28

28 4 0
                                    

Daddare Nur ta yi wanka ta kawnta kan gado. Dan yau ko Abinci Rana batayi ba tare da na dare balle Lipton din shi.
Da ya shigo ya saba gani tea aje kan dinning yau ko babu, babu a parlour ya duba kitchen babu. Ya koma sama ya bude dakin wutar a kashe ya kuna wutar dakin ya nufi closet ya dauko Kayan baccinsa bayan ya sa ya tsaya yana kallon Nur tana ɓacci ya kai 8 minute a haka. Ya yanke hukuncin ya kawnta kan gado duk da yau ma akwai kamshin turaren da yake birkita shi. Ya kawnta ya kasa ɓacci dan kamshin dake tashi daga jikin Nur na daga mai  hankali. Yayi tsaki ya dau pillow ba yanda ya iya ya koma parlour ya kawnta.

Washegari ranar Monday. Tana Tashi tayi wanka sannan tayi Sallah. Ko kasa bata sauko ba ta goma ta kawnta. Ba ɓacci take ba amma idon ta a rufe. Ya dawo daga masallaci kamar jiya ya duba ba tea ya hau sama ya iske ta tana ɓacci, toilet ya shiga ya dauko ruwa ya zuba mata. Nur ta tashi dan ta san za ayi haka. Fuskar sa daure yace ina Lipton din na.

Ta bata rai tace lkc da ka ke sa min shock ka ji tausayin na ne? Ka manta da ina da amfani.

Be quite!
Ya daga mata Tsawa ganin ta na neman gaya mai magana.
wuce ki hada min Lipton.

Nur tace Bayan ka ƙarar min da karfi ay sai da karfi ake aiki.

Zata koma ta kawnta a fisace ya fixgota har sai da ta fada kan shi tana jiyo lumfashi shi. Fuskar sa daure yace Don't provoke me this morning. Sannan ya sake ta tare da ce mata ta wuce. Nur yau bata so hada mai Lipton ba. Ta tsaya ta na kallan shi. Yace ba magana nake miki ba. Ta kalle shi sannan ta fara taka kafar ta a hankali kamar wadda bata san taka kasa.

Aman ya zauna tare da dafe kan shi;" ina dalilin wannan yarinyar duk tabi ta takura ma Rayuwata, Dolle in Nemo wata hanyar da zan mata hankali...

Kitchen ta je ta zauna ta kai 30 minute zaune bata dora mai ba. Ya sauko kasa ya iske ta a kitchen rain shi bacce. Ya karaso kusa da ita. Da manya manyan idanuwan shi yake kallon ta. Nur ta ja da baya har sai da ta kai karshen kitchen din tace mai Lipton din zan ɗora Yanzu, bai bar tazara tsakanin su ba ko wane na iya jin sautin numfashin juna su. Hannuwanta guda biyu ya murde tare da juya ta baya da hannuwan ta. Nur ta kawla ihu saboda zafi. Ta fara bashi hakuri.

Aman yace yaushe na fara wasa dake ehyy?

Nur tace dan Allah kayi hakuri. I'm sorry.

Kara murde mata hannu yayi yace ni tsa'an ki ne ina miki magana ki yi abin da ki ka ga dama.

Nur tace No, A'a please kayi hakuri dan Allah. Har sai da tafar kuka sannan ya Kayle ta yace na baki 2 minute ki kawo min Lipton di na. Ya juya zai tafi a hankali tace mugu azzalumi.

Ya juyo yace miki ka ce??

Nur tayi tsuru Sabida ya tare Hanyar guduwa bakin ta na rawa tace bance komai ba... dan Allah kayi hakuri bazan kara ba. Ta din ga bashi hakuri sai da yazo gab da ita sannan ya juya ya wuce. Ta sauke ajiyar zuciya ta goge hawayenta, cikin zuciyar ta tana ta mai Allah ya isa. Ta dauko yar tukuyar Lipton din ta haɗa mai ta zuba a cup ta kai Mai. Dan ta ga abin nashi yayi yawa.

Fuskar sa daure ta mika mai kallo ɗaya mata ta durkusa ba dan ran ta ya so ba ta mika mai. Ya amsa za ta koma dakin yace wuce ki hada min break fast.

Ta tsaya tare da yin shiru.

Biki ji Ni ba!

Ta juya ta koma kitchen ta rasa mi zata hada mai. Ta dawko Garin danwake ta kawba sannan ta saka a tafasasshen ruwan dake kan wuta bayan ya sulalu ta dora mai kawi ta aje mai a dinning ta jira har sai da yagama abin da zai yi ya karaso dinning. Ta na bude warmer din ya ga danwake. Tana tsaye a wurin yace baki da hankalin dan wake Mutun zai ci da safe.

Nur tace but it's slight food...

Ya tari numfashin ta
Ce miki a kayi ina ci ne??

To ce maka akayi nasan ba ka ci. Ta bashi amsa daidai da Tambayar shi

NURUl QALBI 💖Where stories live. Discover now