Part 18

9 0 0
                                    

*DAWA NAKE TARE*

        *Story by*
*Sa'adatu Alkali D/Tsafe*

       *Written by*
      *Miss Ayush*

*Ana tare writer's association*

*Wattpad@ayshartou*

*Dan Allah duk mai bukatan book d'in nan d'aga farko yaje Wattpad please kar mutun ya min magana yaga na rabu dashi dukkan shi yana Wattpad masu tambayana ta private please*

*{Page 35....36}*

Dawowan Samir ya ma Siyama da Mommy d'adi shi karan kanshi Samir d'in yaji d'adi duk da ba yau ya sab'a tafiya ba amma ganin farin cikin da Mommy takeyi yasa shima yake farin cikin Siyama che ke ta mishi hira yana murmushi dan yarinyar ba karamin debe mishi kewa takeyi ba wani lokacin neh dai rigiman ta yafi k'arfin ta kuma yana saka mishi ciwon kai mai da hankalin shi yayi wurin cin abinci.

"Siyama ni ena nawa cake din da kika samo?

"Yaya ai nazata zaka dad'e shiyasa kuma wannan ba irin wancan bane kumama fa bashida yawa edan zanje school neh nake tafiya dashi"

"Wato sai ki kai ma friends d'inki kuka cinye tare da mantawa da Yaya koh?

"Toh Yaya kayi hakuri zan sake kiran Aunty Salma sae tayi maka"

"A'a no kinga ni bansaki ba dan koda tayi bazan ci ba"

"Mey sa Yaya?

"Kawai dai wancan ma dan kin mat'sa neh shiyasa naci" Mommy na kallon su bata che komai ba Siyama kuwa ta b'ata rai kaman ance ba'a cin abin hannun Mommy.

"Miye neh toh Baby na b'ata rai?

"Ba kai kace baka cin abinda Aunty Salam tayi ba" mamaki yakeyi shi kam wai wacece wannan Aunty Salma da Siyama ta damu da eta hakane da duk maganan da zatayi sae ta sako maganan ta kallon shi ya mayar kan Mommy.

"Mommy wai wannan wace Salma che Siyama ta damu da maganan ta haka? Ruwa baki Mommy ta karasa kaiwa kamin ta mishi magana.

"Kai yanzu Samir ko kunya bakaji ba dan Allah?

"Kunya kuma Mommy"

"Eh mana yaza ache 'ya d'aya tilo wurin Alhaji Jibril ache baka santa ba"

"Toh Mommy amma dai ai bana nan yarinyar ta tashi koh tunda dai ba nan nayi karatu ba kuma time d'in dana dawo etama ta tafi karatun shiyasa bansan ta ba"

"Ai shiyasa nake fad'a maka Samir bakada zumunci tunda gidan Alhaji Jibril d'in ma ba zuwa kakeyi ba toh tayaya koh zaka santa ai yanzu Samir kai kanka kasan abinda ya dace da kai ba sae an fad'a maka ba gidan Alhaji Jibril dai ko sau daya neh zakaje tunda ya zame maka tamkar mahaifi" girgiza kanshi yayi cike da gamsuwa

"Hakane Mommy wallahi nima edan ena son zuwa sai aiki kuma ya taso min"

"Ba wani nan haka kake fad'a kullum duk abinda kasan nada kyau ai ka sani dan yanzu ka wuce matakin da zance Samir kayi" shiru yayi yana kallon mahaifiyar tashi wanda ar kullum kokarin ta neh data nusar dashi abinda ya dace amma shi Allah yayi shi irin mutanan da basu san shiga mutane ko kadan.

"Kiyi hakuri Mommy insha Allah za'a gyara"

"Allah yasa"

"Mommy ni na tafi d'aki munyi fada da Yaya"

"Siyama yanzu zaki eya fada dani akan wacce kika sani daga baya? Kallon Mommy tayi tana k'ara kallon Samir d'in.

"Wallahi Yaya Aunty Salma tanada kirki harfa kyautan waya ta bani"

"Haba" ya fad'a da mamaki

"Eh mana na dauko maka ka gani?

"A'a kinga yanzu ena cin abinci edan na gama sai na gani koh" tafiya tayi ta barshi d'aga shi sai Mommy ajiye spoon d'in hannun shi yayi tare da kallon Mommyn nasu.

DAWA NAKE TAREWhere stories live. Discover now