... Suna zuwa layin gidan su taga bai tsaya ba ya Wuce. Juyo wa tayi ta kalle shi. Ko kallan ta bai yi ba. Tace mai ka gidan chan ka wuce.
Ko tanka mata bai yi ba sai dai kukan da ya fara ji ta haɗa kan ta da Gwiwa. Ya Kayle ta.
Horn yayi a Kofar gidan Hajiya Turai masu gadi suka buɗe mai. Ya kara so yayi parking a parking space sannan yace mata ta sauka. Bayan ya kashe motar. Nur ta karkada mai Kai.Ya kara ce mata ta sauka.
Kan ta na cikin Gwiwa tace Ni gidan mu za ka kay ni ba nan ba.
Aman yace zaki fara taurin kan naki ko??
ya fisgo hannun ta Hakan yasa ta dago ta kalle shi cikin kuka tace Ni ka Kayle Ni
ta fadi tana kokarin cire hannu ta daga hannun shi.Yace zaki sauka ko a'a.
Nur tace to ka sakan min hannu.
Aman ya tsaki hannuta. Zata fita yace mata ta dakata. Ya zaro tissue ya mike mata.
Ta sa hannunta ta goge hawayen ta.
Amsa! Ya daka mata tsawa kamar yanda ya saba.
A hankali tasa hannu ta amsa bayan ta wulla mai harara, ta goge fuskar ta sannan ta fita ta bi shi a baya. Kamar wancan karan sai da suka Wuce parlour biyar kafin su hau sama. Yayi knocking mai aikin gidan ta bude musu suka shigo ta gaishe su. Sannan ta raka su ciki.
Hajiya Turai na zaune kan kujera da ganin su tace Oyo Oyo my daughter, welcome.
Su ka karoso tare da durkusawa suka Gaishe ta kafin su zauna. Duk da Nur ta saki fuskar ta sai da Hajiya Turai ta tambaye ta mi ya faru, kuka ki kayi??
Kallon Aman tayi suka hada ido sannan ya kawda kai.
Sai tace A'a Hajiya ba kuka nayi ba ban dan jin dadi.
Hajiya Turai tace kai Masha Allah, Masha Allah. Ki ce dan jikallen nawa ya ku san zuwa. Daga Aman har Nur ba wanda ya ji daɗin maganar sai dai ta mata dan murmumishi.
Hajiya Turai tace kar ki damu kin ji ina tare da ke in dan da wata matsala ki kira Ni kin ji. Kuma kai Aman yanzu matar ka ta ke bukatar kulawa tin da ba ita kadai ce ba.
Aman ya kalli Hajiya Turai kafin yace Hajiya ba fa abin da ki ke tunani...
Hajiya Turai ta tari numfashin sa ji min jairin yaro, to fadi min mike damun ta, kai Ni tsaya kaji ina so gani jikalle daga wurin ka kafin in rasu in ba zaka min baƙin cikin haka, ka sa har sai bayan bani tukunan.
Aman ya mike dan bai son abinda Hajiya turai take mai yace mata shi zai tafi zai bar Nur a Nan.
Nur bata yi tsammanin haka ba. Wasu hawayen ne za su zubo mata amma sai tayi sauri ta goge su.
Hajiya Turai tace kay naji dadin haka gaskiya na ji dadin. Sai ka dawo babana. Suka hada ido da Nur yayi kamar bai san da Ita ba yayi fuska ya wuce.
ALkc Nur zuciyar ta zafi take ga bakin cikin haka. Aman ya bude kofar ya fita. Hajiya Turai tace Nur ki saki jikin ki kin ji kar ki ji komai. Nan ma gidane. Nur ta ɗan yi murmumishin karfin hali.
Dan zaman minti 30 zuwa 40 Hajiya Turai ta ba wa Nur lbr Aman tare da yarintar shi. Shi kawta kawta wani Irin mutum ne da ba jin cikin shi tun ya na Karami ga tsawrin rai. Ya tashi cikin mata amma kawta kawta mata basa gaban sa. Sun girme shi amma suke girmama shi. Nur Ni ban haife shi ba amma ko Zainab ba zata iya shaidar Aman ba. Ni Nasan kina boye min amma Aman sai mai hakuri ka dai ke iya zama da shi. Kuma Nur ina so ki chanza shi tin da ke ce matar shi.
Nur hankalinta baya nan ya na wurin Bikin.
"Nur ki fadi min gaskiya kina lfy?
Hajiya turai ta katse ta daga tunanin bikin
YOU ARE READING
NURUl QALBI 💖
General Fictionlabarin rayuwar Nur wadda a ka aura mata mutumin da bata sani ba. ta auri mutumin daga shi har dangin shi basa San ta sai mahaifin mijin. like always in all marriages there's chanllages. Nur have to over come all the challenges. ku biyo ni domin ga...