*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
*{Page 33....34}*
Ar hankali Simrah ta d'aga labulen d'akin tana sake wata sabuwar sallaman Faruk da Umma neh kawai suka amsa cike da matukar mamaki take kallon Faruk dan sam hankalinta bai kai wurin Samir ba dan ya sauko kasa cike da mamaki tai ma Umma magana.
"Umma mey ya faru?
"Babu abinda ya faru Simrah sai alkhairi wadanan mutanan da kikaga sunzo,sunzo mana da abin dake tattare da mahaifin ki dan haka ki wuce ki zauna zakiji komai" shigowa cikin d'akin da tayi neh ya sanya ta ganin Samir wanda idon kanshi yake ar sauke yana danna waya wani irin bugawa kirjin ta yayi tare da karanto duk addu'an dayazo bakin ta, taji d'adin ganin su matuka sai dai ganin damuwa tattare dashi da kuma rashin walwala da ko en kula daya nuna mata ya sake d'aga hankalin ta jiki sanyaye ta esa wurin Umma ta zauna ga kirjinta na wani irin lugude na fitina addu'an ta Allah dai yasa kar su fad'a ma Umman ta komai akan abinda ya faru dan bataso Umma ta sani, amma maganan da Umma tayi kan mahaifinta yasa ta mamaki tayaya akai suka san shi kenan dama bincike sukeje sukayi akanta ko mene maganan Umma neh ya dawo da eta d'aga duniyar tunanin.
"Ki gaida su mana Simrah" ar hankali ta gaida Faruk ta kuma gaida Samir wanda Faruk kadai ya ansa Samir ko ji yake kaman an kara zafafa mishi zuciyan shi saboda muryan ta muryan ta dayake bala'in so ar rayuwan shi yake matukar so ar duniya dayake jin d'adin ta fiye da duk was murya na 'ya mace ar duniya amma yau sai gashi yau sam baya kaunar jin wannan muryan baya sha'awan sake jin muryan ar rayuwan shi kin karb'an mata gaisuwan Umma na hankalce tun zuwan su Samir shi ba mutum neh mai san magana ba kuma alamun shi sun nuna wani neh shiyasa tayi tunanin daman haka halin shi yake wannan yasa bata damu da Simrah ta gaida shi bai d'ago ba balle har ya d'ago ya lura da wacce take gaida shi d'in ar hankali Umma ta fara yima Simrah bayanin dalilin zuwan su wanda tana cikin magana Samir yayi ma Faruk magana akan tunda dai sunzo kuma ya sauke nauyin dake kanshi ar tunanin shi kawai yana so ya koma gida,yana so su koma masaukin su tare da mik'ewa yayi ma Umman Simrah sallama ya fita wanda babu yadda Umma batayi ba kan su t'saya ko ruwa su sha amma sam Samir yaqi Faruk kadai neh ya t'saya yana bada hakuri akan abinda Samir d'in yayi da kuma yanayin shi sannan duk abinda ake ciki ta fad'a ma Simrah kuma insha Allah zuwa nan da k'wana biyu zai dawo dan jin abinda ake ciki godiya sosai Umma tayi mishi kaman zata duka hakan nan dai ya fita shima cike da jin d'adi da addu'an Umma ar t'saye ya tadda Samir rai bace yake kallon shi.
"Daman dan ka wulakanta ni yasa ka barni t'saye" ya t'sare Faruk da ido shikam murmushi yayi kafin yay magana.
"Ba haka bane na dan t'saya musu bayani neh"
"Wani bayani neh zaka sake musu bayan wanda akayi musu ai yaci sun gane komai"
"Na t'saya na gaida zuciyar ka da kullum kake kira lokacin kana gida" ya fad'a cike da tsokana.
"Kada ka sake fad'a min irin wannan Faruk na tsani maganan ta enhar kana so mucigaba da shiryawa"
"Afuwan" ya fad'a ya bud'e motan Samir ya shiga bacin rai na nan saman fuskan shi tunda suka shiga Samir kala bai che da Faruk ba har suka esa masaukin su wurin fridge ya nufa tare da daukan ruwa mai uban sanyi ya fara kwankwad'a sabida yadda zuciyan shi ke mishi zafi yana ar haka wayan shi ta hau ruri ganin Mommy che take kiran shi sauke goran yayi ya dauka wayan sallama tayi mishi yayinda shima ya amsa mata sallaman
"Ya kano Samir?
"Alhamdulillah Mommy zuwa gobe insha Allah nima zan dawo"
"Toh daman nima na kira neh na fad'a maka kada dad'e dan akwai magana mai mahimmancin da zamuyi"