*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Bismillahir Rahmanir Rahim, wannan labarin ya faru dagaske sai dai dan abinda aka rage da aka kara, bamu yadda wata wani wata ta canza mana shi ba*
_Page 5&6_
Koda Salma tashiga dakin ta, kasa komai tayi har sai da ta dauke wayar ta, ta duba taga ko guy nata yayi post dik da tasan wannan bashine dai-dai time din da yake ba amma zuciyar ta takasa jure jiran wannan time din har dai ta duba taga b komai qarshe pictures din da yayi post jiya batayi save ba sune tayi taci gaba da kallon kyakyawar fuskar sa mai matuqar kyau da tsari, itace bata ajiye waya ba har sai da taji alamar motsi tamkar ana hawo step din dakin ta ay da hanzari tasake waya tayi toilet tarufo qofa da sauri.
Ay kuwa mamyn ta ce daddy yaturo yaga ko tashiga wankan, ganin bata dakin kuma ga alama na motsin ruwa a ban daki shine yabawa mamy tabbacin lallai tashiga wankan..
*********
Kano- Simra ce ke gyaran daki sai faman fifita take saboda zafin da ake tayi a gari, tinaninsa kawai ne faal aranta, akan abinda tamasa jiya ita kanta tasan bata kyauta ba, tsoronta daya shine kar dai allah yasa b fushi yayi ba, bazai qara kulata ba, "ay kuwa dana shiga ukku ta fadi hakan a fili cikin sa6uwar baki wanda sai cikin kunne mama da take qoqarin shigowa dakin.
"shiga uku kuma? "meya faru na fadar shiga uku simrah?
Cikin dabarbarcewa simra tace "wllh mama wancan abun da kikasaya dazu ne, na dauka zan qarabar dashi na share gurin yatashi faduwa saura qiris yarage yafashe.
"tabbbbb lallai kuwa da kinwa kanki asara dan yana cikin kayan dana fara miki tariya na daki, mama tafada cikin 'yar tsokana kafin ta dauke abinda zata dauka tafita dan tasan halin kayan ta yanzu zata fara mata maganar ita bazatayi aure ba.
ashe kuwa maganar ba qaraman tsayawa simra tayi arai ba, duk da batajin dadi idan aka kawo mata maganar aure saboda shaquwar dake tsakaninta da maman ta, batason abinda zai rabasu amma yau maganar ba qaramin dakar zuciyar ta tayi ba, saboda tinawa da tayi da kyakyawan ta.
tana tsakiya da tinani taji wayar ta tafara ringing wacce ke gefen gado a ajiye, cikin mutuwar jiki da faduwar gaba, ta isa tare da dubawa,
batayi save No shi ba amma ganin da tamata jiya tariga da tasan tasace, sai da wayar ke neman daukewa sannnan ta dauka, shiru dukkan su sukayi b wanda yayi magana.
Samir ne yayi qarfin halin cewa "morning sweetheart."
sai da ta rintse ido saboda yanda taji voice dinsa dagaji basai anfada ba yanzunnan yatashi daga bacci.
Kamar yasan abinda take tunani jin kawai tayi yace "yanzunnan natashi ko idona bana iya budewa sosai na lalaboki saboda jiya nakasa bacci pictures dinki sune nayi ta kallo har bacci ya sace ni, "sweetheart wllh ina matuqar SON KI, da yawa dan allah ko yaya ne kada ki qara kasheman waya, zuciyana tinjiya sai bugaman take tsorona daya allah dai yasa banfadi wata magana data 6ata ranki, dan a yanzu 6acin ranki shine abunda nafi tsana a duniya wllh fiye da komai, kinji?
sulalewa tayi a hankali tafadi qasa a gefen gado tare da dafe kanta qwallah ce take shirin zubowa a idon ta, sai dai allah ya taimaketa ta6oyeta tin kafin tafito, cikin qarfin hali tace.
"wllh baby bakaman komai ba kuma bazaka ta6a man ba, kalamanka nayiwa qwaqwalwana girma ne, sonka na neman girman zuciya na, ina sonka fiye da tunanin ka, kawai ina tausayin rayuwa ta ne, shin yazanyi idan narasaka, wllh baby da mutuwa zanyi, takai qarshin maganar ta tamkar zatayi kuka.