Chapter 9

44 3 0
                                    

The chapter is dedicated to Malama Fatima matar mallan 😍

Baablami ta soma ba Nur labarin iyayen ta. Tace:"Nur baban ki dan Yola ne kuma sana'ar shi ita ce ƙera takalma da jikukkunan na fata." Ita kuma Mahaifiyar ki ba y'ar Nigeria bace y'ar Nijar garin Agadas. Baban ta shi ne Sarkin Agadas. Nur was shock da jin haka. Ta maimaita abin da Lami tace ''yar Sarkin agadas!!!

Lami tace:"Eh."
Nur a rud'e ta tambaya; To Miyasa Mammy ta dawo nan? Miyasa ba ta san zuwa chan? Lami tace:"Abban ki ya hadu da ita a chan Agadas da yaje siyo fatan raqumi dan nan Nigeria yana dan wuyar samu kuma ga tsada." Anan ne ya hadu da Mammy. Abban ki ya sha wahala kafin ya gano ta saboda ita yar sarki ce bayan ya gano ta ba wahala da azabar da bai sha ba a wurin sarki don yace ya na son Mammy. Ita ma ba irin wulakancin ta ba ta mai ba. Ya za ayi wani gaskantancen bawa ba ma dan kasar su yace ya na son ta. Duk cikin ya'yan shi ya fi ji da Mammy, dan duk cikin su ta fi su jajircewa, ga karfi tare da izza. Mutane yankin shakka ta suke yi,  bata yarda da rishin gaskiya ko rishin adalci. Babanta yan kiran ta da Najada, gimbiya najada saboda karfin ta tare da gaskiyar ta. A bayyane yake nuna banbanci tsakanin sauran yan'uwan ta da suke hassada a kan ta.

Abban ki bai hakura da Mammy ba duk da wahala da yasa ya zamo bawan gidan. A hankali ya ci nasarar a zuciyar Mammy dan ita kan ta ta san sai mai sonka da gaske zai iya jure azabtar wa da ta ke mai. A sirrance ta ke haduwa da shi ɗan ta san abin dan yan gidansu baza su taba yardar ba. Haka suka cigaba da haduwa a sirrance suna soyayyar su har  ta samu cikin ki.
Nur da sauri ta kalli Lami cikin mamaki. Lami tace:"Eh Nur Mammy ta samu cikin ki kafin su yi Aure." Hakan ya tsorartar da ita. Dan ba ta san ta fuskar da zata kalli mahaifiyar ta balle mahaifin ta. Ga kishiyoyin babarta. Dan al'ada masaurar ta ce ba a auran bare sai dai su auri familyn sarauta. Ɗan sarki sai iyar sarki haka ma iyar sarki sai ɗan sarki. Ta kawo wa Abban ki shawara su gudu su bar garin in ba haka ba za a kashe shi kuma martabar mahaifanta zai lallace. Abban ki bai yarda ba sbd shi ya fiso mahaifinta ya bashi auran ta. Mammy da kar ta dagatar da shi da ya ce zai fadi wa sarki gaskiya kuma ya mata alkawarin zai aure ta duk rantsi duk wuya tace mai za ta kashe kan ta dan bazata jurar gani an kashe shi kuma martabar mahaifanta ya ruguje. A sannan ne Abban ki ya yarda suka gudu cikin dare. Kuma ta bar wasika a dakin ta da ta ke bawa iyayen ta hakuri tare da neman yafiyar su da albarka su. Bayan ta rubuta musu abin da yafaru. Sun shigo Nigeria a ka daura musu aure agarin kawngawlon,  Dan Abban ki shima ya san family din su na Fulani ba sa  son bare. Bayan an daura musu aure su ka dawo Adamawa. Baban shi yayi fishi da haka amma bayan wani lokaci sai ya yarda da auran su wanda y'an gidan su da sauran dangi busu harda ba. Bayan wata shida Mammy ta haife ki. Haka ya kara tsananta abun duk ka yaushe suka yi aure da za ace har ta haihu. Sai Bayan ta haifeki sannan a ka kara daura musu aure batare da ko wa ya San ba sai mahaifinsa dan ba a daura aure da ciki.

Abban ki tin Farko ya ba wa mahaifin shi lbr to sai bai ce komai ba ya bar dangin shi suna ta yi wa Mammy isgili. Har attempt din kashe Mammy a kayi amma bai yu ba.  Shegeya suke kiran ki dan busu yar da ke yar Khalil ce ba. Abban ki ba arziki ya dawo nan Abuja dan shi Alhaji Sani Sa'idu shi ya taimaka wa Abban ki wurin kasuwancin shi. Har Allah ya yi wa abbanki cika wa. Nur da ke kuka ta kara fashe wa da kuka. Lami ta matsa kusa da ita ta rungume ta tana ba ta hakuri. Tace:"Bayan rasuwar mahaifin ki suka sa ta a gaba a kan gado kashi daya za a bata a kashi dayan ma ba cikakke ba kuma ke baki da gado." Anan Alhaji Sani Sa'idu ya samar wa Mammy lawyer ya shiga karan har a ka ba ku hakkin ku dan da farko Mammy ta so ta kayle su amma Alhaji Sani Sa'idu yace ba za a Kyle su ba hakkin ku ne. Bayan rabon gadon, Nur dukiyar da ki ke da ita yanzu Alhaji Sani Sa'idu ne ke juya miki ita. Shagon nan ko Naira ɗaya taki babu a ciki. Gumin Mammy ney sai da ga baya da ta bai wa hanif kudin shi. Nur kuka ta ke bata da tace wa dan abin ya daure mata kai. Babba Lami tace:"Duk duniyan nan a yanzu da gani sai ke sai Mammy suka san an same ki ba tare da aure ba sai shi kan shi Alhaji da lawyern dan sauran sun mutu da wannan sirrin." Nur kara fashe wa tayi da kuka bayan taji abi ya san komai nata. Kuma ba dangi iya balle uba. Baaba Lami ta cigaba da cewa; Ba kudi ba ba iza ba ba mulki ba ba saurauta ba ba inda Zainab zata nuna wa Mammy dan Mammy ta kere ta. Nur duk wa ina abubuwan bai ci ace kin yarda da alfarma shi ba. Da ɗan shi ba wai da shi ba.

NURUl QALBI 💖Where stories live. Discover now