Chapter 16

31 5 0
                                    

"The more you let go, the higher you rise.”

KOYI YADDA AKEYIN GRAPHIC DESIGN TA HANYAR AMFANI DA WAYARKA ACIKIN HARSHEN HAUSA A SAUKAKE

nayi shawaran nayi wannan kwas ne saboda ganin yawan mutanen da suke son su koyi Graphic design amma basuda laptop.

Shine nazo da wannan kwas din domin mutane su samo damar koyon Graphic design ta hanyar anfami da wayoyinsu.

Sannan nayi wannan kwas ne acikin harshen hausa saboda yan uwa hausawa su fahimta acikin sauqi

Tuntubai su ta 09162382018
Bayan wasu kwanaki Ummi tareda Habiba da asabe suka je Side din Nur. Nur ta na kawnce a parlour tana kallon American movie tajii an yi knocking. Ta tashi ta je ta bude. Tana gani su gaban ta ya fadi. Ta san ba haka nan kawai za su zo ba. Ta sakan musu fuska tace:"ku shigo." Ta basu hanya suka shiga ta rufe kofar ta bi su a baya. Wuri suka samu suka zauna Nur ta runtsina ta Gaishe su ba dan ta so ta gaida Ummi ba saboda ta gan ta tare da wasu da ba dan haka ba ko kallon Ummi ba za ta yi ba. Habiba ka dai ta amsa mata gaisuwar. Nur tace:"barin in kawo muku ruwa."zata wuce kitchen. 

Da Allah dakata! Ummi ta da ga mata tsawa. "Ce wa muka yi muna son ruwa ko an ce miki Ruwa muka zo sha??

Habiba tace:"Ahh kawo mana ruwa."

Nur ta amsa mata da "to." Ta juya za ta wuce Ummi tace:"Shegiya mai kan agawluma." Nur ta share ta ta shiga kitchen ta dauko musu ruwa tare da sobo. Ta durkusa ta aje musu sannan ta zuba musu ta mika musu. Habiba da asabe sun amsa amma Ummi da ta amsa sai ta watsa mata shi a jiki. Tace:"ke har kin kai matsayin da zan sha abu daga hannun ki." Nur ta kai zuciyar ta nesa. Bata ce mata komai ba. Asabe ta na sha ita ma ta zubar da na bakin ta. Tace:"Ay Hajiya Zainab gawra da biki sha ba." K yanzu haka a ke miki sobo ba kayan kamshi ko yar cucumber da pineapple da a ke sa wa baki sa wa.

Ummi tace:"Ina zata iya yarinyar da ba Abin da ta iya sai gantali da bin maza." Magana Nur zata yi sai ta tuno da abin da Mammy ta ce mata tare da na Mummy sai ta Kayle su da ba dan haka ba maganar da ta so fadi musu sai sun yi dana sani fadi mata haka..

Matsiyaciya da ita! Ummi tace tare da kawbe fuska.

Ohni Asabe ko mi Alhaji ya gani da zai aura wa Aman yar karamar yarinyar da ko shayar da ita ba a gama ba bayan haka wannan ay ba class din shi bace. Ace duka fadin Abuja ba sai an kai da masarautar ku ba a rasa wadda za a aura wa Aman sai wannan abar. Ta ƙare maganar tare da nuna Nur.
Nur tsaya tayi chak tana kallon su har suka gama zakin ta tass suka yi mai isar su ka tashi suka tafi dan wawaye ta dauke su su ka dai suke zubar su. Bluetooth ne jikin kunne ta volum karshe. Ta dan rufe shi da hula shi yasa Busu gane ba. Habiba ka dai tayi wa sai anjima. Bayan sun fita ta rufe kofar tare da cewa "ku Allah ya doramawa." Ta goge in da Ummi ta zubar da sobo. Carpet din hade da White sai sobon yayi staining din wurin. Ta cire rigar ta ta atanfa ta wanke ta chanza Kayan.

Bayan sun dawo part din Ummi. Ummi ta fara wa Ummu balla'i. Wai ke Habiba ashe haka za ki min. In da wani ne ya zo yace min ga abin da ki kayi ba zan yar da ba. Sai wani faran faran ki ke wa wacce yarinyar. Haba Habiba kawta kawta kin bani kunya. Asabe da ke zaune ta na takaicin haka.

*****
Sakamakon barcin da Aman ya ke yi kan kujera ya jawo mai ciwon baya. Ba arziki ya koma dakin shi. Da ya shiga Nur ta na toilet kashe fitilar yayi sannan ya kawnta. Nur ta fito daga toilet tayi mamakin wutar takin ta a kashe. Ta je ta kunna ta ga mutum a kan gado. A ranta tace;"ikon Allah yau ko da mi kuma yazo???? Ta bude hannu tare da tabe baki. Mai ta dan shafa tare da fesa turarai ta dako doguwar rigar ta ta barci mai dan nauyi ta sa ta kashe fitilar sannan ta kawnta chan karshen gadon. Har ta gama Aman bai sani ba saboda yau yayi aiki duk a gajiye yake. Sai bayan ta kawnta kamshin turarran ta na dukan mai hanci ya falkar da shi. Side lamp ya kunnan ya ganta ta na barci hankalin ta kawnce. Dafa kan shi yayi tare da fadin "wanna wata irin jarabace abi ya auro min. Dolle ne in chanza gida ko na huta." Ba yabo ba fallasa ya kashe lamp din ya koma ya kawnta ya kai 30 minute bai yi barci ba. Ba arziki ta tashi ya koma dakin karatun shi ya shinfida blanket ya kawnta.

NURUl QALBI 💖Where stories live. Discover now