Part 29

10 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*{Page 55....56}*

Tana k'wance neh kan fadaden gadon ta waya na makale ar kunne ta wanda ga dukkan alamu wayan na mata dadi dan da gwarzon ta take buga soyayya kwana biyun nan ya gama rikita ta wanda kuma abinda ya fad'a na ta fara son shi gaskiya neh eta kanta tana mamakin har yaushe wannan abun yayi tasiri ar zuciyan ta suna tsaka da wayan ney Amina ta shigo hannun ta dauke da Mug tana kurb'an tea gefen gadon ta zauna tana kallon Simrah wanda ta gaji dan tun tuni take zaryan zuwa dubata.

"Wai Simrah bazaki tashi kiyi breakfast bane tun dazu kuketa abu daya  sae ar wani che en kana waya bazaka eya cin abu ba ni gaskiya bazan eya wannan abin ba" duk mitan da takeyi Simrah naji haka ma Khalil naji murmushi kawai yayi.

"Mutumiyan ta eso kenan?

" Gata nan ai sae mita take ma ko ena ruwan ta daci na ko rashin shi oho"

" A'a fa bounty da gaskiyan ta wallahi ya kamata kije kici abinci gaskiya ni kaina ba zan so ki zauna da yunwan ba"

" Nifa bana jin yunwan neh"

" A'a ki tashi dai kici kuma Amina ma bazata ji dad'in hakan ba zatayi tunanin ni na rike ki bana so nayi laifi edan kuka gama zuwa anjima zan kira ki duk da ma zanje bayan magrib muyi sallama zanje Abuja"

" Abuja kuma wurin wa?

"Wurin abokina dan bikin mu yazo daya nida shine Friday za'a daura nashi Saturday za'a daura namu akwai shirye shiryen da zamuyi na had'a dinner da muke so ayi ena so musa date daya"

"Date daya kuma mey sa bazaka bari ayi nashi ba sae ayi namu"

"Abinda banaso kenan ai dan kullum gauro yake kirana gwara nayi kafin nan har kuma nayi magana dashi akan hadawa din ma"

"Toh wai habib qalbi kana wani zancan zuwa Abuja waye zai je ma tukun"

"Ke mana da duk wanda ya dace"

" A'a gaskiya ni baza'ayi haka dani ba Umma ma bazata yarda ba ka manta hidiman wannan kidnapping din da akeyi ko so kake na rasa ka?

"A'a bazaki rasa ni ba babu wanda zai dauke ki dan ar jirgi zaku tafi" idanun ta ta zaro

"Ar jirgi kuma?

" Eh nan fa enaso edan akayi komai daya dace ko lokacin da Umma ta gama duk wani tsare tsaren da take so ayi zakuje Abuja da kawayen ki haka da wasu manya dukkan zan biya muku sai ku tafi kinga yanzu kaman an saka amarya lallae washe gari nasan zakuyi walima toh sai mu tafi Abuja en mukaje akwai gidana da zaku sauka tunda kinga Friday za'ayi daurin auren kuma dole na hallarci daurin auren shi shiyasa aka sanya dinner ar lokacin kinga ranar edan anyi dinner sai mu juyo  Saturday da safe tunda  k'arfe biyu neh daurin auran" tamkar yana gabanta haka ta rufe ido wai yau etace zata taka jirgi ba'a ma t'saya nan ba har Abuja garin shugaban kasa zata je garin da Villa take😂 jin ta takeyi kaman wata sabon mutum dan ko ar mafarki bata tab'a tunanin haka ba gaskiya ta taki sa'a tunda ta samu Khalil matsayin miji jin tayi shiru yasa shi sake magana.

"Toh kuma ki had'a takkadun ki dan ena son fara neman miki makaranta dan bazamu dade nan kano ba zamu tafi ko kin fasa neh"

" A'a wallahi ni bance nafasa ba"

"Na tabo miki yadda yake miki ciwo kenan hadda ansawa da k'arfi zan kamaki" maganan tashi sai kawai ta bata kunya.

"Nidai sae kazo Allah kawo min kai lafiya"

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now