chapter 29

35 5 0
                                    

Mammy ta sauko kasa ta same shi. Ya gaida ta. Ta amsa. Ta tambaye shi ya aiki. Yace aiki alhamdullilah.

Shekarar jiya sai ga Nur ta zo tace min ana zata kawna sai bayan daurin aure zata tafi.

Aman yace ehhh Mammy amma yanzu na zo ne in dauke ta.

Mammy tace eh hakan yayi kyau. Ko Ni nayi mamaki da ta ce min wai ana zata kawna. Muna gari daya, Gawra ta dinga zuwa ta na tafiya.

Aman yayi shiru dan ba mai son surutu bane.

Mammy tace kai Allah ya shirya mim ita. Aman a dinga hakuri da ita yarinya yace. Kuma dan Allah alfarma dai Kamar kullum itace ka kulla min da y'ata. Nasan bata ji amma Nur..

Yayi yar murmumishi yace to Mammy.

Suna zaune kusan 20 minute Nur bata sauko ba. Mammy ta kara sa a kira ta. Baabalami ta koma dakin ta iske Nur zaune kan gado tare da wayar ta tana danna ta.

Nur jiran ki yake fa. Ta karaso kusa da ita.

Nur tace babbalami miyasa zai zo dauka ta bayan sai anyi daurin aure.

Baablami tace saboda ya damu dake..

Nur tace ba wata damuwa da ya yi dani kawai tsabagin mugunta ce.

Babbalami tace Nur naga ji da korafe korafen ki tashi ki same shi a parlour. Tashi muje. Nur ta tashi daga ita sai Three quarter sai yar top.

Baablami tace a haka zaki fita??

Nur ta kalle ta sannan ta dawo tace zan shako bari in chanza kaya. Ran ta abce ta ida maganar.

Baabalami tace ba in da zaki maza ki chanza Kayan.

Ta Turo baki ta nufi wurin closet ta dauko doguwar rigarta ta bacci ta cire ta sa. Baablami tace Nur Kayan mutunci zaki sha.

Daga kasa Mammy ta kira Nur.

Nur ko magana bata yi wa baablami ba ta wuce kasa.

Tana sauko wa suka hada ido da shi tun daga sama har kasa ya kalle ta sannan ya kawda kai.

Ta karaso wurin su ta gaida shi ba tare da ta kalle in da yake ba.

Mammy tace Nur wai dan Allah yaushe zaki yi hankali. Nur fuskar a tamke.

Mammy tace wuce ki dauko hijabin ki ki bi mijin ki.

Nur tace Amma Mammy...

Mammy ta kawbe ta. Ban san jin komai.

Nur kamar zata yi kuka tace Mammy... Sannan ta juya ta koma sama ta fashe da Kuka bata fito ba har sai da Mammy ta shigo ta mata magana tare da bata hakuri. Sannan ta tashi ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta sa hijabi. Mammy ta tattara mata jikar ta tace muje.

Nur cikin kuka tace Mammy wai yau ke kike kora ta Mammy...

Mammy tace Gul shi Yanzu mijin ki ne yafi ni iko da ke. Ke din hakkin shi ne. Ki yi hakuri ki koma ba muna tare ba in yaso gobe tin da safe sai ki zo da daddare sai ki koma. Ki yi hakuri. Ki dai na kuka. Ki yi shiru. Ta goge mata hawayen ta. Tace haba Gul din Mammy nurin na. Ki yi shiru.

Nur ta hade abu tare da goge hawayen ta suka sauka kasa. Sukayi wa Mammy sallama suka tafi.

Baya ta buɗe zata shiga ya dakatar da ita yace ta koma Gaba. Ko sauran shi bata yi ba. Ta shiga ta rufe kofar. Ba yan da ya iya da ita ɗan ko shi kan shi ya san a cike take. Ya koma ya shiga Motar suka fara tafiya.

Nur ta hada kan ta da Giwa tun da suka fara tafiya take kuka har suka isa gida ta na kuka sai dai ya tsaci kallonta ta mirror.

Yayi parking din Mota ya fito. Nur taki fito wa. Yace malam ki fito zan rufe Mota ta. Ba dan ta so ba ta fito, ko jiran shi bata yi ba ta nufi kofa. Yace ta zo ta dau Kayan ta amma tayi banza ta Kayle shi. Dan bai son kowa ya san ni ya dau Kayan ya rufe Mota. Ya karaso Wurin kofar ya buɗe musu suka shiga. Ya rufe gidan.

NURUl QALBI 💖Where stories live. Discover now