye sunyi soyayya shida matar shi kamin kuma ar bingire da bacci.

Washe gari Simrah da wani irin kunya taje gida amma Umma ta nuna kaman bata san ma mey tayi ba ganin haka yasa ta sake aka shiga deban ma Amina sauran abubuwan da zasu kai mata ayarin yan zuwa gidan tabi sai gidan Amina hakan suka cika gidan da ihu sai hira labari yaqi karewa har sauran suka tafi Amina da Simrah kadai ney suka rage hiran su sukai tayi kaman yadda suka saba abinsu suna bama junan su shawara har yamma ta gabato Khalil yazo ya dauketa sukai gida dan jama'an biki kam duk sun watse sai san barka.

Tun bayan bikin Amina Khalil da Simrah suke shirin komawa kuma kullum gidan Umma take yini wata rana kuma gidan Mama ar haka suka karashe hutun da zasuyi suka tattara tare da komawa chan yadda suka fito bayan Simrah ta loda lodin lodin kayan kwadayin da ta san bazata samu ba.

Ar gurguje Alhamdulillah karatun Simrah na tafiya dai dai yadda ya kamata sai godiya kullum cikin sauke hakkin junan suke sai dai rayuwan ma gaba dayan ta 'yar hakuri che dole zo mu zauna zo mu saba ney b'angaran Salma da Samir ma ba'a cewa komai sai hamdala dan komai na tafiya dai dai yadda ya kamata Amina suna zaman su lafiya etada mijin ta haka Umma kasuwanci sai habaka yakeyi ga 'yan yaranta sai girma sukeyi kuma ar kullum suna waya da Simrahn su sai godiyan Ubangiji.

7 Years later(Bayan shekara bakwai) wata hadaddiyar mace che da wani gaye wanda sajen shi ya zauna mishi luff luff suna tsaye ney ar bakin wani asibiti wanda ga dukkan alama ma sabo ney gefe daya na hango Amina da Faruk sai su Umma da kuma Mama yayinda gefe daya kuma wasu yara ney su hudu suna tsaitsaye sun cakare abinsu sunyi kyau abinsu wuri ney ya tara taron jama'a na bude asibitin da Khalil ya bude ma his one and only wife Dr Simrah Abubakar ansha shagali ba kadan ba dan wata kwarya kwaryan walima suka had'a.

"Mommy Mommy kinga yaya Ayrah tana duka na"

"Kai baba nikam bazaku taru ku kashe ni ba cikin mutanan ma sai kun bada ni ga chan su tee kuje kuyi wasa dasu mana" tee dake gefe taji anyi kiran ta ney ta ruga kama hannun su sukayi su Ukun sun bar bash ar gefe yana zaune dai bai cika karamniya ba sosai Simrah taji dad'in wannan waliman abin mamaki wai hadda Samir da Salma ga yaran su biyu Friyal da Abir dan duk mata ney wai taro fa yayi taro kowa sai taya Simrah da Khalil murna akeyi abinda dai sai wanda ya gani hakan nan suka tashi taro kaff din su suka dunguma sai gidan Umma da ta sake zama dattijuwa amma dake hutu ya ratsata shar abinta ga kuma Omar da Salima an girma an fara zama 'yan mata.

Ar wannan shekaran abubuwa sun faru kama da auran Fadeela da Khamis Aisha da Ahmad kai hatta da su Ramlat ma duk sunyi auran su sannan Jumaima eta ta gyara tsakanin Samir da Simrah har ta nema yafiyan shi duk dama tun wancan lokacin tai ta bashi hakuri kuma komai ya wuce kaman ba'ayi ba sai san barka Salma nada yara mata biyu Friyal da Abir sai Simrah nada biyu daya ya rasu Ayrah da Baba wanda yaci sunan mahaifin Simrah dayar kuma Ayrah kuma taci sunan Mama Amina nada biyu Tee Fatima kenan suke kiran ta Tee dai Bashir bash yaran kam tabarkallah Masha Allah sai dai muce Allah yayi albarka ya bar kowa da masoyin shi.


_Ahamdulillah nan muka kawo k'arshe novel din nan wurin da bamuyi dai dai ba Allah ya yafe mana yasa kuma mu gyara mu amfana da abinda ke cikin shi godiya dubu ga dukkan dawa nake tare fan's kun nuna soyayya kun nuna kauna Allah ubangiji ya bar mu tare daku sai mu had'u ar book na gaba mai suna Shahyderh ga dandane nan ar kasa Miss Ayush and Sa'adah loves you all_

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 21, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now