Part 33

10 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{63..... 64}*

Hira sosai Amina da Simrah sukeyi Salima da Omar kuwa sai wasan su sukeyi har Mama ta sake kawo musu abincin rana wanda anan su Amina sukaci bayan ta deba ma mijin ta nashi duk da Amina na gidan haka baqi suka rika dan shigowa gefi gefi dake ma ba wani mutane sosai cikin unguwan zuwan Faruk gidan yasan ya Khalil fitowa gaba dayan su ney suka had'u suna hira sai tsokanan su Khalil sukeyi suma suna musu iskanci hakan nan suka yini har k'arfe 5 sannan suka tafi bata wani bata lokaci ba ta kakkabe gidan tare da saka mishi turaren kamshi etama taje tayi wanka ta callah kwaliyarta abinta tayi kyau Masha Allah tana jiran ogan nata ya dawo eta kam ta gaji da zaman nan wallahi sai taje jin gaba daya jikin ta ya mata nauyi rasa mey zatayi yasa ta fara karatun alqur'ani dan ar haka Khalil ya dawo da abinci ya tadda ta tana wannan karatun.

"Masha Allah hafizata Allah ya bada lada"

"Amin boo yasu Mama?

"Mama na gaida diyar ta"

"Toh ena ansawa muje kayi wanka koh"

"Eh muje" hannun ta ya rike sukayi dak'in shi tsaf ta had'a mishi ruwan wankan kafin ta fito tana kallon shi yadda ya tub'e sai karamin towel din dake daure ar kugun shi ta juyar da kai.

"Nagama had'awa"

"Toh Allah ya miki albarka"Amin ta amsa shi zata fita yayi caraf ya cafke ta tare da janta sai toilet rufe kofan yayi ya tub'e mata kayan ta tsaf wani irin kunya taji ya saukar mata ya zatayi hakan nan ta biye shi sukayi wanka tare da fitowa kimtsa kansu sukayi kamin suje parlo cin abinci magana ney fal ar cikin ranta amma ta fiso sai ya nutsu tukun bayan sun kammala cin abincin ta wanke kwanukan sannan suka zauna kallo yana k'wance saman cinyanta yayinda take shafa kanshi wani wani lumshe idanu.

"Boo"

" Na'am bounty"

"Tambayan ka nakeson yi daman"

"Kunnen Khalil na bud'e yana jiran tambayan matar shi"

"Batun school din ney"mikewa yayi tare da jan hancin ta.

"Yes bounty school sun baki admission ar oxford university kuma nan da kwana biyar zamu tafi saboda fara abinda ya kamata dan nima akwai aikin da zan fara before na barshi sai nan da 2weeks amma lokacin zae wuce min"

"Naji dad'i boo Allah ya saka maka da alkhairi har na fara missing din Umma tun yanzu"

"Kar ki damu gobe zamuje gidan Mama sai muje gidan Umma kinga zaki dan ji dad'i ache kwana biyu kin ganta kafin mu tafi"

"Sosai nagode mijina"

"Yauwa matar Khalil tashi muje daki kiji wata magana" sai da gabanta ya fad'i dan tasan kwanan zancan sai dai tana fatan Allah yasa bashi bane dan wallahi jiya ma daurewa kawai tayi hakan nan ta bishi sukayi dak'in bayan sun kashe komai da komai na parlon.

Akan fadedden kirjin shi take tana shakar kamshin dake fita ar jikin shi yayinda yake wasa da gashin kanta yana shinshinan shi.

"Baby wani country kika fi son zuwa ar rayuwan ki? Tambayan ar bazata yazo mata sai ta shiga tunanin lokacin da suke zuwa Paris etada Jiddarh d'aga school wani sanyayyan murmushi ta saki tuna moments din su ar wannan kasar.

"Honey ena bala'in son Paris ar rayuwana kasan sanda nake school naita karb'an kudi wurin Daddy toh nida Jiddarh muke tafiya d'aga school ko Dubai"

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now