Part 12

6 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 23....24}*

Da wani irin gudu Amina ta fad'a d'akin Simrah duk sallaman datayi sam hankalin Simrah baya wurin dan ta gama zurfi cikin tunani ga kuma wayanta ar gaban ta data kashe ta.

"Ke Simrah lafiya nayi sallama baki amsawa" ar zab'ure ta kalle ta dan tabbas tayi nisa cikin tunanin ta.

"Simrah ena fa ga chan su Samir wallahi ar waje duk da bansan shi ba amma d'aga yanayin su yanayin shigan su tabbas nasan sune bayan ma haka sun tambayeni Simrah suke nema dan haka kuwa kinga kedin che"

"Inalillahi wa'inna illaihir rajiun Amina na shiga uku Amina na mutu ni Simrah na cuci kaina da kaina Amina yanzu ya zanyi"

"Wai Simrah har yaushe zaki zauna kina wahalar da zuciyan ki neh iyye wallahi enhar baki fita kin same shi yau zan tona komai Simrah zanje na sanar da Umma abinda yake faruwa sannan shima zan sa shi ya shigo ciki ya gane ke wacece gwara tun wuri kije ki karyata kanki edan zai cigaba da sonki shikenan edan kuma ba zae cigaba Allah ya baki wanda yafi shi"

"Amina ai abinda bana so kenan amma ayau zanje na karyata kaina da kaina zanje nayi abinda kika che Amina"

Cikin rashin k'arfin jikin ta mik'e tare da daukan hijabi wanda dan k'walin kanta ya zame saboda tsantsin gashin nata.

"A'a Simrah ya zaki saka hijabi kuma?

"Toh Amina ya zanyi bayan yanzu komai ya riga daya wuce"

"Wallahi sai yanzu naji kin burgeni dan enhar ba gaskiya Kika fad'a mishi ba bazaki tab'a samun sauki ba"

"Shikenan Amina muje na raka ki" suna fita Umma na fitowa.

"A'a Amina dama baki tafi ba tun dazu sai bakin sun eso"

"Ai wallahi Mama ena fita sai gasu ar waje sun eso shiyasa nazo ma sanar da eta taje ta same su"

Tsohon d'akin baban su na soro daya sha gyara an saka turare sai kamshi yakeyi anan zasu sa shi ya zauna.

Samir na waje Faruk na mota yake magana.

"Man gaskiya nifa nagaji ko 'yar gwal che ai yakamata ache ta fito yanzu koh nifa d'aga ganin gidan nan ma ban yarda wai yarinyar dake cikin gidan nan kake so ba"har ya gama Samir bai che mishi ci kanka ba dan shima abin ya k'wance mishi kuma ya daure miki kai matuka ga haushi yata kiran ta ta kashe waya mai take nufi da wannan kashe wayan yana jin shi yaki tanka shi sai ga Amina ta fito

"Ke kuma madam tun tuni kin ajiye mu ko kin manta neh" dan murmushi tayi tana magana

"Wallahi ba haka bane dan Allah kuyi hakuri wacce naje kira neh na tadda tana uzuri"

"Amma wacce take gidan Simrah neh sunan ta?

"Eh Simrah neh amma bansan ko etace kuke nema ba" nan Amina zataji ta tafi neh ko a'a amma bazata eya tafiya ta bar k'awarta ba koba komai zata zame garkuwa ar wani wurin  nan suka sake jin shiru kuma.

"Ya kuma har yanzu bata fito ba gaskiya wannan Simrah tacika nawa da jan aji"

"Yi hakuri barin sake dubata" ar bak'in kofa ta tadda ta d'akin da za'a sauke shi.

"Ha'a Simrah mai yasa baki fito ba wai?

"Amina gaskiya bazan eya fitowa ba sai dai ki musu eso" shikenan Amina ta amsa  tayi waje eta kuwa Simrah zuciyan ta na bugu na t'sanani dan tabbas tasan yau kam nata ya kare take ta shiga d'akin daba wani haske sosai yakeda shi ba sai dai kana eya ganin abinda ke ciki.

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now