Part 5

8 0 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/FJR2jsNrkFxG6MDDtqmK7X

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

_Page 9&10_

Samir zaune yake ar office abin duniya ya ishe shi rashin jin Simrah da bai yi ba sannan kuma ya dauka alk'awari ma kanshi ba zai kirata ba har sai endai ta kira shi saboda baya son takura mata yana nan zaune har abokin shi yazo kan shi bai sani ba sam bai ma san da wani ar kanshi ba.

"Samir ya dai meyake faruwa" ya fad'a sadda yake dan tab'a table d'in gaban shi.

"Oops Khamis yaushe ka shigo da banji shigowan ka ba?

"Kayi nisa cikin tunani ta ena zaka san na shigo wai miye yake damunka kayi zurfi haka?

"Man kai dai bari kawai mu fita dan dama na fara jin yunwa"

"Muje ena zaka lauye da maganar danayi kenan wallahi Samir ba ruwana ka daina aje damuwan ma ranka"

"Shii man karka wani damu muje"

Dagasken gaske Samir sai da yasan abinda yayi ya mantar da Khamis maganan mota suka shiga tare da bata wuta suna tafe abinsu suna hira.

                  ********************

"Wai Allah ni Simrah mai na aikata haka kar dai ache yayi fushi dani neh wallahi da bazan eya jurewa ba" tana k'wance neh kan 'yar katifar ta take wannan maganar ma kanta kaman jin karan wayanta yasata zabura ta zatan shine yake kiran ta amma sai Amina ta gani still dai ta dan ji d'adi ganin k'awarta che mai kiran ta.

"Assalam alaiki" Amina ta fad'a d'aga b'angaranta.

"Amin alaiki salam Amina ena ya kike?

"Lafiya lau Simrah, yasu Mama da Rano kuma?

"Mama lafiyan su kalau, Rano kuma dazu muka dawo"

"Iyye k'awa sannun ku da dawowa kiyima Mama sannu kafin na shigo"

"Insha Allah zan mata ki gaida Umma dan Allah"

"Zataji Amina" kitt suka kashe wayan tana sake kallon wayarta.

"Ya Allah kasa ya kirani Allah yasa ba zuciya yayi min ba" tana wannan maganan wayarta ya sake ruri da sauri ta dauka ganin customers d'in su neh yasata dauka wayan mintuna sukayi kafin ta fita wurin Umman su.

"An samu fitowa kenan uwata?

"Wallahi Umma ana son kunun aya neh wai zasu zo anjima su karb'a"

"Alhamdulillah ai haka muke son customers suna zuwan mana maza hanzarta ki dauko kayan had'awan" ganin mahaifiyar ta na farin ciki yasata farin ciki etama duk da zuciyan ta na cike da tunane tunanen shi haka ta tafi dauko kayan jiki duk babu k'wari duk Umma na lure da eta har ta kammala had'awan suka daura su t'saf tana gama gyaran wurin ana kiran magriba dalilin dayasata zuwa d'akin ta dan yin sallah kenan.

"Wai wannan yarinyar yau menene yake damunta haka yanzu danayi tambaya za'a che min babu komai amma bari naje najiyo" Umma ke maganan ta mik'e kenan masu kunun aya sukazo karb'a hakan neh yasata zuwa dauko musu ta bar tafiya wurin Simrah.

Oganniyar taku hankali ya tashi taci alwashin enhar akayi esha'i bai kira ba toh fa eta zata kira shi da kanta don ta gaji tana bukatar jin muryan shi ko zuciyarta zata samu salama ya zatayi da ranta neh kam amma bari ayi sallahn tana wannan tunanin Umma ta shigo.

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now