Aman ya shiga side din Ummi Bayan sun gaisa. Ummi tace:"In ban da rishin Kunya wai yarinyar nan ta wani zo Simisimi wai tazo ta gaida Ni." To ce mata nayi ina son gaisuwar ta. Gaskiya Aman kana hakurin zama da wannan mara kunyar.
A hankali ya tambayi Ummi. "Ummi mi ya faru?''
Ummi tace:"Ta zo gaida Ni nace mata kar ta kara tako wa nan." In ban da munafinci shine ta wani marairaice ita kuma jannah Sarkin tausayawa har tana wani goyan bayan ta. Aman bai ce mata komai ba. Ummi ta kara da; "Muna zaman zaman mu a ka hada mu da alah kakai." Hajiya Turai ta shigo tana ce wa TOH Akwai alah kakai da ya wuce ke. Ay kece babbar alah kakai. Ta samu wuri ta zauna. Aman ya gaida ta. Ta saki murmumishi tare da cewa:"Dana ykk?" Ina amarya?Aman yace "Lfy qlau" sannan ya kara da Ummi Ni zan wuce.
Hajiya Turai tace:"Ina kuma zaka?? Kar kamin karya kace wurin aiki zaka dan na san hutu kake. Dan haka tsaya ka raka Ni wurin amarya. Ke kuma Zainab! Ta mike tare da kallon Ummu. "Ina mai gargadin ki dan na san halin ki kar ki sake ki takurawa wannan yarinyar." Ummi ko kallon ta bata yi Ba tin da ta gaishe ta ta kawda musu kai Har Hajiya Turai ta gama masifar ta tace ma Aman "Tashi mu tafi." Ya tashi ta tisa sa a gaba kamar karamin yaro suka nufi part din shi. Mukulli yasa ya bude kofar. Nur na kitchen taji karan bude kofa ta san Aman ne saboda kofar ba a iya bude ta ta waje sai dai da mukulli. Sai ba ta damu ta fita ba sai da taji murya alamun bashi ka dai bane sannan ta fito. Hajiya Turai ta rabka sallama tare da tambayar ina amarya take. Nur ta amsa sallamar tare da karaso wa Wurin su. Runtsina wa tayi ta gaida ta,Hajiya Turai ta dinga sa mata albarka. "Ka ga iyar arziki, kai Allah miki albarka yar arziki."
Nur tace mata ta zauna barin ta kawo mata drinks. Hajiya Turai tace:"Masha Allah Nurun ala Nur." Yanda ki ke sheki ina fatan ki sa wannan gidan ya dinga sheki haka. Murmumishi Nur tayi sannan ta nufi kitchen. Aman zai nufi dakin shi Hajiya Turai ta dakatar da shi. Ina zaka? Dawo nan ka zauna. Yace:"Hajiya..."
"Ni Hajiya Turai." Ta kame bakin ta sannan tace; ko yaushe danna ya fara min rishin da'a. Aman ya dawo ya zauna. Nur ta kawo mata drinks tare da snaks da suke kan tray ta aje su a kusa da kafar Hajiya turai. Hajiya Turai tace:"Kai amma na godai Allah shi albarka yar nan." Nur ta samu wuri itama ta zauna kusa 3 sitter da Hajiya turai ta zauna. Hajiya Turai bayan ta kai samosa baki dadi ya cika kunnen ta sai da taci samosa 2 nan take sannan ta kora da lemo tukuna tace; Kin san Ni???
A lkc nur ta dago kanta ta kalli Hajiya Turai tare da kark'ad'a mata kai. Hajiya Turai tace:"Ni sunan Binta Amma kowa yafi sani nan da Hajiya Turai. Ni ce babbar Yayyar sani wato sirikin ki." Nur batace mata komai ba.
Ta dau cup cake ta b'are papper ta kutsira sannan ta tambayi Nur wa ya mata samosa ɗan ta na so a ma ta. Nur tayi murmumishi tace:"Shikenan tun da kina so zan miki."Hajiya Turai ta dakata tace:"yanzu ke ki kayi wannan??? Nur ta kada mata kai. Tace:"Gaskiya kin iya samosa." Aman hankali shi na kan waya bama tasu yake ba. Tace gaskiya tayi daɗi za kin dinga min. Cupcakes din fa?
Bani nayi ba.
Wa yayi shi? Hajiya Turai ta tambaye tare da kara kutsirar cake din.
Nur tace:"Friend dita ta min shi." Hajiya Turai tace:"Shima yayi dadi." Kallon Aman tayi wanda hankalin shi bai kan su. Ta tambaye ta ya ta ke ji da bahaguman halin Aman? Nur ta kalli Aman sannan ta kalli Hajiya Turai tace:"A'a bai da wata matsala." A lokacin Aman ya daga kai ya kalle ta sannan ya kaw da kai tin kafin ma su hada ido da shi ko da Hajiya Turai.
Hajiya Turai tace:"Kar ki wani boye min na san halin d'a na gashi kuma aikin da yake sai suka kara burkitan min da shi." Wai tsaya kin ma san aikin da yake? Nur ta kada kai.
Hajiya Turai tace:"laa ilaha illallah!! Yanzu kai Aman baka fadi mata aikin da ka ke ba. Ita din ba matar ka bace ko ita bata da hakkin Sanin aikin ka. Magana nake ma amma sai wani latsa waya kake. Aman yace:"ki hakuri." Ya aje wayar.
YOU ARE READING
NURUl QALBI 💖
General Fictionlabarin rayuwar Nur wadda a ka aura mata mutumin da bata sani ba. ta auri mutumin daga shi har dangin shi basa San ta sai mahaifin mijin. like always in all marriages there's chanllages. Nur have to over come all the challenges. ku biyo ni domin ga...