*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Bismillahir Rahmanir Rahim, wannan labarin ya faru dagaske sai dai dan abinda aka rage da aka kara, bamu yadda wata wani wata ta canza mana shi ba*
_Page 7&8_
Koda su Salma suka koma gida, daddy yayi mata fada tamkar zai doke ta abinda bata ta6a gani a gurinsa ba, saboda son da yake mata kokadan bayason ganin wani ya 6ata mata bare ma shi da kansa yayi mata abinda zai 6ata ranta.
Amma sai yau gashi akan kawai wani banza wanda baima san kansa ba yake qoqarin shiga tsakanin ta da daddyn ta, jin tayi a duniyar nan ta tsane wannan mutumin duk da bata gansa ba, amma kokadan bata qaunar sa, a ranta kuma batajin abinda daddyn ta ke qoqarin yi zaiyu saboda ita har yanzu bataga ajinta ba idan har aka cire Samir, ranta ya sosu matuqa shiya sa ma lokacin da daddyn ta yagama fadan sa, ko haquri kasa bashi tayi, illah miqewa da tayi ta haye sama zuwa dakin ta zuciyar ta na mai cigaba da mata zafi sosai..
*2 Weeks later*
Soyayya tayi nisa sosai tsakanin Samir da simra, jin suke idan har basu kasance a tare na har abada ba zasu iya mutuwa, musamman ma samir yafi zurfafa son a ransa, so ne yake nunuwa simra tamkar ba wata mace a duniya idan ba ita ba, idanusa sungama rufewa gaba daya, ta yanda ko yayane yake takatsantsan da abinda duk zai ta6a ranta, baya qaunar ko dan yatsan ta tace yana ciyo ji yake tamkar yazo gare ta, kamar yanda tafaru kwana biyu da suka wuce.
Koda y kirata yaji muryan ta a qasa sosai cikin tsananin tashin hankali yake tambayar ta meke damun ta,?
a wannan rana sai da simra ta gwammace da bata sanar dashi ba, domin kuwa tinda tace masa kanta ne kawai take jin yane mata ciyo wayyo allah gaba daya rikice mata yayi tamkar zaimata kuka, roqon ta yake tamkar wacce zata bashi gafara akan ta taimaka masa ta cece rayuwar sa tasha magani kuma taje amata allura.
Cikin jin zafi ciyon kai simra tace "wllh baby bazan iya ba, dana tashi hajijiya ke dibana kuma ni daman gaskiya bana son allura.
"haba sweetheart ay badan ke zakiyi ba danni zakiyi, saboda lafiyar ki tamkar jarice a jikina, ina son lapiyr ki banason abinda zai ta6aman ke, dan allah ki taimaka man kicece rayuwata kibari amiki allura nan wllh ba zafi, kisa aranki kawai ina kusa dake ake tsira miki bazakiji zafi ba, sweetheart dan allah kiman wannan taimako..
"baby bazan iya ba, idan akaman allura mutuwa zanyi simra tafada muryar ta namai rawa.
Hakan da samir yaji yaqara daga hankalin sa, "oh my god sweetheart dan allah kada kiyi kuka, shi kenan a daina maganar allura yanzu kinsha magani?
" ehhh nasha, simra tabashi amsa cikin dauriya.
"Alhamdulillah insha allah zai daina, sosai ya dinga jiro addu'a tamkar wani limamin masallacin juma'ah yana mai qoqon barar sa akan allah yabawa sweetheart dinsa lpy, a ranar gaba daya samir da simra ba wanda yasamu natsuwa dan ko cikakkin 2mnt ba'ayi ya ta6o ta, shi kadai yasan yanda yakeji game da ita yake fada mata..
Simrah ranar tasha kuka sosai tausayin kanta kawai take amma tafi tausayin samir saboda yanda yakamu da sonta son abinda ba azahiri haka yake ba, dan tabbas da da asalin pictures dinta ya santa ita tasan bazai ta6a ko kallon ta ba, INAMA NICE SALMA, simrah tafada tare da fashewa da wani erin kuka mai ciyo.
Da gaske suke jin son junan su so bana wasa ba, tayi qoqari matuqa na hana son samir yakama zuciyar ta har haka amma takasa, bazata iya ba kodan saboda erin son da take gani tsantsa acikin zantikan sa, ta yarda dashi ta yarda da kalamansa matuqa, ta tabbatar wa zuciyar ta qarya sam bata cikin tsarinsa da gaske ya keyin komi ye.