Part 27

8 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 53....54}*

Sanyayyan numfashi ta sauke tana jin wani farin ciki daya gama cikata na ganin muradin ta kuma abin kaunar ta ba karamin Missing din su tayi tana wannan tunanin taji karar wangale gate din da akayi gama parking motan yayi ta rugu ar guje tare da fad'a wa kan Mommy.

"I missed you so much Mommy" murmushi Mommy tayi tana shafa bayan ta

"Your Mommy miss you too" kiss tayi ma Mommy ar forehead dinta kafin ta kai kasa ta rungume Siyama.

"My Choco baby i missed you"

"Missed you too fav sis ena tsarabana?

" Kai Choco baby bazaki barni na huta ba zaki sha mamakin irin tsaraban danayi miki harda su Choco naki" kara rungume ta Siyama tayi tana jin dad'i.

" Mommy ena bro yake?

"Yayan ku na office bai dawo ba, bakuyi waya bane?

" Uhm Mommy kinsan halin shi sae kaita kiran shi bai dauka ba"

" Toh shikenan ai yana sane da yau zaki dawo din muje ciki" gaba dayan su ciki suka shiga Altine sai washe baki takeyi ganin Fadeela tana mata sannu da zuwa cikin jin dad'i Fadeela ke kallon ta.

" Baba Altine duk kin canza girma ya sake kamaki kin canza"

" Ai kema kin canza Fadeela ta kamar ba kece wacce na goya ar bayana na ba" duk sai suka sa dariya.

" Mommy barina shiga nayi wanka sai na fito"

" Toh kafin ka sauko an gama had'a abinci dan nasanki ba wasa da ciki"

" Kai Mommy" tafiya tayi zuwa dak'in ta Siyama na bayan ta sai magana takeyi wai ta kara kyau ta kara fari.

" Allah kin raina ni yarinyar nan dauka na kikeyi sa'anki koh"

" Kai Fav" ba tare da tace komai ba tayi toilet Siyama taja wayan nata b'angaran Mommy kuwa tana kasa ana had'a ma Fadeela abinci yayinda cikin sanyin sa ya shigo da sallama ya zauna wanda kallo daya zaka mishi kasan ya gaji.

"Samir yadai ya office?

" Wallahi Mommy ba dad'i ko kadan"

" Toh ya za'ayi Allah dai ya baku juriya da sa'a ya kuma kara taimakawa"

" Amin Mommy yarinyar nan ta eso kuwa?

"Eh ta eso taje wanka ai tayi ta kiran ka baka dauka ba"

"Mommy wallahi ena aiki neh time din"

"Toh yayi kyau yanzu ka tashi kaje kayi wanka sai ku sauko muci abinci" haka kuwa ya mike yayi dak'in shi dan yin wanka.

Bayan kaman awa biyu hira sukeyi kaman sun shekara dubu basuga juna ba wanda duk yawancin hiran eta da Mommy neh sukeyi hankalin shi na akan waya duba sakon da Salma ta turo mishi kasancewan yana kusa da Mommy ya kasa dauka ya tura mata msg tayi mishi reply wanda yasa shi sakin murmushin duk abinda yakeyi akan idon Fadeela kamin tayi gyaran murya dagowa yayi yana had'e rai ta kauda kai.

"Uhm Yaya namijin duniya soyayya tayi dad'i amma gyaran murya kawai nayi ya had'e rai" duk eta kadai take wannan maganan.

"Yaya ena Aunty na? Murmushin fuskan shi che ta sake bayyana.

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now