*DAWA NAKE TARE*
*Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe**Written by*
*Miss Ayush**Ana tare writer's association*
*Wattpad@ayshartou*
*{65..... 66}*
Simrah da Khalil sun dira ar masaukin su dake
Shangri-la the shard, london ta zama tamkar wata 'yar kauye ar wurin duk da ta gaji amma hakan nan bai hanata bud'e ido tasha kallo ba Micheal da Jackson sune suka zo daukan su bata gama tsurewa ba sai data ga haduwan gidan da abubuwan dake cikin su daya d'aga cikin maka maka kujerun ta samu tare da zama Khalil da abokan shi suna magana ar waje har ya shigo dauke da abinci rufe kofan yayi tare da isowa wurin ta."Welcome to London bounty taso muje kiyi wanka sai kizo mu huta koh?" Ko musu bata mishi ba ta kwashi jikin yau babu gaddama ma na wanka hakan nan ta t'saya sukayi wankan su tare abinsu 'yan kana nan kaya suka sanya kafin su fito ciyar da junan su suka shiga yi kafin ya tayata suka tattare wurin sallah sukayi sai baccin da suka kwanta yi dan tana da bukatan shi sosai sukayi bacci abinsu dan har sai da suka fara jin kiran sallah magriba sannan Khalil ya tashe ta sallah sukayi ya fad'a mata ta shirya suje shagon coffee hakan nan tasa dogon riga abinta suka fita har suka esa anan suka ci abinci rana wani eatery dake gefen shagon coffee din sai da suka zaga gari sannan suka koma gida likis ar gajiye tana farin ciki da zuwa wannan kasar bayan sun kai da kanshi ya kira mata Umma da Amina suka sha hira kafin kuma su k'wanta.
Washe gari da wuri suka tashi dan ranar ney zata fara zuwa school Khalil da Michael su suka kaita school din bayan anyi abinda ya dace tsaf ta zauna tana sauraran lectures din duk da akasarin su ma wasu danna wayan su sukeyi tana zaune taji an mata sallama dago kanta tayi tana kallon mai sallaman ganin alaman musulma che yasata ansawa.
"Hey sunana Jumaima" baki Simrah ta saki ganin tana hausa dan kamanin ta bazai che ma ta eya hausa ba.
"Sunana Simrah" etama ta mik'a mata hannu suka gaisa.
"Dagani kina mamaki toh zan eya zama" kai kawai Simrah ta gyada mata.
"Kar kiyi mamaki Sunana Jumaima Mahmoud ni 'yar asalin Nigeria che mahaifina dan chan ney mahaifayata kuma 'yar Sudan che"
"Masha Allah sunana Simrah Abubakar"
"Masha Allah naga alaman sabuwa che ar school din friends? Ta tambaya tana mik'a mata hannu
"Yea friends" murmushi suka sakar ma junan su kafin su maida hankali wurin baturen dake lecture yana tattare kayan shi tare da fita dake biyu suke dashi yasa eta da Jumaima zama suna kara sanar da junan su ar lokacin da Simrah taji wai tanada wani cousin Samir ba karamin bugawa kirjin ta yayi ba sosai tasha jinin jikin ta dan duk yadda taji an ambaci Samir toh fa sai taji wannan faduwan gaba hakan nan dai ta daure suka shiga ta biyun suna fitowa kuwa anan suka tadda Khalil yana zaman jiran ta har wurin motan Jumaima ta raka ta ganin Khalil yasa ta tsananin mamaki.
"Laa daman matar ka che Yaya Khalil?
"Yes Jumaima kiche har kin kame min kafar mata?
"A'a ni rufa min asiri toh lallai ar bikin ku ban wani gane ta ba dan kasan dinner ba wani tsayawa nayi ba etama amaryan Ya Samir din ba lallai ma na ganeta ba yanzu"
"Ai yanzu babu zumunci ney Jumaima Allah dai yasa mu dace" Amin ta amsa suna gaisawa da junan su tayi wurin motan ta suma suka bar wurin yana tambayan ta ya school suna hira sama sama har suka koma gidan nasu.
Ena mutanan Paris gaba daya Samir da Salma sun zama masu yawo sunci kafan kare basu nan basu chan su leka nan su leka chan b'angare daya kuma suna zub'a soyayya abinsu kaman su hadiye junan su basuji basu gani.