*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
*Nayi mistake ar numbering kar kuga haka*
*{Page 29....30}*
Bayan sati biyu Samir neh ya fito yana zambad'a kamshi kamar ka sace shi ka gudu.
"Mommy ena Siyama"
"Na barta ar daki neh fita zakuyi?
"Eh Mommy wallahi na mata alk'awarin neh tun wancan lokacin dana dawo d'aga kano ban samu na cika mata ba saboda yadda nake jin jikina toh yau Alhamdulillah zamu fita"
"Oh kace shiyasa naganta cikin murna da farin ciki auta da son yawo"
"A'a Mommy ni nayi mata alk'awarin fa ta shirya neh? Zatayi magana kenan sai ga Siyama ta fito anci kwalliya kaman wata babba Mommy kanta sai data murmusa ganin dressing da Siyama tayi.
"Yayana nayi kyau" ar hankali ya d'aga mata hannu.
"Kinyi kyau sosai kanwata" d'adi taji tayi wurin Mommy
"Mommy kinji Yaya yace nayi kyau"
"Sosai kuwa autar Mommy Allah ya kiyaye muku hanya"
"Amin Mommy"
"Toh mai za'a siyo min ni kuma?
"Mommy meh kike so?
"Duk abinda kika siyo ma Mommyn ki zata karb'a"
"Shikenan Bye Mommy" hakan nan suka fita suna hira abinsu gwanin sha'awa sun kusa kai Mall d'in yaji wayan shi na k'ara bai d'aga ba har sai daya parking motan suna fitowa Khasim shima ya fito.
"A'a mutumina kace kaima ka shigo?
"Eh wallahi Siyama na kawo" suna maganan wayat ta sake shigowa har zae share sai yaga Alhaji Jibril neh sun dau lokaci suna waya kafin ya furta gashi nan zuwa yanzun nan yana kashe wayan ya juya wurin Khasim.
"Dan Allah ka shiga da Siyama kiran gaggawa ya sameni Alhaji neh ke nemana akwai wasu abubuwa da suka taso zanje na same shi"
"Toh shikenan"Khasim ya fad'a yaja hannun Siyama sukayi ciki yayinda ya tada motan shi kuma dan zuwa samun shi.
*******************************
Salma che sanye da hijabin ta har kasa yayinda shigan tayi Mami kanta sae da tayi mamaki.
"Salma ena zuwa haka da wannan hijabin?kallon Mami tayi da mamaki.
"Mami ko bai min kyau bane?
"Ya miki matukar kyau tamkar ma ache kullum shi zaki saka en zaki fita"
"Mami wani lokacin zafi yakeda kuma bazanji d'adin driving ba kinga yau har nikab ma zan saka saboda kar na kuma had'uwa da mutumin ranar dana baki labari" kallon mamaki Mami ta bita dashi.
"Wani mutumi kuma? Dafe goshin ta tayi tana tunawa ashe Aisha ta fad'a ma ba Mami ba.
"Wallahi Mami wani mutumi neh na had'u dashi yaketa bibiyata shiyasa duk sanda zan fita t'soro yake kamani ban sani ba ko turo shi akeyi kar ar sace ni ba'asan yadda nayi ba"
"Eh kinada gaskiya amma shi baki tab'a ganin shi ba?
"Ban tab'a ganin shi ba Mami gashi nayi laifi har marin shi nayi dan shiga gabana yayi saura kadan muyi accident da sai dai wata maganan ba wannan ba"