chapter 22

33 5 0
                                    

...Tana cikin kukan nan Aman ya shigo ba ma ta san da shigowar sa. Ya nufi toilet ya gama abin da zai yi ya fito. Closet ya buɗe zai dau pyjmas din sa. Bayan ya dauka ya tuna da abin da yace wa Nur da safe. Daga wurin ya daka mata tsawa;
ke!

Nur na kawnce a kasa. Tayi banza ta Kayle shi. ya kara kiranta tayi shiru. Aman ya tsani ya kira mutum ya kayle shi. Ya matso kusa da ita yasa hannu ya daga ta zaune. Tare da matse mata hannu. Fuskar sa a daure yace:"ina aikin da na saki?

Nur tayi shiru.

"Ba magana nake miki ba."

Nur cikin shashekar kuka ta Tambaye shi wanne?

"Ohh, tambaya ta ki ke."
Ya Tada ta tsaye tare da jan ta da karfi wurin closet din. Suka hada ido da shi. Yace this is the last warning. Ki shirya Kayan nan yanzu. 10 minutes for that. Ya koma ya zauna kan sofa. Nur sabida kuka idanuwa ta har sun yi ja sun kumbura. Ta kalle shi tare da hade abu sannan ta fara fiddo kayan closet din. Gown din da Sabir ya bata ta jawo ta. Tayi kissing din ta tare da rungume ta ta cigaba da kuka. kafin ta zauna ta cigaba da fiddo kayan. Wayar shi a ka kira Ya tashi ya fita. Nur ta aje gown din a gefe ta cigaba da fiddo sauran Kayan. Polo shirt ta dauko, wasu zafafan hawaye suka kara sauko mata. Ta aje rigar kan cinyarta tana shafa sunan dake bisa rigar
"4 mi precious darling."

Ta tuno lkc da sabir ya dawo daga Paris ya kawo mata rigar as birthday gift din ta;
(close your eyes. Sabir yace. Nur ta kalle shi. Ya mata nuni da ta kulle. Nur ta rufe idon ta ya jawo hannu ta ya aje papper bag a hannun ta. Tare da rose flower sannan yace bude idon ki. Nur ta bude idon ta ta kalli hannuta. Murmumishi ta yi cikin murnar tace thank you.. sabir yace open the bag. Ta buɗe jikar. Ta dauko rigar daga cikin ledar ta. Ta bude ta. Ta dan daga rigar sama. Sabir yace happy birthday. Nur ta aje rigar tare da hugging din shi. Tace thank you, Thank you my lovely darling. Ta dago tayi kissing din shi a cheeks tare da peack. Yace i didn't attain the birthday party but now me and you will celebrate it together. Ya dauko Wani ƙaramin kawli. Ya bata ta bude. Cake ne ciki tare da stick a saman cake din mai dauke da happy birthday to you. Nur farin cikinta a bayyana yake sai blushing take. Stool ya dauko ya dora cake din bisa. Yace mata ta yanka cake din. Ta yanka ta dauko Small piece ta mika mai ya rike hannu ta ya sa mata cake din a bakin ta. Yace happy birthday once again. Tace thank you. Ta kara yanko cake din ta sa mai a baki. Tace ya sabir i don't know how to thank you. You made this day special to me. Unforgettable. Ya kamo fingers din ta ya sa a nashi. Yace not only today, every single Day hours minutes and seconds of our time Will be unforgettable. Yayi kissing din knuckles din ta yace i love you..)

Nur ta fashe da kuka sabida kuka har shesheka take. Tara da fadin i love you ya Sabir, you mean everything to me, i will continue doing that till end of my last breath. Tayi hugging din rigar tana ta maimaita i love you, i love you ya Sabir har ɓarci barawo ya dauke ta. Aman ya shigo dakin ya karasa Wurin closet din kawnce ya ganta ta rungume Polo shirt din. Da zai tada ta sai ya kayle. Ya koma kasa wurin dinning ba tea din sa ba arziki ya shiga kitchen ya tafasa Lipton ya sha sannan ya koma sama.

Washegari da safe bayan ya dawo daga masallaci ya iske Nur a kawnce. Toilet ya shiga ya dauko ruwa ya zuba mata a fuska. A firgice ta tashi. Idanu ta har sun kumbura saboda kuka.

Bacci ki ka zo yi ne??

Nur bata tanka mai ba. Kara durkutse wa tayi tare da rike cikin ta.

Yace:"Ba magana nake miki ba??

Nur cikin radadin ciwon ciki tace:"Cikin na fa ke ciwo."

Budar bakin Aman yace Ban damu ba ki tashi ke je ki tafasa min tea.

NURUl QALBI 💖Where stories live. Discover now