*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
*{Page 41....42}*
Mami che t'saye k'ofar d'akin Salma tun tuni take bugawa amma bataji mot'sin kowa ba takaici ya isheta yasata magana.
"Salma tun dazu kinaji ena knocking bazaki bud'e ma ranki zae baci fa wallahi" sai da Mami tayi wannan maganan sannan taji mot'sin ta etama Salma tasowa tayi tare da bud'e kofan tana t'saye ar wurin Mami na kallon ta.
"Mey ke damunki haka Salma?
"Wallahi Mami banida lafiya tun jiya"
"Shine baki fad'a ma kowa ba sey kin kashe kanki ar banza ar wofi kan abinda bai kai ya kawo ba ni ki sameni ar parlo" shiga d'akin Salma tayi tare da zaman kan gado kanta na kasa kana ganin ta kasan damuwa tayi mata yawa ta kasa daukan abinda iyayanta suka zabar mata dan eta kam ko kadan bata san wannan hadin nasu mik'ewa tayi dan shiga toilet sai wayan ta ya hau kara ganin Aisha neh yasata dauka.
"Hello Salma kina jina? Jin muryan Aisha haka yasata dan jin d'adi
"Aisha mey faru haka?
"Salma wallahi nagan shi naga Samir yanzun nan"
"What! Ar ena Aisha?
"Yanzu nan wani sabon asibiti nan kusada mu da ake bud'e wa yau yanzu haka yana d'aga cikin manyan bakin da aka gayyata ni kuma na raka Mommy kinsan kawarta neh mai asibitin ni kuma ena chan waya da Kamal kawai na juyo sai na ganshi yana kokarin shiga mota dan dukkan alamu ma bashi kadai bane dan mota biyu nagani"
"Inalillahi wa'inna illaihir rajiun yanzu Aisha kina nufin Samir d'ina kika gani?
"Wallahi Salma shi nagani edanu na sun kasa gane tabbacin shine na gani har sai da nabi bayan wani tare da tambayan shi kaman shine Samir d'in da ake magana koh yako che min eh shine kinga kuwa edan bashi bane tayaya zai che min shine edan bashi din ba ke Salma wallahi shine"
"Yanzu Aisha kina nufin kin ganshi neh ar banza ba tare da wani mot'sin t'sayar min dashi ba" cike da haushi Aisha tayi magana.
"Wai Salma mey sa wani zubin ana miki magana kaman baki fahimtan abinda ake fad'a miki tayaya zan t'sayar dashi cikin wannan mutanen ga uban mutanen da suke san ganin shi kuma ai ma fad'a miki mota zae shiga sadda ma ganshi ar tsaitsaye ma ya gaida mutanan wurin" ba tare da tayi ma Aisha magana ba ta tsinke wayan tare da fashewa da kuka.
"Inalillahi wa'inna illaihir rajiun yau naga samu naga rashi yaya zanyi da wannan abin gashi su Mami sun tasani gaba" mai aikin su che ta sake knocking tare da fad'in waye?
"Mami che tache tajiki shiru" kasa shiga wanka tayi yadda jikin ta yayj sanyi mik'ewa tayi tare da zuwa parlon ta zauna kusada Mami.
"Mami gani"
"Wai Salma menene haka ba nan muka gama magana dake ba kin karb'a umarnin da Daddyn ki ya baki amma har yanzu kin kasa yadda da kaddaran ki da kuma zabin iyayan ki na son abinda baki tab'a ganin shi ba kiyi hakuri Salma zaki so abinda bazaki same shi ba dan na tabbatar da zaki samu da tuni Allah ya kawo miki"
"Mami bazaki gane ba wallahi ko yanzu sanda Aisha tace min taganshi"
"Toh Salma data ganshi ta kawo miki shi neh ki nut'su Salma wallahi d'aga yau bazan sake miki maganan kibi umarnin mahaifin ki ba bazan sake miki magana akan yanayin ki na kin cin abinci da komai ba tunda dai ke baki jin magana" d'aga idonta tayi tana hawaye.