21

30 5 0
                                    

Bayan fito War su daga gidan Hajiya Turai. Nur wayar ta ta dauko tana Mai da messages na YouTube channel dinta  ko ta samu nitsuwa. Birki Aman yaci a Kofar gidan su Nur. Nur ta dago kanta domin ta ga inda suka tsaya. Tana ganin gidan su Wani dadi ta ji da bai mitsultuwa. Farin cikin ta a bayyane yake ko bata ce ba. Ta juya ta kalle sa ta rasa mi zata ce mai da sauri ta buɗe kofar motar ta fita ta fara knocking a gate din gidan.

Hanif ne ya buɗe kofar. Da sauri Nur ta rungume shi tana kukan farin ciki. Ta tambaye shi ina Mammy. Yace mata ta na ciki. Ba ma ta jira shi ba ta nufi ciki.

Aman da ba zai fito ba sai ya fito ya kulle motar. Hanif ya Bashi hannu suka gaisa sannan ya shigo ciki da shi.

Nur har ta hau sama ta sami Mammy a kan carpet din sallah. Cikin annashuwa tace:"Mammy!!!!! Ta ruga ta rungume ta. Ta fashe da kuka. Mammy ta rungume ta. Sun kai minti 5 a haka. Kafin Mammy tace wa Nur ta sake ta. Nur ta kiya ba abin da ta ke sai kuka. Har sai da ta gaji tun kunnan ta sake ta. Mammy ta tambaye ta ina mijin naki?

A lkc Nur ta tuna da Aman tace yana kasa. Mammy tace muje kasa. Nur tace:"Mammy i Miss you so much, i miss You I miss you." Ta kara rungume ta. Mammy tace kina lfy da fatan komai lfy?

Nur bataso yi wa Mammy karya ba amma ba yanda zata yi ko dan lfyr ta. Ta goge hawayen ta tace Mammy komai lfy qlau ban da wata matsala.

Mammy tace kin tabbata.

Nur ta amsa mata da "Eh Mammy."

Mammy ta mike tace muta fi kasa. Nur tace gani nan zuwa.

Mammy ta sauka kasa. Nur ta fito daga Dakin Mammy ta shiga dakin ta. Ta na bin dakin da kallo.
"Daman a kawai ranar da zata zo sai dai ta bi Dakin da kallo? Yanzu dakin ta shine dakin mijinta." Tana bin dakin da kallo tare da tuna moment din ta a dakin. Musamman ma in Inaya ta zo.

Mammy ta sauka kasa ta iske su Hanif da Aman. Aman ya durkusa ya Gaisheta ta amsa sannan ta zauna tare da tambaya shi ya yake da su Ummi.

Aman ya amsa da "Lfy Qlau."

Mammy tace dafatan babu wata matsala. Aman yace babu wata matsala.

Haka a ke so. Kuma Nagode da kulawar da ka ke ba wa y'ata.

Aman yace ba sai kin min godiya ba.

Mammy tace na sani amma sai ka din ga hakuri da ita, yarinya ce sai ka na nuna mata Abin da ya kamata da Abinda bai kamata ba. Aman yace insha Allah.

Baaba Lami ta samu Nur a daki Bayan ta kai wa Aman ruwa da fruit. Nur ta rungume ta. Baaba Lami ta tambaye ta ya take. Nur tace lfy qlau.

Baabalami ta tambaye ta in Akwai matsala ta fadi mata.

Nur ta fadi wa baabalami abin da Aman ke mata.  Ta dan tausaya mata amma bata nuna ba. Tace haka shi ne daidai Nur. Shi faɗin mijin ki ne yafi Mammy iko da ke dan haka dole ki bishi Dolle ki yi abinda yace. In Biki manta ba na taba fadi miki hanyar da zaka siye namiji. Dan haka kar ki damu duk abin da zai miki ki share shi. Su kuma su Ummi kar ki tanka musu balle ki shiga gonar su ay sai ka kula karya take haushi. Abinci ya zamo varieties. Nur zaki iya. Ki sa a ranki zaki iya ji da koma wa ye.

Nur tace baabalami ban san miyasa ba I'm so weak these days abu kadan sai in fara kuka. Sai ma ya dauke ni Sakara ya din ga min abin da ya ga dama.

Baabalami tayi dariya Sannan tace wa yace miki haka. Ke yanzu duk rishin jin ki duk yanda ki ke bata lokacin a banza a Baya wurin maza Yanzu sai ki kasa lankwasa wannan. Wanda shi ne mijin ki. Haba Nur, Nur din da na sani da kisisina.

Nur tace baabalami ba zaki gane ba wannan mutumin ba mutum ba ne kawta kawta baka gane mai. Ni wlh na gaji.

Baabalami tace haba mi a kayi da maza, ita fa rayuwar aure hakuri da jajircewa a ke so. Ba a taba gajiya kuma kukan nan da ke ke ce wa kan ki sakara ba sakarci ba ne, zuciyar maza bata da raunin amma hawayen mace da bai kai ya kawo ba ya na sa zuciyar su tayi rauni. Kuma shima kukan iri iri ne ba sai na ida fadi miki ba ke ma kin sani.

NURUl QALBI 💖Where stories live. Discover now