Part 11

7 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 21....22}*

2:40am wani irin zufa neh take yanko mishi yana ta juye juye kai kana ganin shi kasan yana cikin wani hali kuma da gani mafarki yakeyi da wani irin zab'ura ya tashi da addu'a ar bakin shi.

"Inalillahi wa'inna illaihir rajiun" ya fadeta yafi ar kirga mamakin neh kaf ya gama cika shi wannan mafarkin daya keyi ya dad'e yana yin shi ya dau shekaru yanayi sam abin bai mishi dadi ba tagumi ya had'a yana mai tuna abubuwan daya gani ar cikin mafarkin wanda tabbas abinda yake gani yana mishi nuni da amanar da aka bashi yana cigaba da nazarin mafarkin, tabbas an bashi wata amana wanda sakacin shi yasa ya kasa cika wannan alk'awarin,

Kaman an zab'ure shi ya mik'e tare da nufan wardrobe d'in shi wani hadaddan safe ya dauko tare da sanya pin din safe d'in ya bud'e duk wani abu mai amfani nashi ar ciki yake sawa kamin ya dauko wani handkerchief ya wanda take hasken abunda ke ciki ya bayyana zuba ma abin ido yayi tare da gold d'in dayake ciki sunayen mutane biyu neh ar ciki wanda aka rubuta da arrabi t'sura mishi ido yayi tabbas abubuwan sun kut'su mishi ar lokacin daya kamata ache ya  sauke wannan amanar da aka bashi, tabbas wannan ranar ba zai tab'a manta shi ba wacce tazo mishi da bak'in ciki da tausayi mai da su ciki dukka yayi kafin ya maida safe d'in alwala ya shiga yayo tare da fara gabatar da raka'a biyu wanda ya dau t'sawon lokaci yana addu'a akan Allah ya bashi ikon sauke wannan amanar da aka abubuwan kuma duk sun bud'e mishi dan sauke wannan nauyin ganin bacci yaki zuwa masa ya dauka alqur'ani ya hau karatu wanda bai t'saya ba sai dayaji kiran Sallah asubahi kafin ya mik'e dan tafiya massalaci

8am duk wani shiri daya kamata ache yayi toh fa ya gama shi ganin wayan shi na k'ara ya dauka ya zata Simrah che amma sai yaga Khasim che.

"Man wai yaya neh k'arfe 8 fa girjin ka zai tashi"

"Yes Khasim duk abinda ya kamata nayi yanzu breakfast kawai zanyi zaka eya zuwa sai mu tafi"

"Wai yanzu kai Samir haka zakayi tafiyan ko rakiya bazaka nema ba, ka tab'a ganin yadda mutum yaje neman aure mutum shi kadai"

"Khasim surutun ka neh yasa ban gayya che ba amma akwai wani abokina ar chan Faruk zai zo ya daukeni ya kaini masaukina edan na huta nayi wurin rabin raina"

"Ai shikenan amma dan Allah kar kaje soyayya ta rik'e ka kak'i dawowa fa kasan bikin Haidar fa"

"Kar ka damu k'wana biyu kawai zanyi insha Allah"

"Toh shikenan gani nan zuwa"

Jan jakan sa ya shiga yi kamin ya fita parlo Mommy's d'in shi ya tadda  hira ya zauna suka fara yana karyawa har ya kammala sannan ya duba time ganin zae makara yasa shi mik'ewa.

"Mommy's ni zan tafi ku min addu'a" tuni kuwa suka fara kwararo mishi addu'an Mommy ta bada wani hadaddan zobe na zinari ta mik'a mishi.

"Mommy wannan zoben fa?

"Na 'ya tace ka fad'a mata ga nawa t'saraban kafin tazo gaishe shi neh"

"Wow Mommy nagode mun gode sosai Allah ubangiji ya kara arziki da lafiya" Amin suka amsa small mom najan hancin shi har bakin gate suka raka shi yayi dai dai da zuwan Khasim kuwa suna d'aga ma juna hannu suka tafi abokin sai t'siya yake mishi har suka eso airport wanda Khasim bai tafi ba sai daya ga tashin jirgin su sannan ya bar airport d'in.

               *****************

Khasim dawowan shi kenan d'aga airport ya shiga gidan mai don k'ara mai ar motan shi hangen wata bakar mota yayi ar gefen shi tana sauke glass d'in tayi tana fada akan yasa mata da sauri kafin ta kira Aisha ar waya kan su had'u ar gida idon shi bai sauka akan kowa ba sai akan Salma wacce take waya tabbas idon shi edan ba gizo yake mishi kuma ba karya tunanin shi ke bashi ba to tabbas Simrah che wacce Samir ya nuna mishi eta wacce kuma zai tafi wurin ta, b'angaran ta kuwa jin kaman ana kallon ta yasata juyawa ido hudu sukayi da Khasim wanda ta dauke kai tana tsuki.

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now