Washegari da asuba Aman ya tashi ya yi alwalla sannan ya sauko kasa zuwa masallaci. Ya bude kofa zai fita sai ya tuna da Nur ya juya fuskar shi. Hango ta yayi a kwance. Ya buɗe kofa ya fita. Har ya dawo Nur ba ta tashi ba. Kitchen ya nufa ya dauko ruwa a fridge ya zuba mata shi a jiki. A firgice ta tashi tare da kwala ihu wadda shi kan shi Aman sai da ya tsorata. Kuka ta fashe da shi tare da bashi hakuri abin ba zai gogu ba. Ko sauraran ta bai yi ba. "Na baki 10 minutes kiyi Sallah sannan ki kawo min tea."
Nur ta kalle shi sannan ta tashi ta nufi sama. Ta na shiga dakin ta kara fashe wa da kuka. Allah ya haɗa ta da jaraba Allah ya haɗa ta mugun mutum azzalumi kawai. Tana kuka ta shiga toilet tayi alwalla ta fito tayi sallah tare da kai kara wurin Ubangijin mu. Nur ta rasa dalilin da ya sa take jin tsoron sa, ta rasa mi ya same ta ne da ta ke saurin kuka yanzu miyasa ta zama ragguwa. Nan ta gama ta sauko kasa ta haɗa mai Lipton ta Kai mai dinning sannan ta koma sama Domin ta dan huta. Bayan ya fito daga Dakin karatun shi. Ya zauna kan dinning ya sha tea Bayan ya ga ma. Ya nufi Dakin karatun sa ya dakata ya koma sama. Ya buɗe dakin Nur na kawnce a kan gado ta juya kanta. Ta ji shigowar sa sai tayi shiru. Aman daga Bakin kofar yace:"ke!!!Nur tayi shiru. Yace:"Ina aikin da na sa ki? Tayi shiru. "Ki wuce ki cigaba da goge wancan abun." Nan ma tayi shiru. Bai kara ce mata komai ba ya nufi toilet. Ita ma ta san mi zai yi da sauri ta tashi dan ruwan da ya ke watsa mata har cikin ranta. Karaso wa yayi kusa da ita fuska daure. Fixgo hannu ta zai yi ta silale kasa. Dan in ya murde mata hannu duk kashu shuwan jikin ta sai sun yi ciwo. Hakuri ta bashi dan tayi tayi ya ki Goguwa. Bai mata Magana ba ya sa ta ta tashi, dago kan tayi ta kalle shi suka hada ido ya sauke Yace:"bana san jin komai." Ki wuce ki goge shi. Nur ɗan ta na son zuwa gida shi yasa take abin da ya sa ta. Ta sauka kasa ta shiga kitchen ta na gurnani. Sai ta tuno baabalami abin da ta fadi mata. Ta shiga kitchen ta haɗa ruwan kunfa da warm water ta dauko baking powder da vinegar ta sa ta koma parlour ta fara goge wa. Bayan ta gama gyara gidan ta shiga tayi wanka ta sa kaftan din ta ta dawra dankawli. Ta fito parlour ta kunna burner gidan ya turnike da kamshi. Aman dake dakin karatun shi kamshin na bugo mai. Har sai da ta gama sanan shi ya fito zai je masallaci. Kamshin da parlour yake yi ya birge shi sai sheki ya ke yi amma kawta kawta bai nuna ba. Nur ta na son ta kira shi amma tarasa wanni suna za tace mai. "Brigadier!! ta fadi kamar tana jin tsoran abin da zai biyu baya.
Aman yayi mamakin jin haka don wurin aiki ka dai a ke kiran shi da haka nan ma ba kowa ba sai bai tsaya ba sai da ta kara kiran shi sai ya tsaya bai juyo ba. Nur a hankali tace:"Dan Allah ina son zuwa gida, ina son in ga Mammy." Bai ce komai ba. Nur ta kara da dan Allah.
Ya juyo yac:"Ba zaki ba." Zai juya ta Tambaye shi; why?? Na fa dade ban gan ta ba dan Allah ka bar Ni in je please... Ko kallan ta bai yi ba ya wuce. Nur haushin kan ta ta fara ji. Duk abin da ta mai dan kawai ya barta amma yaki. Ta so ta fita amma gidan babba ney. Ba ta San in da gate din gidan yake sai dai ta hango shi ta window. Takaici ya ishe ta tayi powering din Tv. Ta zauna ta na kallo.
Aman ya na Side din Ummi yana cin abinci abi ya shigo. Aman ya runtsina ya gaida shi. Abi ya tambaye shi ina matarsa. Aman yace:"Tana chan."
"Chan ina??
Aman yace:"Chan part din Na."
Abi yace:"Ohhh shi ne za ka zo na ka na cin abinci ko? Aman zai yi magana Abi yace girkin ney bata yi da kullum na ke ganin ka nan. Ummi ta karso kusa da su tare da tambayar lafiya. Abi yace:"Lafiya Qlau, Ay ke ce ki ka daure mai gindi domin ya din ga abin da ya ga dama." A ce Mutun bai cin abincin gidan shi abincin matarsa.
Ummi tace:"Abi yarinyar nan fa bata iya komai fa." Indomine kadai ta iya shikuma bai cin indomine ba, mace tana mata bata iya komai ba.
"Naji ke lokcin da na Aure ki mi ki ka iya ne..." Ummi sakin bakin ta tayi.
To wai ina Nana?? Ya tambayi Aman.
Na sallame ta.
Abi yace:"wani dalilin? Aman yace:"Abi naga akaiw mata a gidan to ba buƙatar yar aiki. Abi yace:"To ban yarda ba ka je ka dawo da Nana in abincin ney bata iya ba sai ta din ga koya mata ko ka samu chef." Kuma daga yau sai Yau kar ka kara cin abincin gidan nan. In har ka ci to ban yafe. Ummi tace haba Abi ya za ka hanke wannan hukunci shi abinci a mi yake. Abi ya Kalle ta sannan yace wa Aman:"Tashi muje ka raka ni wurin ta." Aman zai yi magana sai ya kayle. Abi yace Ummi ma ta tawo. Kuma bai san jin excuse. Nan ya tisa su gaba suka nufi part din Nur.
YOU ARE READING
NURUl QALBI 💖
General Fictionlabarin rayuwar Nur wadda a ka aura mata mutumin da bata sani ba. ta auri mutumin daga shi har dangin shi basa San ta sai mahaifin mijin. like always in all marriages there's chanllages. Nur have to over come all the challenges. ku biyo ni domin ga...