chapter 23

28 4 0
                                    


. komawar baabalami gida Mammy ta tambayi ta mike damun Nur. Baabalami tace cramp pain ne. Mammy tace Allah mai iko, ke nan ba abin da ya shiga tsakaninsu. Baabalami ta ɗan yi murmumishi tace Mammy ke nan sai kace Biki san halin Nur ba. Kuma kin ga yanda auran nasu ya kasance. Suna bukatar jituwa. Mammy tace wannan haka ne. Allah ya tsawake.

Mammy ce kadai bata san halin da Nur ta ke ciki ba dan ba ta son hankali ta ya tashi Shiyasa Wani abu Nur ke Kayle wa dan in tace za ta tanka musu baza ayi da kayu ba.

Nur na kawnce tana kuka, ta tashi zaune ta goge hawayen ta dan kukan ba zai mata. Toilet ta shiga ta tsaftace jikin ta. Bayan ta fito ta sa sleeping wears. Sannan ta sauko kasa ɗan ciwon cikin ya lafa sai dai yunwa. Zata fito daga Dakin A lkc Aman zai shigo. Ko kallon shi bata yi ba ta wuce kasa. Direct toilet ya shiga ya watsa ruwa ya gama abin da zai yi ya koma kasa.

Kitchen ta shiga. Ta rasa abin da zata ci dan baza ta iya cin spaghettin da baabalami ta dafa ba. Ta yanka fruit ta sha ta dauko ruwa ta nufi sama. Bayan ta sha magani ta dauko wayar ta tayi replying massages bayan minti 30 tayi ɓarci. Bai fi bacin 2hours tayi ta falka. Bata iya goma wa ba sai Wajen 5:30am saboda ciwon Cikin ya hana ta ɓarci. Ta so ta sha overdose Amma bata sha ba dan magana Sabir ta tuna a kan ta dai na shan overdose zai iya jawo mata matsala a mahaifarta sa'annan ba duka jini zai fita wadda Shima hakan na iya jawo mata matsala.

Ko da Aman ya shigo da asuba a kasa ya ganta ta sa pillow tsakanin cikin ta da cinyarta, a haka ɓarci ya ɗauke ta. Kallo ɗaya ya mata ya wuce toilet yayi alwalla ya tafi masallaci. Bayan ya dawo Dakin ya kara shiga amma tana ɓarci zai tada ta sai ya tuno lkc da Amrah take ciwon ciki ita har ma ƙarin ruwa wata sa'in a ke mata. Sai ya fita daga Dakin ya nufi kitchen zai tafasa Lipton amma ya kare ya duba store babu saura. Ya duba kayayyakin kitchen dana store. Sannan ya haɗa normal Lipton ya sha ya bar gidan.

Nur ɓarci take sai wurin 9 wayar ta tayi ringing wadda ta tada ta daga ɓacci. Baabalami ce ke kiran ta ta dau wayar baabalami tace tazo ta bude mata. Nur ta tashi ta daddafa ta bude wa baabalami. Bayan ta shigo ta rufe kofar. Nur ta Gaishe ta. Baablami ta mata ya jiki.

Muryar a shaqe tace da sauki.

Parlour suka zauna. Baabalami ta tambaye ta ina Aman.

Nur bata San magana wannan mutumin. Tace Ni ban sani ba.

Baabalami ta karkada kai.

Knocking akayi baabalami ta tashi ta bude. Jannah ce, Ta gaida ta tare da karaso wa Wurin Nur.

Baabalami ta rufe kofar ta dawo wurin su. Bayan sun gaisa jannah ta tambaye ta ya ji kin kuma? Jiya munzo Ni da Nawfal kina ɓacci. Kin san yanda Nawfal yake da takura.

Nur tayi murmumishi tace wayyo, my boy. Nima kawna biyu naji shi shiru.

Jannah tace Nawfal ke nan, bari in wuce Daman na shigo in duba ki kafin in tafi wurin aiki. Ta mike tare da ɗaukar jikar ta.

Nur tace Nagode. In ya dawo a kawo min shi.

" To shinkena. Sai anjima Allah kara tsawki."
Nur ta amsa da "Amin."

Bayan fitar ijannah baablami tace gaskiya yarinyar nan na da mutunci Biki ga yadda ta damu jiya da ta ji baki da lfy yau ma kin ga ta shigo.

Nur tace baabalami Daman nace miki daga ita sai abi kadai suke kauna ta.

Allah ya kauyta.

Yau ciwon cikin da dan tsawki bakamar na jiya ba. Da yamma baabalami ta tafi. Kawna uku baabalami ta yi tana zuwa kafin ta dai na zuwa. Nur a wannan kawnikan bata sa Aman a idon ta ba. Kuma ba wai bai gidan ba. Ranar Sunday da yamma inaya ta kira ta ta ke tambayar ta lfy taji ta shiru har week din ya kare bata dawo ba.

NURUl QALBI 💖Where stories live. Discover now