Part 31

12 1 1
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 59....60}*

Ar hankali wasu tsala tsalan motoci masu masifar kyau da tsa'da sukayi parking cikin hall wanda ke cike da abokan amare da angwaye kai da gani kasan masu shi sunji kudi shigowa suka cigaba dayi har suka kare nasu Samir na gaba yayinda nasu Khalil yake baya cikin motan Samir ya tsare Salma da ido yayinda ta lumshe idanun ta.

"Wai baby tun da muka shigo motan nan kaketa kallona"

"Laifi ney dan na kalla matata toh ko na daina ney?

"A'a karka daina"

"Kinyi masifan kyau kinfi ko yaushe kyau Mrs Samir"

"Kaima haka angon Salma kayi wani fitinannan kyau fiye da yadda kake tunani ko yaushe ena godiya ga Allah daya bani kai matsayin miji"

"Nida ke dukkan godiya zamuyi ga Allah dan duk munyi dace mun samu cikar burin mu" suna haka sukaje ana knocking glass din dan kasa dashi yayi yayi arba da Khamis.

"Ya dai?

" Kun bar mutane cikin suna jira fa kusa zuwa gida ai sae ku cinye junan ku amma dai ku fito"wani dogon tsaki Samir yaja yana kallon Khamis tare da d'aga shi ya katse musu hiran su mai dad'i.

Cikin motan su Khalil kuwa ar hankali yake magana yayinda fuskarta gefe yana duban ta.

" Yau ma rowan fuskan za'amin ney? Dan murmushi tayi.

"Bangane rowan fuska ba"

"Toh baga shi yau ma boyeta akeyi ba"

"Toh kayi hakuri"

"Ba kya laifi ai bounty" d'ago idanun ta tayi suka yi ido biyu kafin ta maida shi kasa tana murmushi shima wani malalacin murmushin ya saki.

"Alhamdulillah Alhamdulillah har abada bazan daina godiya ga Allah daya bani ke ba"

"Ni yakata nayi wannan addu'an da Allah ya bani kai namiji tamkar daya tamkar dubu"

"Idan ku hakane kuma abinda kike fad'a gaskiya neh lallai kuwa zan miki abinda baki tunani ba zan baki farin ciki,zan baki kulawa fiye da yadda zan kula da kaina"

"Tabbas na yadda na kalaman ka dan na gani tun kafin na shiga gidan ka sai dai fatana Allah ya bamu ikon hakuri da juna" wayan shi ya ciro ya shiga daukan ta hoto bayan ya amsa addu'an ta da amin wanda sukayi masifan kyau dan karkatowa yayi suna kusa da juna ya shiga daukan su dan da halin makalkaleta zae yi amma har yanzu dai bata zama mallakin shi ba tukun ar haka din ma ba karamin kyau suka buga ba abinsu suna kallan junan su ya dauke su wanda yayi masifan kyau kuma take ya canza ya maida shi wallpaper nashi.

"Yanzun nan har ka canza wallpaper"

"Bakiga yadda hoton yayi kyau bane"

"Eh yayi kyau sosai ma sae ka turamin koh"

"A'a gaskiya bazan tura ba sai kin biya"

"Ba matsala zan biya bashi fada kudin shi"

"A'a ba yanzu zan fad'a ba sai gobe en an kai ki gidana zan fad'a farashin"

" Toh nidai yanzu zaka fad'a en ba haka ba na hakura"

"Ai baki esa ba tunda kika taya sai kin siya"

" Toh ana siyan abu dole ney daman"

" Bani na taya ba ke kika fara tayawa dan haka dole ney ki siya"

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now