Bayan tafiyar shi, jannah ta roke ta da ta fadi mike damunta in ba abin da Ummi ta mata.
Nur tace No, when the going get tough, the tough get going.
Nur ban gane ba what do you mean???
Nur tayi ajiyar zuci dan ba ta san tayi wannan maganar ba, tace Jannah ki mance.
Jannah tace No Nur, ki fadi min. Okay nagane yanzu baki jin dadin Zama da yayana ko. Nur kiyi hakuri haka yake,
Nur tace Jannah it's fair a auran ma wanda baka so bayan kana da Wanda yake son ka, ke ma kina son shi. Ta kalli jannah tana jiran amsa.
Jannah tace Nur...
Da ba tasan amsar ta ba sai kuma tace, Eh to.. it's not Fair but Nur ba wai dan ina kanwar Aman ba Amma ina iya baki yaƙi nin ce wa Hakan zai zame miki Alkhairi dan ki bi umarnin mahaifiyar ki tare da shawara ko hukunci da ta yanke miki.Nur idon ta ya cika da hawaye, miyasa ba mai fahimtar zuciyar ta, kowa abu daya yake ce mata.
Jannah tace Nur ki yarda dani zaki ka ribar haka, sai wanda da yaga darasi a kan abu zai iya bai wa masoyan shi darasi.
Nur tace mi ki ke nufi??
Jannah ja numfashi tace dan Ni na ga fa'idar bin iyaye, na ga darasin haka. Da na bi maganar Ummi da Abi da rayuwa ta ba ta chanza ba, Nur when you're in love, you're blind you can't see what's good and bad for you. Nur Kafin in auri mahaifin Nawfal ba irin shawara da abi da Ummi Busu ban ba amma na rufe ido nace Ni sai shi, shi ka dai nake so. Dukkan su sun yarda da auran dan dai ba sa son b'acin rai na. Bayan muyi aure da sati biyu muka koma UK... Sai tayi shiru ta fara kuka.
Nur ganin hawayen jannah da idon ta da suka fayyace mata komai tace, jannah ba sai kin fadi min abin da ya faru ba.
Jannah ta girgiza ta tace, bayan munje uk da sati Daya ya haɗa party da friends din shi, a lkc na gano ce wa mashayi na aura. Na rufe kai na a dakin dan friends din shi kawta kawta basu da d'a, bayan two weeks wasu guda hudu cikin friends din shi tare da shi sukayi reaping di na...
Nur ta girgiza da jin haka.
Nur it was unlucky to me that both of them have affairs with me. Jannah ta fashe da kuka tana tuno quna da baƙin cikin abin da ya faru da Ita
Nur har cikin zuciyarta ta tausaya mata. Tayi embracing din ta tana bata hakuri, Bayan 3 minute jannah ta tashi daga jikin Nur tace after i found ina da ciki, na fadi mai amma budar bakin sa yace wannan bana shi bane ko da ma nashi ney to shi bai shirya zama mahaifi ba haka ya sa kafa ya bar Ni a estate din da dukkan su yan iska ney irin su, sai maman Jenifer ita ce ke taimako na, da taimakon ta na haifi Nawfal duk lkc Ummi da Abi Busu sani ba dan ban san fuskar da zan Kalle su ba. Sauki na shine ina aiki a can, haka na lura da Nawfal sai last few months na dawo nan nigeria na fadi musu duka abin da ya faru abi ya matukar fusata musamman ma yayana. Ko da a ka kira shi, da ya zo ko darajar Iyaye na bai gani ba yace shi bai bukatar mu ya riga ya biya bukatar shi dani dan shi Auran ma nauyi ney a ka dora mai. Abi ya sa shi ya sake ni, nan muka rabu.
Nur ta tausayawa mata matuka.
Jannah tace Ko da ba a yi blood test ba Nawfal dan shine saboda Nawfal yana da rami a cikin zuciyar sa haka shima Yasir.Nur Yasir ta tuna da jin sunan Yasir sai ta kori tunanin ta a kan ya za ayi Yasir ma ya zamo baban Nawfal.
Jannah tace mafarin ke nan Yasir ya zama abin da ya zama ɗan Mahaifiyar sa bata raye sannan baban shi ya dau son duniya ya dora a kan shi ɗan duk lkc da yake cikin damuwa ko baccin rai sai ciwon shi ya tashi. Maganar da nake baban ya yi disowning din shi tare da yin na dama sangartashi. Ta dalilin ciwon Nawfal na dawo gida dan banda kuɗin da za a mai aiki, yanzu An mai aiki amma har yanzu ciwon na dawo mai.
Nawfal bai son baban shi ba bai san waye shi ba, sauki na har yanzu bai taba Tambayata ina baban shi ba kuma na san Dolle watarana zai Tambaya musamman yanzu da ya fara zuwa school. Nur Ɗan Allah kar ki yi kuskuran da na aikata. Ki yi hakuri, Kuma in har zaki ki yaye dokokin yayana to zaki zauna lfy. Shi din mutumin kirki ne amma baza ka gane haka ba sai ka zauna dashi.
Nur ta goge hawayen ta tace Nagode Jannah da tunatar dani, kuma zan cigaba da hakuri. Suka yi hugging din junansu suna kuka kowa da inda yake mai ciwo.
Bayan Aman ya dawo gida ya sami Abi a parlour bayan ya gaishe shi. Yace Abi daman ina so in ma wata magana.
Abi yace fadi ina jin ka.
Sai da ya tauna maganar kafin yace Abi ina so ne in auri Tasnim..
Abi yayi mamakin jin haka yace Aman are You sure of what you said??
Aman ya sauke ajiyar zuciya yace eh Abi.
Abi yace to shikenan ba zan hana ka ba Allah ya taimaka.
Aman yace Amin Abi.
Har yanzu Abi bai gamsu da maganar Aman ba yace wani hanzari ba gudu ba, ba wai zaka yi Auran nan ka din ga wulakanta baiwar Allah nan ka na nuna mata rishin adalci in har ko kayi haka to sai na saba ma.
Aman yace insha Allah Abi zan kula da su.
Abi yace TOH shikenan sai a sa Rana kafin in tafi Hajj in kuma sai na dawo to duk yanda kace.
Aman yace Abi duk lkc da ka ga yayi.
Abi yace to zan kira mahaifin ta sai mu yi magana.
Aman bai ce komai ba sai tashi da yayi yace zai wuce.
Abi yace mai sai da safe.
Aman ya wuce part din sa. Nur na parlour tace mai Sannu dazuwa yace yauwa tare da nufa daki. Daman hankalin ta na kan American movie da take kallo. Bayan ya sauko ya zauna a dinning yana jiran Nur tayi serving din shi, ga shi isasshe. Daga dinning yace mata ke!
Nur ta taso ta matso kusa da shi.
Tana karaso wa Yace common sense will not tell you what is right or not.
Nur tace mi kuma nayi.
Sai an ce miki ki yi serving din mutun.
Nur ta kawshe da dariya da ta tuno incident din dazu na kitchen. Fuskar sa daure with harsh voice yace Hey!
Nur ta shiga taitaiyinta. Tace ohh na manta ya hannu ka???
Fuskar sa a daure, Nur ta bude warmer ta zuba mai jollof rice din da tayi, ta aje mai a gaban shi ta zuba mai zobo Ta aje.
Aman tunanin yanda zai fara cin abinci yake dan hannu shi na dama ya dan kone kuma in yace zai ci da hagu zai yi bari yana cikin wannan tunani Nur ta katse shi, tunanin mi kake? ka ci abinci kar kazama dolaye, y'ar karamar kone wa ka kasa amfani da hannun. Ko kuma bayan serving din sai an sa ma a baki.
Ya Kalle ta with husky voice yace get lost.
Nur ta tabe baki tace daga zan taimaka ma, fine and good ta koma parlour ta cigaba da kallon ta duk da ta na tsatan kallon shi tana kaylkaylewa da dariya dan Aman fada yake da spoon. Bai son ya akayi karamar kone wa ta zama babba ba.
YOU ARE READING
NURUl QALBI 💖
General Fictionlabarin rayuwar Nur wadda a ka aura mata mutumin da bata sani ba. ta auri mutumin daga shi har dangin shi basa San ta sai mahaifin mijin. like always in all marriages there's chanllages. Nur have to over come all the challenges. ku biyo ni domin ga...