Part 20

7 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 39....40}*

Simrah da Umma gyara na musamman sukai ma gidan dan cikin gidan zasu shiga dashi kasancewar d'akin da suke ajiye su duk wanda ya wuce ta jikin wurin zey eya jin abinda ake fad'a tabarma suka fara shimfidawa kafin su bita da dadduma mai uban laushi tana kammalawa taji ana sallama.

"Laa Umma kinga gashi chan ma muryan shi neh"

"Toh jeki shigo dashi" koda ta fita shine t'saye ar jikin mota murmushi ya sakar mata tare da fad'in

"Simrah 'yan mata" cikin jin kunya ta sadda kanta kasa

"Ena yini"

"Lafiya lau Simrah ya Umman take?

"Etama lafiya lau"

"Toh Masha Allah gani nazo"

"Ai yau tace ka wuce ciki" tana gaba yana baya har suka shiga yaga basu t'saya yadda suka saba t'sayuwa na yay mata magana.

"Simrah yanaga mun yi gaba?

"Ai Umma cewa tayi ka wuce ciki saboda maganan tana bukatan sirri kuma kaga d'akin duk wanda ya wuce ta wurin zai rik'a jin magana koma ba wannan ba ai yanzu ka zama tamkar dan gida bismillah" cike da jin d'adi yace ya gode hakan nan ya karasa shiga duk da gidan ba kayatacce bane amma irin gyaran da sukai ma gidan sai ya zamo abin sha'awa an tsaftace komai wanda ar hankali ya zauna kan dadduma sai ko ga Umma ta fito.

"Faruk an eso?

"Eh wallahi Umma ena yini"

"Lafiya lau Alhamdulillah"

"Masha Allah,Simrah kawo mishi ruwa koh" mik'ewa Simrah tayi tare da zuwa ta dauko kayan sanyin da akai mishi sake komawa tayi tare da dauko warmern da suka zuba pepper chicken d'in da sukayi ta ajiye gaban shi cike da mamaki yake kallon Umma.

"Umma dukka wannan nawa neh?

"Naka neh dukka edan ma kana jin kunyan ka eya tafiya dashi dan domin ka akayi shi"

"Nagode Umma nagode sosai Allah ya saka sa alkhairi"

"Bakomai Faruk ai duk abinda nai muku kai da abokin ka wallahi ban biyaku ba nagode muku ubangiji yayi albarka kuma"

"Amin Umma yauwa na karb'o kudin fa" cikin farin ciki Umma tayi magana.

"Haba?

"Wallahi Umma yanzu haka suna cikin account d'ina dan bai dace na shigo da kudin cikin gidan nan ba sai en kinada account ki bani sai ayi transfer cikin naki"

"Eh Faruk enada shi amma mey zai hana ar barshi naka ai nawa da naka duk daya neh" jinjina kan shi yayi.

"Eh Umma hakane amma kinsan kudi yadda suke kuma ba wai dan suna account d'ina zan tab'a ba a'a sai dai yanada kyau su zamana cikin naki tunda hakkin ki neh koba komai kun sauke min nauyi endai nai muku" cike da gamsuwa Umma da d'aga mishi kai.

"Toh Simrah bashi account din sai ya saka koh"

"Babu gaskiya babu eta cikin kaina sai dai akwai ar wayana"

"Toh dauko sai ki bashi" bud'e wayan tayi wanda ta bashi account number ya saka cikin wayan shi.

"Umma insha Allah edan naje gida zan turo dan yanzu nazo neh kan ar t'sara ya za'ayi da kudin"

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now