*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
*{Page 57....58}*
Washe gari ta kama ranar da zasuyi kamu da Sisters day amma oganiyar fur tace ta gaji sai kamu kadai suka bari zasuyi wani ubansu tsareren hall Samir ya kama musu wurin ya gaji da haduwa tunma ba'a gama tsara shi ba yayinda chan gidan kuwa an gama had'a ma Salma duk wani kaya da zata saka sai shiri suke bazawa b'angaran Samir kuwa suma shirin tafiya kamu sukeyi shida su Khamis da sauran 'yan uwan shi da suka zo sai su Jibril wata azzababiyar shadda black che wacce take ta baza kyalli yake sanye ar jikin shi ba karamin haduwa yayi ba bak'i ya hadu da fari jama'a wani irin kyau zae yi hilis😂 Salma ma wani material neh black mai rat'sin pink ar jikin shi dinkin ya samu damas ar jikin ta Mami sai yaba kyan diyar nata takeyi ar hakan nan motoci ya k'washe su sai wurin kamu.
Kusan tare motocin su ya eso wurin yayinda Khamis ke bayan Samir sai Aisha dake bayan Salma kafada da kafada suka shiga wurin tare da zama kan kujeran da aka tanadar musu sai blushing sukeyi masoya anga juna jama'a kunsan dai yadda ake kamu ba sae mun t'saya dogon jawabi ba☺️ ar take koh suka fara abinda ya kawo su har aka fara kirayen sallah magriba sannan suka bar wurin kowa ya koma gida dan huta gajiya.
*********************************
Ar yau take Friday wanda kuma ayau neh za'a daura auran Samir da Salma wanda kuma ayau neh su Simrah zasu diran ma garin shugaban kasa garin da Villa take enjita da fada fitowa tayi tare da tsayawa kallon kanta ar madubi tana mamaki Amina dake k'wance tana latsa wayan ta.
"Amina"
"Na'am amarya Simrah"
"Wallahi na fara jin tsoro duba fatan jikina fa kin fini fari amma ji yanda na wuce ki fari matan nan kayan ta yana sani haske gaskiya kinsan kuma kuma bana son haka"
"Wallahi kuwa Simrah fatan ki ya murje yayi kyau Masha Allah amaryan Khalil" ta fad'a cike da tsokana.
"Uhm nidai ba wannan ba ena su Kausar da Ramla?
"Suna wurin saloon kuma nasan ba dadewa zasuyi ba tunda sun san dai da wuri za'a tafi"
"Sarakan Yawo" shine kadai abinda ta fad'a kamin ta wuce wurin kayan ta wata dogon riga na atampa ta sanya mai golden wanda yana cikin kayan nagani ena so ta dauka ciki tare da dinkawa ya mata bala'in kyau dinkin kaman ba Simrah ba.
"Simrah kinga yadda kikayi kyau kuwa amaryan mu"
"Ai haka zakice tunda aka fara wannan hidiman ko mayafi na saka haka kike cewa nayi kyau nasan badan Allah kike fad'a ba"
"Toh dan wa nakeyi"
"Oho nidai bansani ba"
"Toh naji dai Simrah yanzu gyara ko dauka biyu ney nayi miki sai na tura ma mutumina"
"Ai shiyasa nace ba dan Allah kike cewa nayi kyau ba kuma bazaki dauka ba"
"Simrah bazaki gane ba wallahi ko maqiyin ki ba zae che bakiyi kyau ba"
" Nagode amma baza kimin wani hutu ba nikam"
" Naji mayya kici kanki"
" Oho naji dai bazan ci kaina ba kuma baza'a min na"
"Yarinya kenan anjima sae ki hana mu yi ai" suna wannan maganan sai gasu Ramla da Kausar.
"Amina ena jin fa ana magana ar waje"