Bayan sunyi Sallah la'asar suka sami safna da friends din ta a ka musu kawliya Bayan an gama wa kowa motoci ta zo ta ɗauke su. Nur itama tayi angon fitted nevy blue sequence gown. Dinkin yayi kyau sosai duka friends din amarya ɗinkin daya a ka musu. Suka shigo da amarya da ango. Bayan an fara Dinner Mammy ta zo. Ta sa a ka kira mata Nur. Ta ja ta gefe tafara mata fada;
baki da hankalin Biki san ke yanxu ba daya ki ke da su ba. Ke fa matar aure ce zakiyi Irin wannan shigar ina laifi ki sa Gayle amma zaki wani fito ko Gayle baki da shi.Nur tace Mammy indoor event ne kuma ..
Rufe min baki, dan indoor sai mi? Ki yi hankali mana. Kuma kar ki sake in ga kin biye su kun yi rawa dan haka tsaya nan na aika a kawo miki Gayle.
Gayle!!
Nur ta furta ganin za a lallata outfit din ta. Mammy be ta bata amsa ba. Shagawba ta fara wa Mammy,
"Mammy dan Allah, yau kaɗai fa."Amma Mammy bata beye mata ba tace rufe min baki.
Sai wurin 10pm Aman ya dawo. Ya samu Hajiya Turai a parlourn ta ya gaishe ta sannan ya tambaye ta Nur. Hajiya Turai tace ka kyauta kaji. Aman yace Hajiya mi ya faru. Hajiya Turai tace inban da rishin imani Aman zaka hana yarinyar nan zuwa gidan su. Ay ba haka ake ba. Wannan rishin imani.
Aman yace Hajiya naso in dawo da wuri sai muje amma aiki ya rike Ni. Hajiya Turai tace Sannu Sarkin aiki, kowa ma ba yana aiki ba. To Ni na sa an kai ta.
Aman ya dago ya kalli Hajiya Turai yace an kai ta!! Ina ?
Chan gidan su, kuma kar ka sake ka dauko ta sai gobe ka ji Ni. Ta masa gargadi
Aman bai ji dadin haka ba yace amma Hajiya aikin gidan...
So damar yar aiki ka ɗauke ta ban sani ba?
Aman yace A'a Hajiya. Kawai dai...
Ka ga ban san jin komai. Ga abincin chan a dinning ka je ka ci in Kuma bazaka ci ba shikenan.
Aman bai so cin abinci dan dai yasan in ya koma gida ba abin da zai ci. Haka ya sa ya nufi dinning Bayan Hajiya Turai ta kira Asiya ta zuba mai abinci. ya gama ci ya mata sallama ya wuce.
Number Mammy ya kira. Lkc tana tare da Nur ta na jiran a kawowa Nur Gayle. Ta amsa kiran. Gaida ta ya fara yi sanna yace mata Aman ne.
Mammy tace Allah Sarki Aman ykk.
Nur na jin Mammy ta ambaci Aman Gaban ta ya fadi.
Aman yace lfy qlau.
Ya kara da "Mammy ina so in Nur na kusa a bata wayar.".Mammy tace ta na kusa bari in bata waya.
ta mika wa Nur wayar. Nur taki amsa. Mammy ta mata nuni da ta amsa. Ban dan ta so ba ta amsa wayar. Ta karata a kunne ta.Murya kasa kasa Mammy tace yi magana.
A sananne Nur ta bude baki tace hello.
Kafin ta rufe bakin ta yace ke taurin kan ki ya miki yawa ko??
Da na aje ki wurin Hajiya shine ki fadi mi su ko? Dan haka ki fito ina wajen hall din da kuke sakarcin ku.Nur tayi shiru batace mai komai ba.
Ya kara da;"Na baki minti 5 ki zo ki same Ni in ba haka ba zaki gane kuran ki in ki ka dawo. Ya katse wayar." Ta mika wa Mammy wayar tare da murguda baki.
Mammy ta karkada kai tace Allah ya shirye ki. Saudat ta karaso ta mika wa Mammy Gaylen. Mammy ta mika wa Nur Gaylen
Nur ta kalli gyalen tace Mammy Gaylen fa yayii girma kalla shi fa.
Ta daga shi.Mammy tace in dai ba zaki sa ba sai dai ki biyo NI ki koma gida.
Nur ta dau Gaylen ta yafa ban dan rain ya so ba, ga shi har gwiwa ya kawo mata tamkar ta sa hijabi. duk jin ta take takure.. Suka koma ciki. Inaya da Ammah dariya suka kawshe da ita ɗan ganin Nur cikin dogon mayafi. Ta harare su ta zauna ran ta bace. Inaya tace c'mon my friend, ya da fushi wurin Dinner,, ta dauko juice tace amsa juice ki sha za ki ji dadin.
YOU ARE READING
NURUl QALBI 💖
General Fictionlabarin rayuwar Nur wadda a ka aura mata mutumin da bata sani ba. ta auri mutumin daga shi har dangin shi basa San ta sai mahaifin mijin. like always in all marriages there's chanllages. Nur have to over come all the challenges. ku biyo ni domin ga...