Aman na parlour ya juyo kauri daga kitchen ya tashi ya shiga kitchen din. Nur dake duniyar tunanin ji tayi an fixgota ta fada kan shi. A lkcn ta dawo cikin hankalinta. Tunkunyar ta fado kasa. Ta juya ta kalli tunkunyar, da ba dan Aman ba da ya fado mata.
Fuska daure ya fara zazzaga mata masifa baki da hankali? Daga ki tafasa abu zaki tsaya kina shashanci kin bar abu na kone wa.
Nur ta yi shiru ba tace komai ba. Yayi tsaki ya dauko wata tunkunya ya zuba ruwa tare da Lipton din ko kallon ta bai yi ba har ya tafasa. Hannu ya sa zai dau tunkunyar amma ya yi sauri ya janye hannunsa ya kashe gas din.
Nur ta kawshe da dariyar k'eta ga Kuma hawayen da suka jika mata fuska hakan bai hana ta dariya ba.
. Kallon ta yayi hakan ya sa ta yi shiru. Aman ya kalli tafin hannu shi wanda yayi ja.Nur ta matso kusa da shi ta riko hannu shi. Da zai janye amma sai ya kayle ta ya ga mi zata yi. Wurin sink ta janyo shi tasa wa hannu shi ruwa sannan ta dauko gishiri ta fara shafa mai a hannun shi a hankali. Sannan tace, Daman masu hankali suna daukar tunkunya batare da rag ba,, i think dolaye ne kaɗai ke haƙa.
Aman ya janye hannunsa fuskar sa a daure ya Nufi kofa. Zai fita tace At-least ka godai min tinda na taimaka ma, dan tafin hannu ka ya kumbura.
Juyo wa yayi ya Harare ta ya wuce. Nur tace:" halin ka bai yi ba, ta kawshe da dariyar k'eta sai kuma. Tayi tsaki tare da dawowa cikin hayyacin ta. Tace ya Allah mi nayi yanzu? Miyasa ma na taimaka mai. Uhmm ko ba komi Ni ma ya ceceni.
Sai kuma ta koma nazarin abinda za su ci. Ta bude fridge ta ga Akwai banana ta dauko guda biyu ta yi felling din ta ta fara kawb'a fruity banana pancakes. Ta gasa ta dauko plate ta sa mai sannan ta rufe ta aje mai a kan dinning ta haɗa mai coffee sannan ta wuce sama, bata iske shi ba ta san ya sauka dakin karatun shi. Dakin ta fara gyara wa tana cikin gyara wa Babalami ta kira ta a waya. Nur ta duba ta ga ita ce ta Kayle wayar. Ana ukun ne Nur ta dau kiran ba tace komai ba.Baabalami tace Nur ko ki kira ki ce ya muke? Ko da zaki tafi biki yi wa Mammy sallama duk tabi ta tada hankalin ta.
Nur ta yi shiru baabalami tace Nur kina ji na??
Nur tace eh ina jin ki.
Baabalami tace kuma ki kayi shiru.
Nur tace mi zan ce, ku da buku damu da Ni ba, Ba mai fahimta ta sannan ma buku san ta yan da na goma gida ba. Ta ja nunfashi tace Ba ma sai kun sani ba, ki gaida Mammy. Ta katse wayar.
A dayan bangaren da Mammy ke jin abin da Nur ke cewa. Tace Allah na godai ma. Allah ka kara shiryar da ita ka kara bata karfin gwiwa zama da mijinta tare da sirikanta.
Baabalami tace, Mammy ki kawntar da hankalin ki, kin san Nur na da saurin fishi amma dan dana take mance wa. Ki bata lkc.
Nur tayi tsaki ta aje wayar ta cigaba da gyaran dakin. Bayan ta gama ta sauko kasa, Aman har ya gama breakfast ta zauna taci bayan ta gama ta kawshe kawnikan ta kai kitchen tareda wanke su. Ta gyara gidan ta kunna burner sannan ta koma sama tayi wanka ta shinkedai har ɓacci ya dauke ta.
Ko da Aman ya shiga part din Ummi bai gan ta a parlour ba ya tambayi mai aiki tace mai tana daki. Ya nufi Chan bayan ya buɗe kofar zai shigo, tace mai kar ya sake ya shigo mata daki tin da bai ɗauke ta a matsayin uwar shi ba dan haka bata bukatar gaisuwar shi.
So innocent Yace Ummi ki yi hakuri.
Ummi tace bace min daga nan.
ya juya ya fita ya bar gidan gabaki daya. Gidan su Ahmad ya je. Ya shiga wurin Ummu ya gaida ta, ta tambaye shi ina Nur take? Tana lfy. Aman yace lfy ta qlau. Sannan yace zai shiga wurin Ahmad. Ya tashi ya nufi side din Ahmad bayan yayi knocking Ahmad ya buɗe mai. Aman kai ney??
YOU ARE READING
NURUl QALBI 💖
General Fictionlabarin rayuwar Nur wadda a ka aura mata mutumin da bata sani ba. ta auri mutumin daga shi har dangin shi basa San ta sai mahaifin mijin. like always in all marriages there's chanllages. Nur have to over come all the challenges. ku biyo ni domin ga...