*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
_Page 19&20_
Washe gari.
Simrah kamar yadda ta saba tashi hakan nan ta tashi sai dai ta tabbatar ta gama wa Umma duk aikin da zatayi sannan taje tayo wanka ta zauna domin karyawan su dan kannan ta kam sun karya har sun wuce islamiyya ma etane dai da Umma suka zauna tare suka karya sannan tayi d'aki kiran Samir amma bai dauka ba sai tayi tunanin ko bai tashi bacci bane.
Haddadiyar motan shi etace tayi parking k'ofar gidan su Simrah dan bai mance kwatan can da Amina tayi mishi ba yana nan t'saye kuwa sai ga yaro yazo wucewa.
"Dan samari ji mana" yaron neh ya t'saya tare da zuwa wurin shi.
"Dan Allah shiga gidan nan kace ana sallama da Simrah" toh ya amsa shi kafin yayi cikin gidan da sallaman shi kuwa Simrah na waje Umma na d'aki ta amsa sallaman.
"Wai ana sallama da Simrah"
"Kaje kace bata nan" fitowan Umma kenan taji abinda ta fad'a.
"Kai yaro kace tana zuwa" toh ya amsa ma Umma kafin ya tafi ya kai sakon dari biyu Khalil ya bashi tare da mishi godiya ya tafi.
"Haba Umma banfa san waye ba kuma kika che ena zuwa"
"Sai ki fita kiga waye ai" tana fad'in haka tayi d'aki kafin Simrah ta sake mata wani magana rai bace ta zari hijabi tare da yin waje ganin shi wurin ba karamin mamaki abin ya bata ba kuma tasan ba kowa yayi mata haka ba sai Amina dole bazata tab'a eya t'sayawa ba tare da sallama ba shiyasa tana sallama taja bakin ta tayi tsit.
"Simrah ya kike?
"Lafiya lau" ta fad'a tana tunzura baki gaba dan wani iri takeji bata saba t'sayuwa da namiji haka ba.
"Simrah dan Allah kiyi hakuri kar kiga kaman ena takura miki wallahi zuciyata neh shiyasa na kasa hakuri sai dana sake biyo ki"
"Toh ya kamata kuwa kaba zuciyan ka hakuri dan ar gaskiya ni yanzu karatu nake son yi ba aure ba"
"Endai wannan neh mai sauki neh aure baya tab'a hana karatu enhar kuma ni kikeji wallahi bazan tab'a tauye miki hakkin ki nason yin karatu ba"
"A'a dan Allah banason ka wahalar da kanka shiyasa na fad'a maka gaskiya da dai ka hakura din zai fi ni enaso na shiga gida"
"Ok ba damuwa nima kyakyawar fuskan ki kawai nazo gani sannan banajin zan dawo saboda akwai bikin wani abokina da za'ayi ar kaduna sannan tachan zan wuce Abuja sai dai na dawo tukun zaki sake ganina"
"Allah ya bada sa'a ya kiyaye" tace kamin ta wuce ba tare da jiran ansan shi ba koba komai tabbas yaji d'adin addu'an ta gare shi ledan daya taho mata dashi ya sake samun yaro kan ar shigan mata dashi gida tuni kuwa ya tada mota ya bar wurin.
Suna zaune etada Umma yaron ya shigo da ledan.
"Wai gashi abama Simrah enji wani mutumi ar waje"
"Kai koma masa da ledan shi"
"Zo yaro kaji" karb'an ledan Umma tayi tare da dubawa ganin kayan ciye ciye neh yasata bama yaron sannan ya tafi ta koma ga Simrah.
"Ke Simrah waye wannan d'in ar ena kika san shi?
"Umma nima bansan waye shi ba kawai dai abinda na sani da mukaje kasuwa yayita bin mu ar baya sukayi magana da Amina kuma na tabbatar da etace tai min wannan abun wallahi zamu had'u da eta shima kaman maye nace ya hakura yaki ana dole neh wai"