*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
*{Page 51....52}*
Tun d'aga bakin kofan parlon zaka rika jin wani mugun kanshi na tashi mai daukar hankali yayinda Amina da Umma suke kitchen suna ta faman girke girke Simrah na daki tana kimt'sawa parlo ta fito yadda taga wayan ta na kara dake kan kujera dubawa tayi taga bakuwan number tabbas wannan number Khalil neh dan dashi ya kirata sukayi maganan kan zai zo zama tayi kan d'aya d'aga cikin kujerun.
"Assalam alaika" ta fad'a da sanyayan muryarta b'angaran Khalil kuwa ajiyan zuciya ya sauke.
"Amincin Allah su tabbata ar gareki kyakyawata" dan murmushi tayi kaman yana gabanta.
"Amin kaima ya tabbata ar gareki babban mutum"
"Ena fatan dai baki manta ba koh?
" Ban manta ba dan tun dazu na sanar da Umma zaka zo ai kaga kuwa ban manta da kai din ba"
" Lallai kuwa baki manta din ba ashe dai ana ji dani" dan shafa fuskan ta kawai tayi tana narke fuska kaman yana kallon ta.
"Ai wani abun neh ake mantawa wani kuwa ba'a manta shi"
"Hakane toh mey kike so na taho miki dashi?
" A'a bana bukatan komai zuwan ka kadai ma ya wadatar"
" Ena godiya da wannan daddadar magana taki yayi min dad'i sosai"
" Ka cancanci magana mai dad'i nima kuma nagode sai kazo koh"
" Toh sai nazo" ar hakan nan suka kashe waya tayi kitchen tana sauke ajiyan zuciya alamun ya mata dad'i.
" Kai Umma irin wannan abinci wallahi ni miyau na har ya tsinke"
" Hehee lallai Simrah toh nan gani nan bari dan kuwa badan ke akayi ba" fad'ar Amina hararan wasa ta jefa ma Amina.
" Kin ma esa wannan uban abinci kamshi ya gama ciki min ciki kice bazan ci ba toh wallahi sai naci" Umma na jin su tak bata che dasu ba yayinda zuciyan ta kuwa ta cika da farin ciki en har tunanin da takeyi gaskiya neh lallai Simrah tayi dace da miji na gari dan Khalil ko wace mace zatayi fatan samu ar rayuwan ta hakan nan dai sukayita aiki har suka kammala suka fito parlo.
" Toh Simrah aje wanka koh, Amina kema ki shiga bayi na kiyi kunga time din daya fad'a ya kusa"
" Ai shine Umma tun dazu Simrah taje ta kimt'sa tayi banza dani"
" Amina fita sha'anin ta nasan mey zan mata" kallo daya Umma ta jefa mata tare da wucewa dak'in ta tayi wanka cikin mintuna kalilan ta gama shiri ta fito fes abinta sosai Amina ke kare mata kallo yadda tayi masifar kyau cikin wani tsadadden lace wanda Umma ta bada kudi sukaje kasuwa sukayi siyayya dinkin ya matukar karb'an jikin ta turare take fesawa wanda Amina keta faman gwada kyan da tayi.
"Wannan surutun ni da kika cika ni dashi ena ma wanda zuciya ta ke so" zata sake maganan Amina ta kat'sar da eta.
" Allah kina sake maganan shi zan tafi naje na fadawa Umma" bata fuska Simrah tayi.
" Shikenan bazanyi maganan abinda yake raina ba ni kenan"
" Na dai fada miki wlhy zan fadawa Umma ta dau mataki akai" shiru tayi tare da saka sarka da madubi tana kallon kanta ar madubi eta kanta tasan yau tayi kyau ba kadan ba suna haka Umma ta same su.