chapter 26

33 3 0
                                    

Washegari da Asuba kafin ya tashi har ta tashi ta shiga toilet tayi alwalla sannan tayi salatul fijir ta sauka kasa ɗan ko hada ido bata so son yi. Tana kitchen Aman ya fita zuwa masallaci. Ta aje mai tea din sa a dinning sannan ta wuce sama tayi sallah, bayan ta gama ta fito kitchen ta musu breakfast dan yau zata je school. Bayan ta gama ta aje mai a dining ta koma ta kawda kitchen. Ta Fito zata koma daki dan tayi wanka suka hada ido huɗu da shi. Za ta juya ta koma kitchen ya dagatar da ita:

Ke zo nan.

A tsorace ta juya ta karasa kusa da shi ta bar tazara a tsakanin su. Idon ta yau a kasa ta Gaishe shi. Ko amsa wa bai yi ba.

With husky voice yace baƙi da wayo ne, kina abu kamar yarinyar.

Ta marairaice tace, kayi hakuri, hannuwana na min cewo, kuma bana son ka murde min hsnnu Shiyasa...

Quite!
Ya daga mata tsawa. Sannan ya kara da useless. Ya ida karasa wa kasa. Za ta koma daki ya kira ta dan tayi serving din shi, ta gama sannan ta koma daki tayi wanka ta shirya ta sauko kasa tayi breakfast. 

Wurin 9:40am Ta kira drivern ta. After 10 minutes ya kira ta yace ya iso. Ta saka hijab tare da rataye hand bag din ta kan shoulder ta sauko kasa. Bude kofa tayi zata tafi sai ta tsaya tana contemplating shin tace mai ta tafi ko ta Kayle shi. Sai ta juya ta nufi dakin karatun shi tayi knocking ba a bude ba ta kai 8 minute tsaye Hakan ya bata haushi tayi tsaki ta wuce.

Suna shiga cikin school department din su ya aje ta. Ta shiga class anan yayi parking motar ya jira ta. Bayan 2 hours ta fito tare da friends din ta. Yana wurin securities tana fito wa ya musu sallama ya karaso ya buɗe mata Mota suka shiga ciki tare da friends din ta. Ta nuna mai Chemistry department yayi parking sannan ya zagayo ya bude mata Mota ta sauka. Ya take mata baya har sai da ta shiga cikin office din Abdurrazaq sannan ya tsaya a wajen kofar.

Tana shiga ko Gaishe shi bata yi ba ta ja kujerar ta zauna. Su inaya da suke tsaye suka gaishe shi.

Nur tace Dr Nazo ne batun maganar project din na. Yaza ayi ne.

Abdurrazak ya dagatar da aikin da ke gabansa yace i will just guide you in that.

Kallen raini tai Mai sannan tace ohh really!  Ta lumshe mai ido daya, cikin sanyin Murya tace haka muka yi da kai.

Nan take ta burkitar da shi. Dan yanda ta mai magana kamar mai mai barazana ko kuma wani abu. Da sauri yace A'a.. yanzu mi ki ke so.

Tayi bajawarar dariya tace ka min project din what i will do is the presentation.

Abdurrazak yace only presentation???

Nur tace ehenn! Ko ba Za kayi ba??

Abdurrazak yace No, i think at least if I guide you You will...

Wait Dr, will you do it or not??

Cikin mamaki ya kalli Nur. Wai ita ke tambayar shi zai yi ko ba zai yi ba. Kamar wata mahaifiyar shi, duk fadin school din wa ya isa ya mai haka.

Nur tayi murmumishi tareda gyaran Murya tace Dr kana so aji mu Ni da kai?? Ta tabe baki tace Okay woo.
Ta mike zata tafi yace shikenan i will, in nagama zan Turo mike. She smirks and leave with her gang.

Suna fito wa driven ya take mata baya su ka fita ya buɗe mata motar ta shiga.. Drivern ya koma wurin driver seat ya bude ya shiga Tambayar ta ina su kayi. Nur tace mai wuse. But Wait..

Ta duba wayar ta bata da number Aman Balle tace mai zata je gidan su Inaya ɗan ta amso cupcakes din da ianya ta mata. Tace mai su tafi. Suka aje Ammah a gida sannan suka wuce gidan su Inaya. Yayi parking a waje sannan ya buɗe mata kofa suka shiga ciki ya bi su a baya. A Kofar parlour ta dakatar da shi sannan suka shiga ciki. Tana shigowa taci karo da Sabir nan ta ke zuciyar ta tayi melting. Idonta ta sauke kasa ta gaishe shi ta wuce ciki dan bata so ta tsaya a wurin.

NURUl QALBI 💖Where stories live. Discover now